Oct 18, 2018 12:26 UTC
  • WHO Ta Bukaci A Hana Amfani Da Sinadarin Lead A Fenti Zuwa Shekara Ta 2020

Hukumar lafiya ta duniya WHO ta bukaci kasashen duniya su dakatar da amfani da fenti wanda aka sanyawa sinadarin lead kafin shekara ta 2020

Jaridar Premuimtimes ta Najeriya ta bayyana cewa hukumar ta yi wannan kiran ne a taron  makon kasa da kasa na hana amfani da guba lead na shekara ta 2018. wanda aka gudanar tsakanin ranar 21 zuwa 27 na watan Octoba da muke ciki. 

A ranar laraban da ta gabata ce hukumar lafiya ta duniya tare da gangamin kasashen duniya don hana amfani da sinadarin lead wanda ake sanya a cikin fenti suka bada sanarwan haka, don irin yadda yara kanana suke cutuwa da wannan sinadarin a duniya.

Kamfanoni masu samar da fenti a duniya suna sanya sinadarin lead a cikin fenti don sa shi saurin bucewa, amma kuma sinadarin gobe ne musamman ga yara kanana a gidaje ko wuraren da aka yi amfani da irin wannan fentin. 

 

Tags