Dec 19, 2017 04:31 UTC
  • Iran A Mako – 19-05-1396

Iran A Mako – 19-05-1396

Masu saurare assalamu alaikum barkanmu da warhaka da kuma sake saduwa cikin wani sabon shirin Iran A Mako shirin da ni Muhammad Awwal Bauchi na saba gabatar muku da shi a kowane mako inda muke leko muku wasu daga cikin batutuwa masu muhimmanci da suka faru a Iran cikin mako da fatan masu saurare suna cikin koshin lafiya kuma za  su kasance tare da mu tun daga farkon shirin har zuwa karshensa.

 

Kamar yadda muka saba ga wasu daga cikin batutuwan da suka fi daukan hankula cikin makon da za mu yi dubi cikinsu.

 

Ko shakka babu batun tabbatar da zaben shugaban kasar Iran Hasan Ruhani da Jagoran juyin juya halin Musulunci Ayatullah Sayyid Ali Khamenei yayi da kuma rantsar da shi da aka yi daga baya na daga cikin lamurran da suka fi daukar hankula don haka shi ne ma abin da shirin na mu na yau zai fi ba shi muhimmanci. Haka nan kuma a cikin makon ne dai Alhazan kasar Iran suka fara tashi zuwa kasar Saudiyya don sauke faralin bana, kamar yadda kuma a cikin makon ma dai jami'an Iran daban-daban sun mayar da martani dangane da ci gaba da keta yarjejeniyar nukiliyan da aka cimma da Iran da Amurka take yi, bugu da kari kan nasarorin da jami'an tsaron kasar Iran suka samu wajen dakile kokarin 'yan ta'adda na kawo hari kasar.

 

Wadannan watakila da ma wasunsu suna daga cikin batutuwan da za mu yi dubi cikinsu a shirin na mu na yau, don haka sai ku biyo mu sannu a hankali.

 

-----------------------------------/

 

Masu saurare barkanmu da sake saduwa.

 

Kamar yadda kuka ji a farkon shirin, a ranar Alhamis din da ta gabata ce aka gudanar da bikin tabbatar da shugaba Hasan Ruhani a matsayin shugaban kasar Iran na 12 a Husainiyar Imam Khumaini (r.a) da ke gidan Jagoran juyin juya halin Musulunci Ayatullah Sayyid Ali Khamenei.

 

Kamar yadda ya zo cikin doka ta 110 na kundin tsarin mulkin kasar Iran, amincewa da zaben shugaban kasa da kuma tabbatar da shi a matsayin shugaban kasa bayan jama'a sun zabe shi, daya ne daga cikin ayyukan da suke wuyan jagoran juyin juya halin Musulunci na kasar. A don haka aiki kowane shugaban kasa yana farawa ne daga lokacin da Jagoran ya amince da haka da kuma ba wa shugaban kasar da aka zaba din takardar hukuncin amincewar.

 

A saboda haka ne a ranar Alhamis din da ta gabata din aka gudanar da wannan bikin karkashin jagorancin Jagoran juyin juya halin Musulunci Ayatullah Sayyi Ali Khamenei.

 

A cikin takardar amincewar dai wanda shugaban ofishin jagoran Hujjatul Islam Muhammadi Golpaygani ya karanto, Jagoran ya bayyana cewar gagarumin zaben da aka gudanar din da kuma kuri'ar da jama'a suka kada wa zababben shugaban kasar wani lamari ne da ke nuni da imanin da mutane suke da shi da tsarin Jamhuriyar Musulunci, don haka ya kirayi shugaban kasar da ya ba da himma wajen tabbatar da adalci, goyon bayan marasa galihu da raunanan cikin al'umma, gudanar da dokokin Musulunci, tabbatar da hadin kan kasa, riko da koyarwar juyin juya halin Musulunci, karfafa karfi na kasa da dai sauransu.

 

Tape 1 Golpaygani

 

Hujjatul Islam Golpaygani kenan yayin da yake karanta hukuncin Jagoran juyin juya halin Musulunci.

 

Jim kadan bayan karbar takardar amincewar Jagoran, shugaban kasar Iran din Dakta Hasan Ruhani ya gabatar da jawabi da kuma bayyanar da mahangar sabuwar gwamnatin tasa.

