Feb 02, 2016 15:08 UTC
  • Zanga zangar Allah wadai da Saudiyya saboda kashe Sheikh Nimr
    Zanga zangar Allah wadai da Saudiyya saboda kashe Sheikh Nimr

Masu saurare assalamu alaikum barkanmu da warhaka da kuma sake saduwa cikin wani sabon shirin Iran A Mako da ke leko muku wasu daga cikin muhimman al’amurran da suka faru a Iran cikin mako wanda ni Muhammad Awwal Bauchi na saba gabatar muku da shi a kowane mako da fatan masu saurare suna cikin koshin lafiya.

Kamar yadda muka saba ga wasu daga cikin muhimman al’amurran da suka farun kana mu yi karin haske kansu daga baya.

 

Daga cikin batutuwan da suka fi daukar hankula a kasar Iran cikin makon nan ko shakka babu shi ne batun sanarwar da kasar Saudiyya ta yi na katse alakarta ta dipmasiyya da kasar Iran biyo bayan ci gaba da nuna rashin amincewa da kashe shehin malamin nan na kasar Sheikh Nimr Baqir al-Nimr da mahukuntan Saudiyyan suka yi, wanda shirin na mu na yau zai fi ba shi muhimmanci ne da kuma irin maganganun da jami’an Iran daban-daban suka yi kan wannan lamarin. Har ila yau kuma wani batun da shi ma yake ci gaba da daukan hankula a ciki da wajen kasar ta Iran shi ne batun zabubbukan majalisun kwararru na jagoranci da kuma majalisar shawarar Musulunci na kasar da za a gudanar a nan gaba a kasar da kuma irin yadda ma’abota girman kan duniya musamman Amurka suke kokarin ganin sun yi tasiri a cikin zaben.

 

Wadannan watakila da wasu batutuwan ma na daban su ne za mu yi dubi cikinsu a shirin na mu na yau. Sai a biyo mu sannu a hankali.

 

-----------------------------------/

 

Masu saurare barkanmu da sake saduwa.

 

Kamar yadda watakila kuka ji a farkon shirin daya daga cikin batutuwan da ke ci gaba da daukan hankula a cikin gidan Iran kai har ma daga waje shi ne batun zaben ‘yan majalisar kwararru ta jagoranci wacce take da alhakin zabe da kuma sanya ido kan ayyukan jagoran juyin juya halin Musulunci na kasar haka nan da kuma zaben ‘yan majalisar shawarar Musulunci ta kasar Iran wacce take da alhakin kafa dokoki a kasar.

 

A makon da ya wuce ne dai aka gama rajistar ‘yan takaran da suke son tsayawa takara a dukkanin wadannan majalisu guda biyu masu muhimmanci ga kasar ta Iran inda a halin yanzu ake ci gaba da gudanar da sauran aiki na tantance dacewa ko rashin dacewar mutanen da suka yi rajistar sunayensu da bayyana aniyarsu ta tsayawa takarar zaben, wanda cibiyoyin da doka ta dora musu alhakin hakan da suka hada da majalisar kiyaye kundin tsarin mulki na kasar da kuma ma’aikatar cikin gida suke ci gaba da yi.

 

Bisa la’akari da irin muhimmancin da wadannan majalisu biyu suke da shi ne wajen ayyana makomar kasar Iran, ya sanya a duk lokacin da irin wannan zabe ya karato, su kuma makiya al’ummar Iran din musamman Amurka a nan ne suke baza komarsu da nufin yin duk abin da za su iya wajen ganin sun yi tasiri cikin zaben don cimma bakaken manufofinsu, hakan ne ma ya sanya jami’an kasar daban-daban suke ci gaba da kiran al’umma da su yi taka tsantsan dangane da wannan makiricin.

