Feb 17, 2019 06:34 UTC
  • Rasha Ta Bayyana Wajabcin Samo Hanyar Lumana Ta Warware Damabruwar Siyasar Kasar Venezuela

Ministan harkokin wajen kasar Rasha Sergei Lavrov ne ya yi wannan kiran, a matsayin hanyar fitar da kasar daga rikicin da Amurka ta jefa ta

Tashar talabijin din Russia Today ya ambato ministan harkokin wajen kasar yana fada a wani taron manema a birnin Munich na kasar Jamus cewa; Kasashen Rasha, Iran Bolivia, Mexico, da Sin suna son a warware dambaruwar siyasar kasar ta Venezuela wacce Amurka ta jefa ta a ciki.

Ministan harkokin wajen na kasar Rasha ya zargi kasashen turai da cewa suna daukar matsayar da take cin karo da dokokin kasa da kasa akan Venezuela.

Bugu da kari Sergei Lavrov ya zargi kasashen na turai da yi wa shugaba Nicolas Maduro matsin lamba saboda ya gudanar da zabe cikin gaggawa.

 

Tags