Oct 04, 2017 07:32 UTC
  • Iran A Mako 05-10-2017

Masu saurare assalamu alaikum barkanmu da warhaka da kuma sake saduwa cikin wani sabon shirin Iran A Mako da ke leko muku wasu daga cikin lamurran da suka faru a Iran cikin mako wanda ni Muhammad Awwal Bauchi na saba gabatar muku da shi da fatan masu saurare suna cikin koshin lafiya kuma za su kasance tare da mu tun daga farkon shirin har zuwa karshensa.

Kamar yadda muka saba ga wasu daga cikin kanun labaran abubuwan da suka farun wadanda za mu yi dubi cikinsu.

Daga cikin batutuwan da suka farun har da gudanar da bukukuwan juyayin Ashura da aka gudanar a duk fadin kasar Iran. Haka nan kuma a cikin makon ne aka kawo karshen makon kariya ta kasa da aka gudanar don tunawa da kallafaffen yakin da kasar Iraki ta kallafawa Iran. Har ila yau kuma a cikin makon ne dai aka gudanar da jana'izar Shahid Muhsin Hujjaji daya daga cikin dakarun kare juyin juya halin Musulunci na Iran da ya tafi Siriya don ba da kariya ga wajaje masu tsarki na kasar daga hare-haren 'yan ta'adda. Haka nan kuma wani batun da ke ci gaba da daukar hankula shi ne batun maganganun jami'an Amurka kan yarjejeniyar nukiliya da kuma zaben raba gardamar da Kurdawan Iraki suka gudanar da ke barazana ga hadin kan kasar Irakin da kuma tsaron lafiyar sauran kasashen da suke makwabtaka da ita.

Wadannan watakila da ma wasunsu suna daga cikin batutuwan da za mu yi dubi cikinsu a shirin na mu na yau. Sai a biyo mu sannu a hankali.

-----------------------------------/

Masu saurare barkanmu da sake saduwa.

Wannan makon dai yayi daidai da ranakun juyayin shahadar Imam Husaini (a.s) da sahabbansa su 72 a Karbala a saboda haka ne aka gudanar da bukukuwan juyayin wannan musiba a duk fadin kasar Iran.

Daga cikin wajajen da aka gudanar da wadannan tarurrukan har da Husainiyar Imam Khumaini (r.a) da ke gidan jagoran juyin juya halin Musulunci Ayatullah Sayyid Ali Khamenei taron da ya sami halartar jagoran da sauran manyan jami'an gwamnatin Iran bugu da kari kan sauran al'ummar gari.

An fara gudanar da wadannan tarurrukan na juyayin a Husainiyar ta Imam Khumaini (r.a) ne daga daren bakwai na watan Muharram din har na tsawon kwanaki 6 inda malamai suke gabatar da wa'azi dangane da wannan yunkuri na Imam Husaini (a.s) kana mawaka da masu yabon Ahlulbaiti (a.s) kuma su zo su gabatar da wakoki da bayanin asalin abin da ya faru da Zuriyar Annabi (s.a.w.a) a ranar Ashuran a Karbala.

Baya ga Husainiyar ta Imam Khumaini (r.a), har ila yau al'ummar Iran din sun ci gaba da gudanar da wadannan tarurruka na juyayi a masallatai da Husainiyoyi da dakunan tarurruka bugu da kari kan tituna don nuna aihininsu ga abin da ya sami Zuriyar Annabi din.

A ranar 10 ga watan Muharram na shekara ta 61 bayan hijirar Ma'aiki (s.a.w.a) ne Imam Husaini (a.s), limamin Shi'a na uku tare da iyalai, dangi da kuma sahabbansa su 72 ne suka yi shahada a kasar Karbala din bayan da sojojin Yazid dan Mu'awiyya suka tsare su Karbala din da hana su ruwan sha har na kwanaki uku, kana daga baya kuma suka kashe su da kuma daukar mataye da kananan yaran su a matsayin fursunonin yaki inda suka kai su garin Kufa kana daga baya kuma suka wuce da su zuwa Damashq fadar mulkin Umayyawan.

------------------------------------------./

Masu saurare barkanmu da sake saduwa.

Makon da ya wuce din nan dai yayi daidai da zagayowar ranar da tsohuwar gwamnatin Iraki ta kallafawa Iran yaki na tsawon shekaru 8 da nufin ganin bayan jaririyar gwamnatin Musulunci da aka kafa a kasar, to sai dai kuma sun gaza cimma wannan manufa ta su sakamakon jaruntaka da tsayin daka da sojojin Iran suka nuna tsawon wannan lokaci duk kuwa da karancin makamai da kayan aiki bugu da kari kan goyon bayan na kasa da kasa da suka fuskanta.

