Sanar Da Sakamakon Zaben Nijar Zagaye Na Faro
Jama’a masu Assalamu Alaikum barkanku da warhaka barkanmu kuma da sake saduwa da kua cikin wanann shiri na Afirka a mako.
Shirin dai kan yi dubi kan wasu daga cikin muhimman batutuwa da suka shafi nahiyar Afirka, inda a yau da yardar Allah za mu duba wasu daga cikin batutuwa da suka shafi zaben da aka gudanar a jamhuriyar da kuma halin da ake bayan sanar da sakamakon zabe, kamar yadda kuma zamu leka Najeriya, da wasu kasashen gwargwadon yadda lokaci y aba mu hali, da fatan za a kasance tare da mu.
………………………………..
A ranar Juma’a da ta gabata ce dai hukumar zamen jamhuriyar Nijar CENI ta sanar da cewa, za a je zagaye na biyu a zaben shugaban kasa a ranar 20 ga watan Maris mai kamawa, bayan da aka kasa samun ko daya daga cikin 'yan talarar da ya samu kashi 50% na kuri'un da aka kada. Za a je zagaye na biyu ne tsakanin Isufu Muhammadu da ke gaba da kashi 48.4%, da kuma mai biye masa Hama Amadu da ke kashi 19% na dukkanin kuri'in.
……………………..
To dangane da wannan batu kuma mun ji mahangar wasu daga cikin jam’iyyun da suka fafata a wannan zabe, Jam’iyyar PNDS ita ce za ta fatata da Lumana a zageye na biyu, kuma ya zuwa ko wadanne shirye-shirye jam’iyyar take domin fuskantar zabe zagaye na biyu, ga abin da Iro Sani kusa a jam’iyyar ya sheda abokin aikinmu Hassan Baraka.
……………………………
To su kuma a nasu bangaren kawance adawa wadanda suka sha alwashin marawa Malam Hama Amadu baya a zagaye na biyu, ko ya suka ga zaben da ya gudana? Kuma wane shiri suke yi domin zabe zagaye na biyu tsakanin dan takararsu Hama Amdu da kuma Muhammad Isufu? Ga dai abin da Malam Sedu kusa a jam’iyyar Lumana ya sheda mana ……………………..
To tanzu kuma bari mu ji ra’ayoyin wasu daga cikin al’ummar ta jamhuriyar Nijar da suka kada kuri’a da kuma fatar da suke da ita a zaben da za a gudanar a zagaye na biyu
…………………………
Daga batun zabe a Jamhuriyar Nijar kuma bari mu nufi tarayyar Najeriya, domin duba daya daga cikin batutuwa wanda shi ma yake da aalaka da siyasa kai tsaye, shi ne batun alkawalin da ‘ya’yan jam’iyyar APC mai mulki suka yi ma matasa marassa aikin yi na ba su N5000 a duk wata, matukar dai suka zabi jam’iyyar har ta kai ga nasara, inda a halin yanzu matasan marassa aikin ji suke jiran su ga wannan alkawali a aikace, to amma kuma a nasa bangaren shugaba Buhari ya tabbatar da cewa shi bai yi wannan alkawali ba a lokacin yakin neman zabe, duk kuwa da cewa bai kore cewa wasu yan jam’iyar sun yi wa matasa wanann alkawali ba.
Dr. Kabir mato na jami’ar Abuja masani kan harkokin siyasa a Najeriya, ya bayyana mana yadda yake kallon wannan lamari.
…………………………………
To a can kasar Gambia kuwa shugaban kasar yahaya Jame ne ya sanar da aniyarsa ta sake tsayawa takarar shugabancin kasar a karo na biyar, bayan kwashe shekaru fiye da 20 kan karagar shugabancin kasar.
Malam Nuhu aruka daya daga cikin jagororin farar hula a jamhuriyar Nijar kuma masani kan harkokin siyasa a kasashen yammacin nahiyar Afirka, ya bayyana mana mahagarsa kan wannan batu.
…………………..
To jama’a masu sauraee lokacin da muke da shi ya riga ya kawo jiki, dole a nan zamu dasa aya sai Allah ya hada mu a mako nag aba, inda za a ji mu dauke da wani shirin, kafin lokacin nake yi muku fatan alkhairi, wassalamu alikum alaikum warahmatullah.