Feb 27, 2016 17:02 UTC
  • Zaben Iran
    Zaben Iran

Masu saurare assalamu alaikum barkanmu da warhaka da kuma sake saduwa cikin wani sabon shirin Iran A Mako shirin da ke leko muku wasu daga cikin lamurran da suka faru a Iran cikin mako wanda ni Muhammad Awwal Bauchi na saba gabatar muku da shi da fatan masu saurare suna cikin koshin lafiya.

To yau ma ga mu da wani sabon shirin, sai a biyo mu don jin yadda shirin zai kasance.


Daga cikin muhimman al’amurran da suka faru a Iran cikin makon ko shakka babu batun zabubbukan da za a gudanar gobe Juma’a su ne a kan gaba inda jami’an kasar suke ci gaba da kiran al’umma da su fito kwansu da kwarkwatarsu yayin wannan zaben don ba wa marada kunya. Daga cikin lamurran da za mu yi dubi cikinsu har da ganawar da Jagoran juyin juya halin Musulunci yayi da mutanen lardin Azarbaijan ta Gabas inda yayi karin haske kan batutuwa daban-daban. A bangaren tattalin arziki ma dai daga cikin batutuwan da suka dau hankula din har da taron ministocin man fetur na wasu kasashen kungiyar OPEC da aka gudanar a nan Tehran don tattauna hanyoyin farfado da kasuwar mai din. A bangaren tsaro kuwa daga cikin batutuwan da suka dau hankula har da ziyarar da ministan tsaron kasar Iran ya kai kasar Rasha a ci gaba da karfafa alaka ta tsaro dake tsakanin kasashen biyun.

Wadannan da ma wasunsu suna daga cikin batutuwan da za mu yi dubi cikinsu a shirin na mu na yau. Don haka sai a biyo mu sannu a hankali.


 


-----------------------------------------/


 


Masu saurare barkanmu da sake saduwa.


 


Kamar yadda kuka ji a farkon shirin a gobe Juma’a ce ake sa ran za a gudanar da zaben ‘yan majalisu biyu masu matukar muhimmanci a Iran wato zaben ‘yan majalisar shawarar Musulunci wacce take da hakkin tsarawa da kuma kafa dokoki a kasar da kuma na ‘yan majalisar kwararru ta Jagoranci wacce take da hakkin zabe da kuma sanya ido kan ayyukan Jagoran juyin juya halin Musulunci na kasar.


 


A ranar Alhamis din da ta gabata ce aka bude yakin neman zabe ga dukkanin ‘yan takaran wadannan zabubbuka guda biyu a duk fadin kasar don ba su damar isar da sakonninsu da kuma irin ayyukan da suke fatan yi wa al’umma idan har aka zabe su.


 


An fara yakin neman zaben ne bayan da Ma'aikatar cikin gida da kuma hukumar zabe ta kasar Iran din suka sanar da cewa an gama kammala dukkanin shirye-shiryen da suka kamata a yi don fara yakin neman zaben a duk fadin kasar kamar yadda doka ta bayar.


 


A bisa sanarwar da hukumar zaben ta bayar, akwai kimanin 'yan takara 6,200 da suka sanar da aniyarsu ta neman zaman 'yan majalisar shawarar Musulunci ta kasar mai kujeru 290, kamar yadda kuma akwai wani adadi na 'yan takarar ma da suka tsaya don takarar kujerun majalisar kwararru ta jagoranci wacce ta ke da alhakin zabe da kuma sanya ido kan ayyukan Jagoran juyin juya hali na kasar.


 


Rahotanni daga bangarori daban-daban na kasar ta Iran na nuni da cewa 'yan takarar sun yi amfani da wannan dama ta mako guda da aka ba su nay akin neman zaben wajen gabatar da kansu ga al’umma. Gwamnati dai ta tanadi dubban wajaje da 'yan takarar za su mammanna hotuna da takardunsu na yakin neman zaben a duk fadin kasar don isar wa jama'a da abubuwan da suke son yi idan an zabe su. Kamar yadda kuma ‘yan takaran sun yi amfani da kafafen yada labarai irin su facebook, whatsapp, telegram da sauransu wajen isar da shirye-shiryensu ga Jama’a din.


