Jan 07, 2019 05:41 UTC
  • Paparoma Francis Ya Soki Lamirin Kasashen Turai Kan Batun 'Yan Gudun Hijira

Jagoran mabiya addinin kirista 'yan darikar Katolika na duniya Paparoma Francis, ya bukaci kasashen turai da su taimaka ma 'yan gudun hijira da suka lakahe a cikin ruwan tekun mediterranean.

Tashar talabijin Euro News ta bayar da rahoton cewa, Paparoma Francis ya bayyana halin da wasu 'yan gudun hijira su 49 suke ciki a cikin jiragen ruwa guda biya a ickin tekun mediterranean da cewa yana da matukar tarayar da hankali.

Baya ga haka kuma ya ce, wannan batu ne na 'yan adamkata da ya kamata kasashen turai su nazaria  kansa, domin barin wadannan mutane a cikin ruwa ba tare da ceton rayuwarsu ba, alhaki ne da ya rataya kan kasashen turan.

Haka nan kuma Paparoma ya yi kakkausar suka kan yadda gwamnatocin kasashen Italiya da Malta suke yin mummunar mu'amala da bakin haure 'yan ci rani.

Fiye da makonni biyu kenen a jere jiragen ruwa masu ceto a cikin tekun mediterranean wato jirgin Sea-Watch 3, da kuma Sea Eye, suke dauke da 'yan cirani 49, wadanda har yanzu ba su samu izini daga wata kasa r da za ta karbe su ba.

Tags