A ranar 22 ga watan Satumban 1980 ne sojojin Iraki, da tunanin cewa cikin mako guda za su iya isowa har birnin Tehran, suka kaddamar da gagarumin hare-hare kan kasar Iran. Gwamnatin Irakin dai ta yi amfani da sojoji kasa na bataliyoyi 12, tankunan yaki da sauran motocin daukar sojoji 4500, jiragen yaki 360 da kuma wasu 400 na daukar kayayyakin soji da sauran nau'oi daban-daban na makamai yayin wannan farmaki. Taha Yasin Ramadhan, firayi ministan Iraki na wancan lokacin ya sanar da cewa manufar wannan yakin ita ce fada da juyin juya halin Musulunci na Iran, yana mai cewa yakin ba shi da alaka da yarjejeniyar 1975 ko kuma wasu 'yan kilomitoci, face dai manufar ita ce kawo karshen gwamnatin Jamhuriyar Musulunci.

Tsawon shekaru takwas na yakin dai, manyan kasashen duniya masu tinkaho da karfi sun kasance suna goyon bayan gwamnatin Iraki da kuma ba ta dukkanin abin da take bukata wajen ganin bayan gwamnatin Musulunci ta Iran din, to sai dai irin ruhin tsayin daka da sadaukarwa da neman shahada da al'ummar Iran suka nuna ya hana masu wuce gona da irin cimma wannan bakar aniya ta su.

A cikin wani sako da ya fitar don tunawa da makon kariya din, Jagoran juyin juya halin Musulunci Ayatullah Sayyid Ali Khamenei ya bayyana cewar:

"Girmar matsayin shahada a matsayinta na wani kolin matsayi da mutum zai iya kaiwa ta yi daidai ne da girmar sadaukarwa da kyakkyawar niyyar da mutum yake da ita; wanda hakan ne ya ke jan shahidi zuwa ga fagen jihadi inda daga karshe dai ya ke dandana zakin da ke cikin shahadar".

-------------------------------------/

Masu saurare barkanmu da sake saduwa.

Kamar yadda kuka ji a cikin makon nan ne dai aka gudanar da jana'izar Shahid Muhsin Hujaji daya daga cikin dakarun kasar Iran da 'yan kungiyar ta'addancin nan ta Daesh suka kama da yanka shi a kasar Siriya, inda aka bisne shi da garin haihuwarsa na Najafabad.

Rahotanni sun bayyana cewar tun da safiyar Alhamis din da ta gabata ce dai dubun dubutan al'ummar garin Najafabad din cikin yanayi na juyayi sanye da bakaken kaya suka fito kan titunan garin don maraba da shahidin da yi masa rakiya zuwa makwancinsa na karshe.

Rahotanni sun bayyana cewar garin na Najafabad dai ya cika da manyan jami'an soji da na siyasa na Iran, wadanda suka hada da Manjo Janar Husain Salami, mataimakin babban kwamandan dakarun kare juyin juya halin Musulunci na Iran wadanda suka iso garin na Najafabad don halartar jana'izar Shahid Muhsin Hujaji, inda bayan sa'oi na jana'izar aka yi masa salla da kuma bisne shi.

A ranar larabar makon da ya wuce din ne dai aka iso da gawar tasa daga birnin Mashad zuwa birnin Tehran inda daga cikin wadanda suka halarci wajen da aka ajiye gawar har da Jagoran juyin juya halin Musulunci Ayatullah Sayyid Ali Khamenei da sauran manyan jami'an gwamnati.

Jagoran juyin juya halin Musuluncin ya bayyana cewar: Dukkanin shahidai suna da girman matsayi a wajen Allah, to sai dai wata siffa da wannan matashin shahidi ya kebanta da ita shi ne cewa Allah Madaukakin Sarki Ya daukaka sunansu da mai she shi wata alama abar girmamawa.

A kwanakin baya ne dai 'yan kungiyar ta'addancin nan na Da'esh suka kama shahid Muhsin Hujaji a kasar Siriya inda ya tafi can din don ba da kariya ga wajaje masu tsarki na Musulunci da suke wajen daga hareharen 'yan Da'esh din suke son rusa, inda suka masa yankan rago bayan azabtarwar da suka yi masa.

----------------------------------/

Masu saurare barkanmu da sake saduwa.