 

Hakan ne ma ya sanya Jagoran juyin juya halin Musulunci Ayatullah Sayyid Ali Khamenei cikin wata ganawa da yayi da limaman masallatan Juma’a na duk fadin kasar Iran a ranar Litinin din da ta gabata yayi karin haske dangane da muhimmancin zaben da kuma kiran al’ummar kasar da su fito kwansu da kwarkwatarsu don kada kuri’arsu don zaban mutanen da suka dace, kamar yadda kuma ya ja kunne dangane da kokarin makiya din wajen tasiri cikin zaben.

 

A bangaren karshe na jawabin nasa, Ayatullah Khamenei yayi ishara da kokarin yin tasiri cikin zaben da za a gabatar din da Amurkawa suke kokarin yi inda ya ce: Amurkawa suna kokarin ganin al'ummar Iran sun nesanci manufofin juyin juya halin Musulunci da kuma rungumar manufofinsu.

 

Jagoran ya ci gaba da cewa: Don cimma wannan manufar, Amurkawa sun damfara fatansu ga wannan zaben. To amma al'ummar Iran masu girma da kuma sanin ya kamata, shin a lokacin zabe ne ko kuma ba lokacin zabe ba, za su yi dukkanin abubuwan da suka saba wa manufofin Amurka ne, sannan kuma kamar yadda suka saba a wannan karon ma za su bada musu kasa a ido.

 

-----------------------/

 

Masu saurare barkanmu da sake saduwa.

 

Kamar yadda kuka ji a farkon shirin daga cikin batutuwan da suka dau hankula a cikin kasar Iran kuma suke ci gaba da yi har da batun zartar da hukuncin kisan a kan babban shehin malamin nan na kasar Saudiyya wato Sheikh Nimr Baqir al-Nimr da gwamnatin Saudiyya ta yi a ranar Asabar din da ta gabata, lamarin da ya fuskanci tofin Allah tsine daga bakin jami’ai daban-daban na Iran da kuma al’ummar kasar.

 

A nasa bangaren Jagoran juyin juya halin Musulunci Ayatullah Sayyid Ali Khamenei yayi Allah wadai da kisan da aka yi wa Shehin malamin inda ya ce ko shakka babu mahukuntan Saudiyyan za su fuskanci fushin Ubangiji dangane da zubar da jinin wannan bawan Allah da suka yi ba tare da hakki ba.

 

Jagoran ya bayyana hakan ne a wani jawabi da ya yi a safiyar ranar Lahadin da ta gabata a wajen darasin Bahasul Kharij na fikihu da yake bayarwa ne inda ya kirayi duniya baki daya da ta sauke nauyin da ke wuyanta dangane da wannan danyen aikin da kuma wasu makamantan hakan da gwamnatin Saudiyya take aikatawa a kasashen Yemen da Bahrain. Jagoran ya ci gaba da cewa: Ko shakka babu nan ba da jimawa ba za a ga tasirin jinin wannan shahidi da aka zalunta da aka zubar ba bisa hakki ba. Lalle Allah zai dau fansa a kan shugabannin Saudiyya.

 

Baya ga jagoran juyin juya halin Musulunci, har ila yau manyan jami’an kasar ta Iran daban-daban da suka hada da shugaban kasa, shugaban majalisa, shugaban ma’aikatar shari’a da kuma kusan dukkanin maraja’ai da manyan malaman kasar ta Iran sun yi Allah wadai da wannan danyen aiki na mahukuntan Saudiyyan.

 

Su ma a nasu bangaren al’ummar kasar Iran da suka hada da daliban jami’oi da na makarantun addini sun gudanar da zanga-zangogi don yin Allah wadai da wannan danyen aikin, kamar yadda kuma wasu gundun al’ummar suka taru a gaban ofishin jakadan Saudiyyan da ke nan Tehran da kuma karamin ofishin jakadancinsu dake birnin Mashad lamarin da ya kai ga an samu faruwar ‘yan rikice rikice da ya kai ga sanya wuta a wadannan ofisoshin.

