Tunawa Da Ranar Da Sahyoniyawa Suka Sanya Wa Masallacin Kudus Wuta
(last modified Mon, 22 Aug 2016 05:38:19 GMT )
Aug 22, 2016 05:38 UTC
  • Tunawa Da Ranar Da Sahyoniyawa Suka Sanya Wa  Masallacin Kudus Wuta

Ranar 21 ga watan Augustan 1969 ta kasance rana ce wacce ta shiga cikin tarihin irin aika-aikan da yahudawan sahyoniya suke ci gaba da yi wa bil'adama don kuwa rana ce da wani mai ra'ayin sahyoniyawan dan asalin kasar Australiya mai suna Denis Michael Rohan ya sanya wa masallacin Al-Aqsa alkiblar musulmi na farko kana kuma waje na uku mafi tsarki a wajensu, wuta; lamarin da ya kara fito da irin bakar aniyar sahyoniyawan.

Kafin wannan danyen aiki na kona masallacin Kudus din, sahyoniyawan sun mamaye garin na Kudus a yakin kwanaki shida a shekarar 1967. Don kuwa tun bayan mamaye garin na Kudus, sahyoniyawan suke ta kokari wajen sun kawar da duk wata  alama  ta Musulunci dake wannan garin. To sai dai sun fuskanci turjiya kala-kala daga wajen al'ummar birnin da sauran Palastinawa da suke kasar Palastinun.

Kokarin hana Palastinawa shiga masallacin Al-Aqsan, ruguje gine-ginen garin Kudus da wadanda suke makwabtaka da masallacin Al-Aqsan, fadada matsugunan yahaudawa da nufin sauya adadin mutanen da suke wannan garin da dai sauransu suna daga cikin abubuwan da sahyoniyawan suka yi kuma suke ci gaba don cimma wannan manufa da suke da ita tun bayan sanya wa  masallacin na al-Aqsa wuta shekaru 47 da suka gabata.

Wannan sabon kokarin sahyoniyawan na kawar da duk wata alama ta Musulunci daga masallacin Al-Aqsan da kuma cire shi daga tarihin ci gaba na Musuluncin shi ne ya janyo boren Intifada na uku da al'ummar Palastinu suka kaddamar. Tun daga ranar farko ta watan Oktoban bara (2015) al'ummomin yankuna daban-daban na garin Kudus da wasu garuruwan na Yammacin Kogin Jordan suka yunkura da gudanar da zanga-zangogi da sauran nau'oi na turjiya wajen tinkarar wannan danyen aiki na sahyoniyawan, lamarin da ya taimaka nesa ba kusa ba wajen dakile yahudawan aiwatar da wannan bakar aniya ta su a daidai wannan lokaci da suka so yin hakan.

Batun sauya yanayi da kuma kawar da alamu na Musulunci a birnin na Qudus da kuma masallacin Al-Aqsan wani babban buri ne da sahyoniyawan suke da shi kuma suke ci gaba da fadada shi ba tare da sun fuskanci taka burgi na a zo a  gani daga hukumomi da kungiyoyi na  kasa da  kasa ba.

Babban misalin irin  wadannan cibiyoyi na kasa da  kasa din ita ce kungiyar hadin kan kasashen Musulunci wacce aka kafa ta a ranar 25 ga watan Satumban 1969 wata guda bayan sanya wuta da aka yi wa Masallacin na Kudus, amma ta gaza wajen hana yahudawan ci gaba da wannan bakar aniya ta su duk kuwa da cewa hakan ita ce babbar manufar kafa ta. Kai wasu ma suna ganin irin raunin da kungiyar ta nuna bugu da kari kan ayyukan wasu gwamnatoci da shugabannin kasashen musulmi suna daga cikin abubuwan da suka karfafa sahyoniyawan ci gaba da abin da suke yi.

A halin yanzu dai ayyukan nuna adawa da Musulunci da duk wata alama tasa da sahyoniyawan suke yi bai takaita kawai da yankunan Palastinawa da suka mamaye ba, face dai ya ketare zuwa har  wasu yankuna  da kuma  kasashe, ko da kuwa ba kai tsaye ba, sahyoniyawan sun kasance suna amfani da wasu hanyoyi da wajen cimma wannan manufa ta su. Babban misalin hakan shi ne irin goyon bayan da sahyoniyawan suke ba wa wasu kungiyoyi na 'yan ta'adda irin su kungiyar Da'esh da sauran su a kasar Siriya ko kuma ta hanyar goyon bayan wasu gwamnatocin larabawa kamar yadda suke goyon bayan hare-haren da gwamnatin Saudiyya take kai wa kasar Yemen duk dai da nufin ruguza kasashen musulmi da sauran alamomi na Musulunci da suka hada da masallatai da wajajen tarihi.

Ko shakka babu rusawa  da kuma shafe ababen tarihi na mazhabobin Musulunci da shi kansa addinin Musulunci a yanayi na gaba daya a kasashen musulmi wani lamari ne da ke cikin tunani da kuma akidun sahyoniyawan wanda a halin yanzu suke ta kokarin cimma shi a kasashen musulmi irin su Siriya, Yemen Bahrain da sauran yankuna da kasashen musulmi sakamakon gazawar gwamnatoci da kungiyoyin na musulmi a wasu lokutan kuma bisa hadin baki da daurin gindin wasu gwamnatocin irin su Al-Sa'ud na Saudiyya.