Kamar yadda kuka a ji a farkon shirin a cikin makon dai jami'an Iran daban-daban suna ci gaba da mayar da martani dangane da maganganu da barazanar da shugaban Amurka da sauran jami'an kasar suke yi na yin watsi da yarjejeniyar nukiliya da manyan kasashen duniya ciki kuwa har da ita Amurka suka cimma da Iran, inda suka ja kunnen Amurkan kan abin da zai iya biyo bayan wannan mataki na su.

A nasa bangaren Ministan harkokin wajen kasar Iran Dakta Muhammad Jawad Zarif ya bayyana cewar Iran za ta iya ficewa daga yarjejeniyar nukiliyan da ta cimma da manyan kasashen duniya a shekara ta 2015 matukar dai Amurka ta fice daga yarjejeniyar.

Ministan harkokin wajen na Iran ya bayyana hakan ne a wata hira da yayi da gidan talabijin din Al-Jazeera na kasar Qatar inda ya ce matukar dai Amurka ta yanke shawarar ficewa daga yarjejeniyar ta nukiliya, to Iran ma tana da zabin ficewa daga yarjejeniya da ma wasu zabin na daban.

Kalaman na ministan harkokin wajen na Iran suna zuwa ne a daidai lokacin da shugaban Amurka Donald Trump da wasu jami'an gwamnatin nasa suke ta maganar ficewa daga yarjejeniyar ta nukiliya da aka cimma tsakanin Iran da wasu kasashe shida na duniya da suka hada da Amurkan, Rasha, China, Birtaniya, Faransa da kuma Jamus.

Jami'an Iran ma dai sun ce matukar dai Amurka ta fice daga yarjejeniya to kuwa za su dau mataki kan hakan.

Jami'an sauran kasashen da aka cimma yarjejeniyar da su dai sun nuna damuwarsu kan wannan shiri na Amurka da cewa hakan yin karen tsaye ne ga kudurin kwamitin tsaron MDD wanda bisa yardarsa ne aka cimma yarjejeniyar.

--------------------------------/

Masu saurare barkanmu da sake saduwa.

Yanzu bari mu je ga bangare na karshe na shirin. Inda kamar yadda kuka ji a farkon shirin jami'an Iran daban-daban sun ci gaba da bayyana matsayar gwamnatin Iran dangane da batun kuri'ar raba gardamar da Kurdawan kasar Iraki suka gudanar a kokarin da jami'an yankin suke yi na ballewa daga kasar Irakin inda jami'an na Iran suka bayyana rashin amincewar Iran ga duk wani kokari na cutar da hadin kan kasar Iran.

Ministan harkokin wajen kasar Iran Dakta Muhammad Jawad Zarif ya jaddada cewa: Zaben neman ballewar yankin Kurdawan Iraki daga kasar babbar barazana ce ga zaman lafiya da tsaron yankin gabas ta tsakiya.

A bangare guda kuma Manyan hafsoshin sojojin kasar Iran da Iraki sun yi wata ganawa ta musamman a nan birnin Tehran don tattauna batun zaben raba gardamar da aka gudanar a yankin Kurdawan aksar Iraki da nufin balle yankin daga kasar Iraki.

Rahotanni sun ce babban hafsan sojojin na Iran Manjo Janar Mohammad Baqeri ya gana da takwararsa na kasar Irakin Manjo Janar Othman al-Ghanmi wanda ya iso nan Tehran a jiya Laraba tare da wata tawaga  ta sojojin kasar Irakin da nufin tattaunawa da jami'an Iran kan zaben raba gardamar da kuma batun fada da ta'addanci don daukan matakan da suka dace.

Kafin hakan ma dai babban hafsan sojojin na Iran Manjo Janar Mohammad Baqeri ya gana da wata tawaga ta manyan sojojin kasar Turkiyya wadanda suka zo nan Tehran don tattauna batutuwa daban-daban ciki kuwa har da batun zaben raba gardamar na yankin Kurdestan na kasar Irakin.

Kasashen Iran da Iraki da Turkiyya dai duk sun bayyana rashin amincewarsu da zaben raba gardamar suna masu jaddada wajibcin ci gaba da tabbatar da hadin kan kasar Irakin a matsayin kasa guda kamar yadda kuma suka sha alwashin daukar matakan da suka dace kan yankin na Kurdestan matukar jami'an yankin suka ci gaba da wannan shiri na su na ballewa daga kasar Irakin.

----------------------------/

END

Tags