 


--------------------------------------/


 


A ci gaba da karin haske da kuma muhimmancin da wadannan zabubbuka guda biyu suke da shi, a cikin makon ne dai Jagoran juyin juya halin Musulunci Ayatullah Sayyid Ali Khamenei ya gana da dubban mutanen lardin Azarbaijan ta Gabas don tunawa da zagayowar shekarar yunkurin ranar 29 ga watan Bahman shekarar 1356 na mutanen garin Tabriz inda ya jaddada muhimmancin wadannan zabubbuka da kuma sake kiran al’umma da su fito kwansu da kwarkwatarsu yayin wannan zaben inda bayyana cewar: Fitowar mutane cikin basira da sanin ya kamata yayin zaben, zai zamanto bada wa makiya kasa a ido ne.


 


Har ila yau a cikin jawabin nasa, Jagoran juyin juya halin Musulunci ya ce tun farkon nasarar juyin juya halin Musulunci har zuwa yau din nan makiya sun yi iyakacin kokarinsu wajen kashe wa mutane gwuiwa da hana su fitowa zabubbukan da aka gudanar. Ayatullah Khamenei ya ce: Makiyan sun fara aiwatar da makircinsu dangane da wannan zaben na ranar 7 ga watan Esfand da kokarin cutar da matsayin majalisar kiyaye kundin tsarin mulki ta kasa da sanya alamun tambaya kan matsayar da ta dauka, wanda yace hakan yana nufin tabbatar da rashin ingancin zabubbukan da za a gudanar kenan. Jagoran ya kara da cewa: a lokacin da aka sanya alamun tambaya kan rashin ingancin zabe, hakan yana nufin majalisar shawarar Musulunci da za a kafa ta hanyar wannan zaben da kuma dokokin da za ta kafa duk za su zamanto marasa inganci Kenan.


 


Jagoran juyin juya halin Musulunci ya ci gaba da cewa: Manufar wannan makircin ita ce sanya kasar nan ta zamanto ta rasa majalisa da kuma dokoki, sannan tsawon shekaru hudu masu zuwa za su shagaltar da kwakwalan mutane da wannan lamarin.


 


A wani bangare na jawabin nasa kuwa, Jagoran juyin juya halin Musulunci yayi ishara da ci gaba da kiyayyar da Amurka take yi wa al’ummar Iran yana mai ishara da maganganun wasu jami’an Amurka na cewa za su ci gaba da kokari wajen ganin sun hana manyan ‘yan kasuwa na duniya zuba jari a Iran duk kuwa da yarjejeniyar nukiliya da kuma dage wa kasar takunkumi da aka yi wanda ya ce hakan yana nuni da irin tsananin kiyayyar da Amurka take yi da al’umma da kuma kasar Iran ne.


 


------------------------------------/


 


Masu saurare barkanmu da sake saduwa.


 


Daga cikin lamurran da suka dau hankula a Iran din cikin mako har da wani taro na bangarori hudu na ministocin man fetur da makamashi na kasashen Iran, Iraki, Venezuela da Qatar da aka gudanar a nan Tehran da nufin aiki tare tsakanin wadannan kasashen masu arzikin man fetur don kyautata yanayin kasuwar man fetur ta duniya da kuma daidaita yanayin farashin man fetur din a kasuwar duniya wanda cikin ‘yan watannin baya-bayan nan ya fuskanci matsala da kuma faduwa kasa warwas.


 


Bayan tattaunawar da ta gudana tsakanin ministocin a asirce, daga karshe dai ministan man fetur da makamashi na kasar Iran Malam Bijen Zangene ya bayyana wa manema labarai cewa: Jamhuriyar Musulunci ta Iran dai tana goyon bayan duk wani abin da za a yi wajen tattabatar da kasuwar man fetur din da kuma kara karfafa yanayin farashin danyen man fetur a kasuwar duniya.


 


Ministan man fetur din na Iran ya ci gaba da cewa: duk da cewa wannan taron wani mataki ne na farko a wannan bangaren da wajibi ne a ci gaba da aiwatar da wasu ayyuka don cimma wannan manufa da ake da ita, to amma duk wani aiki da za a yi tsakanin kasashen membobin kungiyar OPEC ta kasashe masu arzikin man fetur da ma wadanda ba membobin kungiyar ba da nufin kyautata yanayin kasuwar mai din wani lamari ne mai amfani sosai.


