Dec 19, 2017 04:44 UTC
  • Iran A Mako – 23-09-1396

Iran A Mako – 23-09-1396

Masu saurare assalamu alaikum barkanmu da warhaka da kuma sake saduwa cikin wani sabon shirin Iran A Mako da ke leko muku wasu daga cikin muhimman al'amurran da suka faru a Iran din cikin mako wanda ni Muhammad Awwal Bauchi na saba  gabatar muku da shi a kowane makon da fatan masu saurare suna cikin koshin lafiya, kuma za su kasance tare da mu tun daga farkon shirin har zuwa karshensa.

 

Kamar yadda muka saba ga wasu daga cikin batutuwan da za mu yi dubi cikin wasu daga cikinsu gwargwadon yadda lokaci zai ba mu dama.

 

Daga cikin batutuwan da suka dau hankula cikin makon har da batun makon hadin kan musulmi da aka gudanar don tunawa da ranakun haihuwar Ma'aiki (s.a.w.a) da kuma jawabin da Jagoran juyin juya halin Musulunci yayi kan wannan batun. Haka nan kuma wani batun da ya dau hankula cikin makon kuma yake ci gaba da dauka shi ne batun birnin Qudus da matakain da shugaban Amurka ya dauka kan birnin, wanda kusan ma shi ne abin da shirin na mu na yau zai ba shi muhimmanci da jin matsayar da Iran ta dauka kan wannan batun. A fagen diplomasiyya ma dai babban batun da ya fi daukar hankula shi ne ziyarar aiki da sakataren harkokin wajen Birtaniyya ya kawo nan  Iran.

 

Wadannan watakila da ma wasunsu suna daga cikin batutuwan da za mu yi dubi kansu cikin shirin na mu na yau. Sai a biyo mu sannu a hankali.

 

--------------------------------/

 

Masu saurare barkanmu da sake saduwa.

 

Kamar yadda kuka ji a farkon a ranar Larabar makon da ya wuce ne aka gudanar da bukukuwan ranar haihuwar Ma'aikin Allah (s.a.w.a) da kuma jikansa Imam Sadiq (a.s) a duk fadin kasar Iran wanda kuma hakan ne ya kawo karshen bukukuwan makon hadin kan al'ummar musulmi da aka gudanar don tunawa da ranar haihuwar Ma'aiki din (s.a.w.a).

 

Daga cikin bukukuwan da aka gudanar a wannan ranar har da ganawa da Jagoran juyin juya halin Musulunci Ayatullah Sayyid Ali Khamenei yayi da manyan jami'an kasar Iran da kuma baki mahalarta taron Makon Hadin Kai na kasa da kasa da aka gudanar a nan Tehran inda ya bayyana muhimmancin hadin kai tsakanin musulmi da kuma yin taka  tsantsan da makirce makircen makiya musamman Amurka da sahyoniyawa kan musulmi musamman matsayar da shugaban Amurka ya dauka kan birnin Qudus.

 

A jawabin da ya gabatar yayin wannan ganawar Jagoran juyin juya halin Musulunci Ayatullah Sayyid Ali Khamenei ya bayyana cewar kokarin da Amurka ta ke yi na mayar da birnin Qudus a matsayin helkwatar haramtacciyar kasar Isra'ila wata gazawa ce daga bangarensu don kuwa matsalar Palastinu wani lamari ne da ya fi karfinsu, yana mai jaddada cewar ko shakka babu za a 'yanto kasar Palastinu daga mamayar sahyoniyawa; yana mai cewa makiyan dai babu wani abin da za su iya don kuwa lamarin Palastinu ya riga da ya fice daga hannunsu.

 

Ayatullah Khamenei ya ci gaba da cewa siyasar Amurka a yankin Gabas ta tsakiya ita ce haifar da fitina da yake-yake don tabbatar da tsaro da zaman lafiyar haramtacciyar kasar Isra'ila, to sai dai abin bakin cikin shi ne a halin yanzu ana samun wasu shugabanni da 'yan siyasa da suke taimakon Amurka wajen cimma wannan manufa nata.

 

Abin bakin cikin shi ne cewa a halin yanzu akwai wasu shugabanni da masana a wannan yanki da suke rawa da bazar Amurka, dukkanin abin da take so shi suke aikatawa. Suna gudanar da abubuwan da suke cutar da al'ummar musulmi da kuma Musulunci. Wannan ita ce siyasarsu ita ce abin da suke aikatawa….to mu dai muna musu nasiha da su nesanci hakan.

