Faransa: Jami'an Tsaro Sun Kama Masu Zanga-zanga 1000
Kamfanin dillancin labarun Faransa ya ambato cewa; Jami'an tsaron kasar ta Faransa sun kame fiye da mutane 1000 masu Zanga-zanga yayin da wasu 30 su ka jikkata
Har ila yau jami'an tsaron sun yi amfani da karfi wajen tarwatsa masu Zanga-zangar a cikin birnin Paris da wasu biranen kasar
Bugu da kari taho mu gama a tsakanin jami'an tsaro da masu Zanga-zangar ya yi sanadin jikkatar 'yan sanda uku
A garin Leon ma an yi taho mu gama mai tsanani a tsakanin masu Zanga-zangar kin jinin tsarin tattalin arziki na jari-hujja da jami'an tsaro
An fara gudanar da Zanga-zangar dai a ranar 17 ga watan Nuwamba bayan da gwamnati ta dauki matakin kara farashin makamashi.
Ma'aikatar harkokin cikin gida kasar ta Faransa ta bayyana cewa adadin mutanen da su ka fito kan titi a yau su kai 31,000.