Dakarun Ansarullah Sun Kaddamar Da Wasu Sabbin Makamai Masu Linzami
Dakarun kungiyar Ansarullah ta kasar Yemen sun sami nasarar harba wani makami mai linzami mai cin gajeren zango da suka kaddamar da shi a ranar Asabar din da ta gabata, inda suka harba shi kan wasu sansanin sojojin haya na kasashen waje da suke goyon bayan Saudiyya a Yemen.
Rahotanni sun jiyo kakakin dakarun kasar Yemen din Sharaf Luqman yana fadin cewa dakarun na su sun sami nasarar kera wannan makami mai linzamin da aka ba shi sunan Badr P1 wanda kuma yake da karfin rusa duk wajen da aka harba shi kansa.
Rahotannin dai sun ce tuni dai dakarun na Ansarullah suka gwada wannan makamin a kan wani sansani na sojojin hayan da Saudiyya ta shigo da su kasar inda ya haidar da gagarumar hasara ga sansanin. Wasu rahotannin sun ce sansanin dai yana dauke ne da sojojin kasar Sudan da aka turo su kasar Yemen din don taimakawa Saudiyya din a fadar da take yi da kasar Yemen din.
Wasu jami'an kungiyar ta Ansarullah sun ce lalle za a yi amfani da wannan sabon makami mai linzamin wajen kai hare-hare kan cibiyoyin soji da na tsaro da na tattalin arziki na Saudiyya da kawayenta da suke yaki a kasar Yemen din.