Dec 19, 2017 07:03 UTC
  • Iran A Mako – 21-12-2017

Masu saurare assalamu alaikum barkanmu da warhaka da kuma sake saduwa cikin wani sabon shirin Iran A Mako shirin da ni Muhammad Awwal Bauchi na saba gabatar muku da shi a kowane mako inda muke leko muku wasu daga cikin batutuwa masu muhimmanci da suka faru a Iran cikin mako da fatan masu saurare suna cikin koshin lafiya kuma za  su kasance tare da mu tun daga farkon shirin har zuwa karshensa.

 

Kamar yadda muka saba ga wasu daga cikin batutuwan da suka fi daukan hankula cikin makon da za mu yi dubi cikinsu.

 

Ko shakka babu batun birnin Qudus da sabon makircin da Amurka ta shigo da shi da nufin cutar da birnin ta hanyar sanar da shi a matsayin babban birnin HKI shi ne babban lamarin da ke ci gaba da daukar hankula a ciki da wajen Iran don haka shirin na mu na yau kan wannan batun ne zai yi dubi da kuma karin haske kansa. Don haka sai a biyo mu sannu a hankali.

 

------------------------------/

 

Masu saurare barkanmu da sake saduwa.

 

Da dama dai suna ganin matsayar da shugaban Amurka Donald Trump ya dauka na sanar da Qudus a matsayin babban birnin HKI a matsayin wani bangare na makirce-makircen Amurka da sahyoniyawa kan duniyar musulmi; wanda hakan na ci gaba da fuskantar tofin Allah tsine daga dukkanin bangarori na duniyar musulmin; ciki kuwa har da kasar Iran inda ake ci gaba da nuna rashin amincewa da wannan matsayar ta hanyar fitar da sanarwar Allah wadai, shirya tarurruka da jerin gwanon nuna goyon baya ga al'ummar Palastinu da kuma  tattaunawa da shugabanni da 'yan siyasa na kasashen waje da nufin kawo karshen wannan makircin.

 

A saboda haka ne ma shugaban kasar Iran Dakta Hasan Ruhani ya halarci taron shugabannin kasashen musulmi membobi a kungiyar hadin kan kasashen musulmi ta OIC da aka gudanar a birnin Istanbul na kasar Turkiyya a kwanakin baya. A yayin wannan zaman dai shugaba Ruhani ya bayyana muhimmancin Palastinu a matsayinta na babbar matsalar duniyar musulmi a halin yanzu inda ya ce: A halin yanzu dai musulmi ba su da wata hanyar magance matsalolin da suke fuskanta face hanyar hadin aiki da aiki tare a tsakaninsu. A saboda haka ya zama wajibi su daga murya guda wajen yin Allah wadai da wannan mataki na kuskure da shugaban Amurkan ya dauka. Don haka sai ya ce Iran dai a shirye take, ba tare da wani sharadi ba, wajen hada gwiwa da sauran kasashen musulmi wajen tabbatar da hakkokin al'ummar Palastinu da kuma 'yanto kasar daga mamayar sahyoniyawa.

 

Haka nan kuma  yayin da yake Magana kan wajibcin hadin kai wajen tinkarar makircin HKI, ya bayyana cewar wajibi ne Amurka ta ji a jikinta cewa al'ummar musulmi ba za su zama 'yan kallo ba dangane da abin ya shafi makomar Palastinu da Kudus

 

