Nov 23, 2018 10:16 UTC
  • Kungiyar Red Crescent Ta Iran Ta Sanar Da Aniyarta Na Taimakawa Al'ummar Yemen

Babban sakataren kungiyar agaji ta Red Crescent ta kasar Iran, Muhammad Muhammadi Nasab ya bayyana aniyar kungiyar ta su ta kasantuwa a kasar Yemen don ba da agaji na gaggawa ga al'ummar kasar Yemen din da suke fuskantar matsaloli na rayuwa sakamakon ci gaba da hare-haren wuce gona da iri da Saudiyya da kawayenta suke kai wa kasar.

Babban sakataren kungiyar agaji ta Red Crescent ta kasar Iran din ya bayyana hakan ne a wata ganawa da yayi yau din nan da mataimakin  babban sakataren MDD kan lamurran agaji, Rashid Khalikov da ke ziyara a nan Tehran inda ya ce: ba da agaji ga al'ummomin da suke fuskantar wata masifa da suka hada da ambaliyar ruwa a Pakistan, fari a Somaliya, matsalolin tsaro da yaki a Iraki, Siriya da Yemen suna daga cikin ayyukan da kungiyar Red Crescent ta Iran ta yi a fagagen kasa da kasa.

Mr. Muhammadi Nasab ya kara da cewa kungiyar ta su a shirye ta ke ta tura da jami'anta dauke da kayayyakin agaji daban-daban zuwa kasar Yemen don taimakawa al'ummar kasar da suke fuskantar matsaloli na yunwa da yaduwar cututtuka sakamakon ci gaba da hare-haren wuce gona da irin Saudiyya da kawayenta a kasar.

Shi ma a nasa bangaren mataimakin  babban sakataren MDD kan lamurran agaji, Rashid Khalikov ya jinjinawa irin namijin kokarin da kungiyar Red Crescent ta Iran din take yi yana mai bayyana aniyar MDD na aiki tare da kungiyar wajen isar da kayayyakin agajin da suke da su ga mabukata a wadannan kasashen.

 

Tags