 

 -----------------------------------/

 

A nata bangaren kasar Saudiyyar wacce daman tana cikin fushi sakamakon irin nasarorin da Iran ta samu musamman a yayin tattaunawar nukiliya da ta yi da manyan kasashen duniya duk kuwa da kulle-kullen da gwamnatin Saudiyyan bisa hadin bakin HKI suka yi wajen ganin ba a cimma wannan yarjejeniyar ba, ta yi amfani da wannan yanayi na irin zanga-zangogin nuna rashin amincewa da danyen aikin nata da al’ummar Iran suka yi da wannan batu na sanya wuta a ofisoshin jakadancin nata da ke cike da alamun tambaya wajen sanar da cewa ta katse alakarta ta diplomasiyya da Iran.

 

Wannan sanarwar dai ta fuskanci mayar da martani daga jami’an Iran daban-daban bugu da kari kuma kan al’ummar kasar ta Iran wadanda mafiya yawansu ma sun yi na’am ne da hakan sakamakon irin cutar da su da mahukutan Saudiyyan suka yi a lokuta daban-daban na baya-bayan nan shi ne hatsarin da ya faru a yayin aikin hajji a Mina inda daruruwan Iraniyawa suka yi shahada.

 

Martanin farko-farko kan wannan mataki na Saudiyya ya fito ne daga bakin Mataimakin ministan harkokin wajen kasar Iran kan harkokin kasashen larabawa da na Afirka Amir Husain Abdullahiyan wanda ya bayya cewar, yanke alaka da Iran da masarautar Saudiyya ta yi, ba zai taba rufe laifin da ta tafka na kashe malamin addini mai kira zuwa ga adalci da zaman lafiya ba, wato Sheikh Nimr Baqir al-Nimr.

 

Shi ma a nasa bangaren mataimakin shugaban kasar ta Iran Ishak Jahangiri ya bayyanar Matakin da mahukuntan Saudiyya suka dauka na hanzarta yanke alakar jakadanci da kasar Iran mataki ne da babu tunani cikinsa, kuma Saudiyya ce zata cutu kan matsayin da ta dauka saboda Jamhuriyar Musulunci ta Iran ba kanwar lasa ba ce.

 

Shi ma Alkalin alkalai na kasar Iran Ayatullah Sadiq Amoli Larijani ya bayyana cewa Jamhuriyar Musulunci ta Iran ba ta da wata bukatuwa da kasar Saudiyya da ma iyayengijinta, don haka katse alakarta da Iran babu ta hanyar da zai cutar da Iran, kamar yadda kuma ya bayyana Saudiyya a matsayin kanwa-uwar gamin duk wasu ayyukan ta'addancin da ke faruwa a duniyar musulmi don biyan bukatun ma'abota girman kan duniya da kuma haramtacciyar kasar Isra'ila a kasashen Musulmi.

 

Da dama daga cikin masana da masu sharhi kan lamurran yau da kullum suna ganin wannan mataki na yanke alakar diplomasiyya da Iran da Saudiyya ta yi a matsayin wani ihu bayan hari don kuwa kamar yadda mai magana da yawun gwamnatin Iran ya fadi ne babu wata rawa da Saudiyya take takawa a fagen ci gaban tattalin arzikin Iran ballantana a ce katse alakar zai cutar da kasar Iran. Da dama suna ganin wannan mataki a matsayin wani abu kawai na farfaganda ta rashin mafadi hakan ne ma ya sanya wasu suke ganin biyo sahun Saudiyya wajen katse alaka da Iran da wasu kasashe suka yi musamman irin su Sudan da Djibouti da Bahrain a matsayin wani matsin lamba daga wajen Saudiyya don kuwa babu wani tasiri da katse alakar da wadannan kasashen suka yi da Iran face ma dai watakila su ne za su cutu.

 

------------------------------------/

 

END

Tags