Daga nan sai shugaban ya gabatar da wasu shawarwari guda bakwai ga sauran kasashen musulmin da suka hada da (1). Wajibi ne taron yayi Allah wadai da wannan matsaya ta Amurkan (2). Wajibcin hadin kai tsakanin musulmi don fuskantar kalubalen da suke fuskanta. (3). Ya kamata a nuna wa Amurka cewa duniyar musulmi ba za su zamanto 'yan kallo ba kan abin da ya shafi kasar Palastinu, ci gaba da hakan zai zamanto yana da nasa sakamakon a fage na siyasa. (4). Wajibi ne gwamnatocin kasashen Musulmi su kara kaimi wajen nuna rashin amincewa da wannan matsaya ta Trump musamman a ganawar da suke yi da kawayen Amurka na Turai. (5). A sake dawo da matsalar Palastinu ya zama shi ne babban lamarin da ya shafi duniyar musulmi. (6). Wajibi ne MDD musamman Kwamitin tsaron majalisar su taka gagarumar rawa wajen kawo karshen wannan matsaya ta shugaban Amurkan (7). Wajibi ne kasashen musulmi su ci gaba da sanya ido kan sahyoniyawa da ayyukan da suke gudanarwa da kuma shirya tarurruka na gaggawa don tattauna lamarin da kuma daukar matsayar da ya dace.

 

-----------------------------------/

 

Sama da shekaru sittin kenan kasar Palastinu da wasu bangarori na wasu kasashen musulmi suka kasance karkashin mamayar sahyoniyawa. Shi kansa garin Kudus din ya kasance karkashin mamayar sahyoniyawa din ne a shekarar 1967. Tsawon wadannan shekaru al'ummr Palastinun in ma dai sun zama 'yan gudun hijira ko kuma sun ci gaba da zama a yankunan da aka mamaye din karkashin mummunan nuna wariya da barazana ga lafiya da tsaronsu ko kuma su kasance cikin mafi munin killacewa a Zirin Gaza. Ita kuwa Amurka, tsawon wannan lokacin ta kasance mai tursasa wa al'ummomin yankin musamman Palastinawan amincewa da mamayan da aka yi musu a bangare guda kuma da ba da kariya ido rufe da yahudawa 'yan share guri zauna din.

 

Amurkawa da sahyoniyawan suna ci gaba da gudanar da shiri na makircinsu a kan al'ummar musulmi. Ta hanyoyi daban-daban suna kokarin raba birnin na Kudus daga sauran kasashe na musulmi da kuma kawar da irin siffa ta Musulunci da yake da ita. Gwamnatocin Amurkan daban-daban sun ta wannan kokarin sai dai sun gaza. Duk da cewa gwamnatin Amurkan ta yanzu ta taka wani mataki wajen cimma wannan manufa ta hanyar sanar da Kudus din a matsayin babban birnin 'Isra'ilan', to amma ci gaba da nuna rashin amincewar da musulmi da ma sauran kasashe na duniya musamman na Turai suke nunawa wa wannan matsaya ta Trump wani lamari ne da ke tabbatar wa Amurkan da Isra'ila cewa lalle hakan ba lamari ne da za a amince da shi ba.

 

Siyasar Jamhuriyar Musulunci ta Iran, wacce ta samo asali daga kundin tsarin mulkin kasar, ta ginu ne bisa nuna goyon bayan al'ummar Palastinu da dukkanin al'ummomin da ake zalunta. Tafarkin da Iran take kai musamman dangane da matsalar Palastinu shi ne goyon bayan kungiyoyin gwagwarmayar Musulunci da kuma tsayin daka wajen tinkarar da Isra'ila ma'abociyar mamaya da wuce gona da iri.

 

Wannan tushe da ake da asali cikin addinin Musulunci da kuma 'yan adamtaka yana isar wa makiya da sakon cewa al'ummar Iran a koda yaushe sannan kuma a kowane lokaci kuma a kowane waje da bukata ta taso ba za su taba yin kasa a gwiwa ba wajen ba da kariya ga Musulunci, Palastinu da kuma Kudus ba, sannan kuma suna da karfin tinkarar masu kokarin wuce gona da iri kan hakkokin al'ummar musulmi.