 

Tape 2 Ruhani

 

Shugaba Ruhani ya bayyana cewa gwamnatin Iran tana kokari wajen tabbatar da wani juyi na tattalin arziki a cikin kasar da kuma karfafa alakarta da kasashen waje musamman kasashen makwabta, to sai dai kuma ya sake jaddada cewar ko da wasa Iran ba za ta taba mika kai da kuma yarda da kokarin da makiya suke yi na mai she ta saniyar ware a tsakankanin kasashen duniya ba.

 

Shi ma a nasa bangaren a jawabin da ya yi a wajen bikin, Jagoran juyin juya halin Musulunci Ayatullah Sayyid Ali Khamenei ya bayyana cewar Jamhuriyar Musulunci ta Iran ba ta taba kuma ba za ta taba mika kai ga mulkin kama-karya na ma'abota girman kai, yana mai cewa a halin yanzu Iran tana tsaya da kafafunta kyam sama da shekarun baya.

 

Tape 3 Agha

 

"A Yau Jamhuriyar Musulunci ta Iran ta kara samun karfi da tsayawa da kafafunta sama da yadda ta kasance a shekarun baya duk kuwa da irin wadannan takunkumin da kuma kiyayya da ake nuna mana. Ba wai kawai kiyayya ta fili ba, don kuwa wasu a fili suke nuna kiyayyar ta su irin su jami'an Amurka na yanzu da sauran wajaje, wasu kuma a boye suke nuna kiyayyar ta su….to amma cikin yarda da kuma taimakon Ubangiji don kara samun karfi da tsayin daka da kuma dogaro da kanmu".

 

Jagoran ya ci gaba da cewa: Wajibi ne jami'an gwamnati su yi la'akari da abubuwa uku, na farko yanayin tattalin arziki da yanayin rayuwar mutane, sannan su yi kokari wajen kyautata alakarsu da sauran kasashen duniya, na uku kuma su tsaya kyam wajen tinkarar girman kan ma'abota girman kan duniya.

 

--------------------------------/

 

To a bisa doka din dai bayan Jagoran juyin juya halin Musulunci ya tabbatar da shugaban kasar wajibi ne kuma ya yi rantsuwar kama aiki a gaban 'yan majalisar shawarar Musulunci ta kasar.

 

A ranar Asabar din da ta gabata ce dai shugaba Ruhanin yayi rantsuwar kama aiki din a gaban 'yan majalisar shawarar Musulunci din, a wani bikin da aka gudanar da a babban dakin taro na majalisar da ya sami halartar manyan baki da daga sama da kasashe 90 na duniya da suka hada da shugabannin kasashe, mataimaka, firayi ministoci, shugabannin majalisu, ministocin harkokin waje da sauran wakilan gwamnatoci daban daban na duniya.

 

An fara wannan bikin ne dai da jawabin shugaban majalisar shawarar Musulunci ta kasar Iran Dakta Ali Larijani wanda yayi maraba da manyan bakin da suka halarci taron musamman daga kasashe daban-daban na duniya da kuma bayyanar da mahangar Iran kan batutuwa daban-daban musamman a bangare na kasa da kasa, kana kuma sai ya bukaci shugaban kasar da ya zo yayi rantsuwar kama aiki a gaban Alkalin alkalai na kasar Ayatullah Sadiq Amoli Larijani kamar yadda doka ta tanada;

 

Tape 4 Ruhani Rantsuwa

 

Shugaba Hasan Ruhani kenan yayin da ya ke rantsuwar kama aiki inda yayi alkawarin zai kare mazhabar kasa, da tsarin jamhuriyar Musulunci da tsarin mulkin kasa, kuma zai yi aiki da dukkanin ikon da ya ke da shi wajen sauke nauyin da ya ke wuyansa da yi wa mutane hidima da daukaka matsayin kasa. Haka nan kuma zai kiyaye koyarwar addini da kyawawan halaye da goyon bayan gaskiya da kuma kare 'yancin da mutuminci mutane da hakkokinsu kamar yadda tsarin mulkin kasa ya tanada.

