Dec 28, 2018 17:48 UTC
  • Fiye Da 'Yan Ci Rani 2200 Ne Suka Mutu A Cikin Tekun Mediterranean A Cikin 2018

Hukumar da ke kula da taimaka ma 'yan gudun hijira a kasar Spain ta sanar da cewa, tana da alkalumma na adadin mutanen da suka mutu a cikin wannan shekara a cikin tekun Mediterranean a yayin da suke hankoron tsallakawa turai ba bisa ka'ida ba, inda adadin ya haura 2200.

Kamfanin dilalncin labaran Anatoli ya bayar da rahoton cewa, a cikin bayanin da hukumar ta kasar Spain ta fitar, ta ce alkalumman nata nuni da cewa mutane 2241 ne suka mutu a cikin tekun Mediterranean tun daga watan janairun da ya gabata ya zuwa yanzu, duk kuwa da cewa adadin ya ragu idan aka kwatanta da shekarar da ta gabata.

Akasarin mutanen da suka mutu dai sun fito ne daga kasashen nahiyar Afrika da kuma gabas ta tsakiya, musamman wadanda ake fama da matsaloli na rikice-rikice a kasashensu, ko kuma matsaloli na tattalin arziki, inda suke yin kasada da rayuwarsu domin neman mafaka a nahiyar turai, bisa tsammanin ko sun samu saukin rayuwa.

Bayanin ya kara da cewa, a cikin wannan shekara kimanin mutane 50,000 ne suka isa gabar ruwan Spain ba bisa kaida ba, wadanda aka ajiye sua  wurare na musamman da ake kula da wadanda suka shigo kasar ba bisa kaida ba, kafin sanin makomar lamarinsu.

 

Tags