 

A saboda haka ne ma shugaban kasar ta Iran Dakta Hasan Ruhani cikin jawabin da yayi a wajen taron shugabannin kasashen musulmi na kungiyar OIC ya bayyana cewar Iran dai a shirye take, ba tare da wani sharadi ba, wajen hada gwiwa da sauran kasashen musulmi wajen tabbatar da hakkokin al'ummar Palastinu da kuma 'yanto kasar daga mamayar sahyoniyawa.

 

---------------------------------/

 

Dubi baya zai nuna mana cewa HKI a koda yaushe kan kasance cikin shirin neman tabbatar da ikonta na gaba daya a kan Kudus ta hanyar dogaro da goyon baya da kuma taimakon Amurka. Sun gudanar da shirye-shirye mabambanta da suka hada da korar asalin mazauna wajen, kwace filaye da gidaje, mayar da gurbin Palastinawa da aka kora a wani waje da yahudawa sahyoniyawa da aka shigo da su da nufin sauya yanayin al'ummar birnin na Kudus bugu da kari kan ruguza duk wata alama ta tarihi ta Musulunci da ke wajen da kuma ci gaba da cin mutumcin da take hurumin wannan waje mai tsarki.

 

A halin yanzu dai babbar manufar Amurka da Isra'ila it ace raunana kungiyoyin gwagwarmaya musamman kungiyar Hizbullah ta kasar Labanon a matsayinta na tushen gwagwarmaya wajen tinkarar wuce gona da irin haramtacciyar kasar Isra'ilan.

 

Tsawon shekaru goma da suka gabata, gwamnatin sahyoniyawa ta Isra'ila cikin yakukuwa guda hudu da suka yi da Hizbullah ta kasar Labanon da kungiyoyin gwagarmyar Palastinawa sun sha kashi ainun. Daga cikin irin wannan shan kashin kuwa sun hada har da shan kashin da suka yi tun farko kafa kungiyar ta Hizbullah a shekarar 1982 har zuwa tilasta musu barin kasar Labanon da aka yi a shekara ta 2000, haka nan da kashin da suka sha a lokacin yakin 33 a shekara ta 2006, kamar yadda a Gaza ma sun kasha din a lokuta mabambanta.

 

Irin wadannan kashin da sahyoniyawan suka sha ne ya sanya Amurka da Isra'ilan shigo da wasu sabbin makirce-makirce wadanda daga cikinsu har da batun masallacin Kudus da shugaban Amurkan ya taso da shi a halin yanzu.

 

-----------------------------------/

 

Irin wadannan abubuwan da suke faruwa da kuma rikon sakainar kashin da wasu gwamnatocin musulmi suke yi wa lamarin Palastinu da kuma birnin na Kudus ne ya sanya Iran matsa kaimi wajen sanar da matsayarta da kuma kara tabbatar da aniyarta na taimakon al'ummar Palastinu musamman ma kungiyar gwagwarmayar Palastinawan.

 

Hakan ne ma ya sanya kwamandan dakarun Qudus na dakarun kare juyin juya halin Musulunci a Iran (IRGC) Laftanar Janar Qasim Sulaimani ya bayyana cewa rundunarsa a shirye take ta tallafawa kungiyoyi masu gwagwarmaya da yahudawan Sahyoniya a Palasdinu.

 

Janar Sulaimani ya bayyaa hakan ne a wata tattauna da yayi da kwamandojin dakarun Izzuddin Qassam reshen soja na kungiyar Hamas da kuma Quds Brigades bangaren soji na na kungiyar jihadul Islami. 

 

Janar Sulaimani ya kara jaddada wa kungiyoyin cewa dakarun Quds a shirye suke su kare masallacin Qudus ta hanyar taimakawa dakarun Palasdinawa da suke gwagwarmaya da yahudawa a halin yanzu a cikin Palasdinu da aka mamaye. 

 

Daga karshen Janar Sulaimani ya kammala da cewa tallafin da rundunarsa zata bawa Palasdinawan ya hada dukkan bangarorin da suke bukata.

 

--------------------------------/

 

END

 

Tags