 

Jagoran yayi ishara da yadda wadannan kasashe suka kirkiro kungiyoyin 'yan takfiriyya duk dai da nufin gwara kan musulmi wanda ya ce ko shakka babu hakan wani lamari ne da zai koma kansu, wato kaikayi zai koma kan mashekiya. Don haka ya kirayi al'ummar musulmi da su kara kaimi wajen tabbatar da hadin kai a tsakaninsu wanda hakan shi ne abin da zai haifar musu da ci gaba da kuma tsira daga makirce-makircen makiyansu

 

-------------------------/

 

Har ila yau dangane da batun murnar haihuwar Ma'aikin Allah (s.a.w.a) din, Jagoran juyin juya halin Musulunci Ayatullah Sayyid Ali Khamenei yayi afuwa ga wasu fursunoni da kuma rage wa'adin zaman gidan yari ga wasu don tunawa da murnar zagayowar Maulidin Manzon Allah (s).

 

A wata sanarwa da ofishin Jagoran juyin juya halin Musuluncin ya fitar a ranar Talatar da ta gabata ya bayyana cewar saboda zagayowar ranar Maulidin Manzon Allah (s) Jagoran juyin juya halin Musuluncin, Ayatullah Khamenei ya amince da bukatar da shugaban Ma'aikatar shari'a kuma alkalin alkalai na Iran Ayatullah Sadeq Amoli Larijani ya gabatar masa na yin afuwa da  kuma rage hukuncin zaman gidan yari da aka yanke wa wasu fursunoni 1700 da suke zaman gidan yari.

 

A kwanakin baya ne da Ayatullah Larijanin, cikin wata wasika da ya aike wa Jagoran ya bukace shi da yayi afuwa ga wadannan fursunoni don murnar zagayowar ranar haihuwar Ma'aikin Allah (s).

 

A kowace shekara dai Jagoran juyin juya halin Musuluncin ya kan yi afuwa ko kuma rage wa'adin zaman gidan yarin wasu daga cikin fursunonin da ake tsare da su don nuna farin ciki da ranar haihuwar Fiyayyen Halittan, Manzon Allah Muhammad (s).

 

----------------------------------------/

 

Masu saurare barkanmu da sake saduwa.

 

Kamar yadda kuka ji a farkon shirin daga cikin batutuwan da suke ci gaba da daukar hankula a ciki da wajen kasar Iran shi ne batun sanarwar da shugaban Amurka Donald Trump yayi na daukar birnin Qudus a matsayin babban birnin HKI wanda jami'an Iran daban daban suna ci gaba da mayar da martani kan hakan da kuma yin Allah wadai da shi.

 

Shugaban kasar ta Iran Dakta Hasan Ruhani yana daga cikin jami'an kasar da ya fara jan kunnen shugaban Amurkan kan wannan matsaya da ya dauka inda ya bayyana cewar wajibi ne kasashen musulmi su hada kansu waje guda don tinkarar wannan lamari.

 

Shugaba Ruhani ya bayyana hakan ne a wata tattaunawa da yayi da takwararsa na kasar Turkiyya Recep Tayyib Erdogan, wanda ya bugo masa waya don gayyatarsa taron shugabannin kasashen musulmi na kungiyar OIC don tattaunawa wannan lamarin inda ya ce a irin wannan yanayi ya zama wajibi kasashen musulmi da al'ummominsu su hada kansu waje guda da kuma daukar matakin da ya dace wajen tinkarar wannan haramtacciyar matsaya kana kuma mai hatsarin gaske da Amurka ta dauka.

Shugaban na Iran ya ci gaba da cewa lamarin Palastinu da kuma fada da irin zaluncin da haramtacciyar kasar Isra'ila take yi wa Palastinawa shi ne babban lamarin da ke gaban duniyar musulmi.

 

Ita ma a nata bangaren Ma'aikatar harkokin wajen kasar ta Iran ta yi kakkausar suka da kuma Allah wadai da matsayar da shugaban Amurka Donald Trump ya dauka na mayar da ofishin jakadancin Amurka birnin Quds a matsayin babban birnin haramtacciyar kasar Isra'ila tana mai cewa hakan wani lamari ne da zai kunna wutar sabon boren intifada a kasar Palastinun.