 

Bayan kammala rantsuwar kama aikin a matsayin shugaban kasar Iran na 12 kana kuma a wa'adin mulkinsa na biyu kuma na karshe, shugaba Hasan Ruhani yayi dogon jawabi inda yayi Karin haske dangane da mahangar sabuwar gwamnatin tasa da kuma abubuwan da za ta fi ba su muhimmanci, kamar yadda kuma yayi Karin bayani dangane da yarjejeniyar nukiliya da manyan kasashen duniya suka cimma da Iran yana mai shan alwashin kare hakkin Iran a wannan bangaren, yana mai cewa: Duniya ta kwana cikin sanin cewa Jamhuriyar Musulunci ta Iran zata dauki matakan da suka dace wajen maida martani kan duk wani saba yarjejeniyar da aka cimma tsakaninta da manyan kasashen duniya biyar gami da kasar Jamus kan shirin Iran din na nukiliya musamman irin Karen tsayen da Amurka take yi wa yarjejeniyar.

 

--------------------------------/

 

Masu saurare barkanmu da sake saduwa.

 

Kamar yadda watakila kuka ji a farkon shirin a cikin makon da ya wuce ne alhazan kasar Iran suka fara tashi don tafiya kasar Saudiyya da nufin sauke farali na bana bayan yarjejeniyar da aka cimma tsakanin Iran da kasar Saudiyya musamman dangane da kare lafiya da tsaron maniyyatan na Iran.

 

Shugaban hukumar alhazai ta kasar Iran Sa'id Auhadi ya bayyana cewar cikin 'yan kwanaki za a kammala kwashe alhazan kasar ta Iran kimanin 86,500 zuwa Saudiyya domin gudanar da aikin hajjin bana, bayan sun samu dukkanin horon da ya dace kan yadda ake gudanar da aikin hajji.

 

Har ila yau a wani jawabi da yayi yayin ganawa da jami'an aikin hajjin na Iran, Jagoran juyin juya halin Musulunci Ayatullah Sayyid Ali Khamenei ya bayyana cewar aikin hajj wata dama ce ta bayyanar da matsaya dangane da lamurran da suka shafi al'ummar musulmi musamman lamarin da ya shafi kasar Palastinu da kuma masallacin Kudus musamman irin hawar kawara da kuma keta hurumin masallacin da yahudawan sahyoniya suke yi cikin kwanakin nan.

 

A shekarar bara dai alhazan kasar Iran ba su sami damar tafiya aikin hajjin ba sakamakon kafar ungulun mahukuntan Saudiyya biyo bayan kisan gillan da aka yi wa maniyyatan Iran da na sauran kasashen musulmi a yayin aikin hajj na shekarar bara wancan.

 

------------------------------/

 

Masu saurare barkanmu da sake saduwa.

 

Jami'an tsaron kasar Iran sun sanar da samun nasarar kama wasu 'yan ta'adda guda 27 da suke da alaka da kungiyar ta'addancin nan ta Da'esh (ISIS) a kokarin da suke yi na kawo harin ta'addancin cikin kasar Iran din.

 

A cikin wata sanarwa da Ma'aikatar tsaron cikin gida da tattaro bayanan sirri na kasar Iran din ta fitar a yau din nan Litinin ta ce jami'an ma'aikatar sun sami nasarar ganowa da kuma kama 'yan wata kungiyar ta'addanci da suke da alaka da kungiyar Da'esh wadanda suke kokarin kai hare-haren ta'addanci a cikin kasar ta Iran musamman a wajajen addini a daidai lokacin da ake shirin rantsar da shugaban kasar Hasan Ruhani a ranar asabar din da ta gabata.

Sanarwar ta kara da cewa 10 daga cikin 'yan ta'addan an kama su ne a wajen kasar bisa taimakon hukumomin tsaron wata kasar makwabta, sannan sauran 17 din kuma a cikin Iran. Sanarwar ta ce 5 daga cikinsu ne aka tsara za su kai harin ta'addanci alhali sauran kuma za su taimaka musu da dukkanin abubuwan da suke bukata da kuma share musu fage.

A ranar Lahadin da ta gabata ma ma dai babban kwamandan sojin kasa na dakarun kare juyin juya halin Musulunci na kasar Iran din Birgediya Janar Mohammad Pakpour ya ce dakarun nasa sun sami nasarar tarwatsa 'yan wata kungiyar ta'addanci da suke son kawo hari cikin Iran din a kan iyakan kasar ta arewa maso yammaci inda suka hallaka wasu daga cikinsu da kuma kwace makamai masu yawa daga hannunsu.

----------------------------/

END

 

 

 

 

 

Tags