 


Cikin ‘yan watannin baya-bayan nan dai farashin man fetur din yayi wani irin faduwar da aka jima ba a ga irinsa ba, lamarin da ya sanya kasashen duniya musamman wadanda tattalin arzikinsu ya dogara a kan man fetur din gudanar da tarurruka daban-daban da nufin samo hanyoyin da za a bi wajen kyautata yanayin kasuwar.


 


------------------------------------/


 


Masu saurare barkanmu da sake saduwa.


 


Kamar yadda watakila kuka ji a farkon shirin, a cikin makon ne dai ministan tsaron kasar Iran Birgediya Janar Husain Dehqan ya kai ziyarar aiki kasar Rasha, bisa gayyatar da takwararsa na kasar Rashan yayi masa, da nufin ganawa da manyan jami’an kasar a ci gaba da karfafa alakar da ke tsakanin kasashen biyu musamman a bangaren tsaro.


 


A yayin wannan ziyarar, ministan tsaron na Iran tare da wata tawaga ta kwararru da jami’an sojin Iran ya gana da shugaban kasar Rashan Vladimir Putin, ministan tsaro Sergey Shoygu da kuma mataimakin firayi ministan kasar Dmitry Rogozin don tattauna batutuwan da suka shafi lamurran tsaro da soji bugu da kari kan lamurra na siyasa da suka shafi gabas ta tsakiya da ma duniya baki daya.


 


A yayin wannan ganawar, ministan tsaron kasar Rashan Sergey Shoygo ya bayyana cewar akwai tsohuwar alaka tsakanin kasashen Iran da Rasha yana mai cewa a halin yanzu ma akwai kyakkyawan yanayi da zai sanya ci gaba da fadada irin wannan alakar, yana mai cewa tun bayan ziyarar da shugaba Putin ya kawo Iran da kuma ganawar da suka yi da jagoran juyin juya halin Musulunci da shugaban kasar Iran, kasar Rasha ta bayyanar da aniyarta na kara karfafa alakar da ke tsakanin kasashen biyu.


 


Ziyarar ta ministan tsaron kasar ta Iran dai ta zo ne a daidai lokacin da ake ci gaba da tattaunawa tsakanin kasashen biyu dangane da batun wasu makamai na kare kasa da Iran take shirin saye daga wajen kasar Rasha, bugu da kari kuma kan alakar da ke tsakaninsu musamman dangane da rikicin kasar Siriya da kuma kokarin da kasashen biyu suke yi a fagen fada da ta’addanci musamman a kasar Siriya.


 


--------------------------------/


 


Masu saurare barkanmu da sake saduwa.


 


A bangaren diplomasiyya ma a cikin makon ne ministan harkokin wajen kasar Iran Dakta Muhammad Jawad Zarif ya tafi birin Brussel, babban birnin kasar Belgium don ganawa da takwararsa ta tarayyar Turai Federica Mogherini da tattaunawa kan batutuwa daban-daban da suka shafi bangarori biyu, musamman a matsayinta na babbar jami’a mai kula da aiwatar da yarjejeniyar da aka cimma tsakanin Iran da manyan kasashen duniya kan shirin nukiliyan zaman lafiya na kasar Iran.


 


Tun dai fara aiwatar da wannan yarjejeniyar ta nukiliya, Iran da Tarayyar Turai suka fara tattaunawa kan batutuwa daban-daban dangane da yadda za su karfafa alakokin da ke tsakaninsu musamman a bangaren tattalin arziki da kasuwanci, bugu da kari kan hanyoyin da za a bi wajen magance rikice-rikicen da suka kunno kai a yankin nan.


 


A wata ganawa da suka yi da manema labarai jim kadan bayan tattaunawar ta su, babbar jami’an siyasar waje ta Tarayyar Turai din ta ce sun yi amanna da cewa ta hanyar tattaunawa ce kawai za a iya magance matsalolin da suka kunno kai a Gabas ta tsakiya.


 


Shi ma a nasa bangaren ministan harkokin wajen kasar ta Iran ya sake jaddada matsayar Iran ta cewa tattaunawa ta siyasa ita ce kawai hanyar da za a iya bi wajen magance dukkanin rikicin da ke faruwa a yankin Gabas ta tsakiya musamman ma rikicin kasar Siriya.


Tags