 

A cikin wata sanarwa da ta fitar a jim kadan bayan sanarwar Trump din, Ma'aikatar harkokin wajen kasar ta Iran ta yi kakkausar suka ga wannan mataki na Amurka tana mai bayyana hakan a matsayin wani gagarumin karen tsaye ga dokokin da kudururruka na kasa da kasa.

 

Sanarwar ta kara da cewa: A koda yaushe Jamhuriyar Musulunci ta Iran ta kasance tana jaddada cewa Isra'ila ita ce ummul aba'isin dukkanin rashin tsaron da yankin Gabas ta tsakiya ke fuskanta sakamakon ci gaba da mamaye kasar Palastinu da take yi da kuma irin goyon baya ido rufe da Amurka take ba ta.

 

Sanarwa ta karkare da kiran kasashe da cibiyoyin kasa da kasa da su ci gaba da matsa wa Amurka lamba dangane da batun mayar da ofishin jakadancin nata zuwa birnin Qudus ko kuma sanar da birnin na Qudus a matsayin helkwatar haramtacciyar kasar Isra'ila.

 

A bangare guda kuma kwamandan dakarun Qudus na dakarun kare juyin juya halin Musulunci a Iran (IRGC) Laftanar Janar Qasim Sulaimani ya bayyana cewa rundunarsa a shirye take ta tallafawa kungiyoyi masu gwagwarmaya da yahudawan Sahyoniya a Palasdinu.

 

Janar Sulaimani ya bayyaa hakan ne a wata tattauna da yayi da kwamandojin dakarun Izzuddin Qassam reshen soja na kungiyar Hamas da kuma Quds Brigades bangaren soji na na kungiyar jihadul Islami. 

 

Janar Sulaimani ya kara jaddada wa kungiyoyin cewa dakarun Quds a shirye suke su kare masallacin Qudus ta hanyar taimakawa dakarun Palasdinawa da suke gwagwarmaya da yahudawa a halin yanzu a cikin Palasdinu da aka mamaye. 

 

Daga karshen Janar Sulaimani ya kammala da cewa tallafin da rundunarsa zata bawa Palasdinawan ya hada dukkan bangarorin da suke bukata.

 

------------------------------/

 

Masu saurae barkanmu da sake saduwa.

 

Kamar yadda kuka ji a farkon shirin a ranar Asabar din da ta gabata ce sakataren harkokin wajen Birtaniya, Boris Johnson, ya fara wata ziyarar aiki a nan Iran  don ganawa da manyan jami'an kasar ciki kuwa har da takwaransa na Iran Muhammad Jawad Zarif da sauransu, inda zasu tattauna batutuwa daban daban da suka shafi kasashen biyu da kuma wadanda suka shafi yankin nan musamman batun kasar Yemen da Siriya da kuma yarjejeniyar nukiliyan Iran da aka cimma da manyan kasashen duniya.

 

Jim kadan bayan isowarsa Iran, sakataren harkokin wajen Birtaniyyan ya gana da takwaransa na Iran Dakta Muhammad Jawad Zarif inda ya jaddada cewar Kasar Birtaniyya tana ci gaba da aiki da yarjejeniyar ta Nukiliya da aka cimma tsakanin Iran da manyan kasashen duniya, kamar yadda kuma ya bayyana fatan da yake da shin a ganin an

 bunkasar alaka a tsakanin Iran da Birtaniya ta fuskoki da dama.

 

Har ila yau a rana ta biyu ta ziyarar tasa, Mr. Johnson ya gana da shugaban kasar Iran Dakta Hasan Ruhani inda suka tattauna kan batutuwa da dama, daga ciki har da yadda kasashen biyu zasu aiwatar da yerjejeniyar shirin Nukliyar kasar Iran wacce ake kira (JCPOA) a takaice, da kuma matsalolin da yankin gabas ta tsakiya ta ke fama da su.

 

Hari ila yau kuma sakataren harkokin wajen na Birtaniyya ya gana da shugaban majalisar shawarar Musulunci ta kasar Iran Dakta Ali Larijani da babban sakataren majalisar koli ta tsaron kasar Iran Ali Shamkhani da kuma shugaban hukumar kula da makamashin nukiliya ta Iran din Dakta Ali Akbar Salehi.

------------------------------------/

 

Tags