Sep 03, 2018 11:16 UTC
  • MDD Ta Yi Gargadi Kan Karuwar Hadari Da Bakin Haure Ke Fuskanta A Kan Hanyarsu Na Zuwa Turai

Manzon musaman na babban kwamishinan dake kula da 'yan gudun hijra na MDD a al'amuran da suka shafi ruwan Bahrun ya yi gargadi kan karuwar hadarin da bakin haure ke fuskanta wajen ratsawa ta ruwan a kokarin isa zuwa Turai

Mista Vincent Kochtl manzon musaman na babban kwamishinan dake kula da 'yan gudun hijra na MDD a al'amuran da suka shafi  ruwan Bahrun ya ce cikin bakin haure 18 mutum guda na rasa ransa a kan  hanyarsa na ratsawa ruwam Bahrum zuwa Turai.

Mista Vincent Kochtl ya ce matakan da masu safarar mutune zuwa Turai ke dauka na kaucewa jami'an yaki da masu safarar mutane a ruwan Libiya shike kara jefa bakin hauren cikin hadari.

Cikin wani Rahoto da MDD ta fitar kimanin bakin haure dubu da 600 ne suka nutse a ruwan Bahrun cikin  watani takwas na wannan shekarar ta 2018.

Tags