Feb 02, 2016 15:11 UTC
  • Dawowar Imam Khumaini Iran
    Dawowar Imam Khumaini Iran

Masu saurare assalamu alaikum barkanmu da warhaka da kuma sake saduwa cikin wani sabon shirin Iran A Mako da ke leko muku wasu daga cikin muhimman al’amurran da suka faru a Iran cikin mako wanda ni Muhammad Awwal Bauchi na saba gabatar muku da shi da fatan kuna cikin koshin lafiya.

Bisa la’akari da kusatowar ranakun nasarar juyin juyin juya halin Musulunci a kasar Iran don haka shirin mu na yau zai yi dubi ne kan batutuwan da suka shafi wannan juyin da kuma irin kalubalen da ya fuskanta

Tun dai daga lokacin da Juyin Juya Halin Musulunci na Iran ya yi nasara ranar 11 ga watan Fabrairun 1979 zuwa wannan lokaci da ake bukukuwan shekaru 25 da wannan nasarar, juyin ya fuskanci al’amurra da matsaloli daban-daban. Wasu daga cikin waxannan matsaloli kuwa, idan aka lura da irin girma da yadda suka bijiro, sun isa su kawo qarshen wata gwamnati ko kuma wani juyi. To sai dai kuma bisa dogaro da Ubangiji da qarfin al’umma, Jamhuriyar Musulunci ta Iran ta samu nasarar kawo qarshen irin waxannan matsaloli da suka taso mata.

Yanzu bari mu yi dubi cikin wasu daga cikin waxannan matsaloli:

Xaya daga cikin manyan abubuwan da suka faru jin kaxan bayan samun nasarar Juyin Juya Halin Musulunci shi ne mamaye ‘Ofishin Jakadancin’ (ko kuma mu ce ofishin leqen asiri) Amurka a Tehran da kame ma’aikatan ofishin da wasu xalibai mabiya tafarkin Imam suka yi. Su dai waxannan ma’aikata na ‘ofishin jakadancin’ Amurkan sun fake da kariya ta diplomasiyya da suke da ita, inda suka mai da wannan ofishi zuwa wajen leqen asiri da kuma qoqarin yin zagon qasa wa jaririyar gwamnatin Musulunci da dawo da tsohuwar gwamnatin kama karya da aka kawar. Wannan kame ‘ofishin jakadanci’ dai da xaliban suka yi ya samu goyon bayan al’ummar Iran da kuma shi kansa mu’assasin Juyin Juya Halin Marigayi Imam Khumaini (r.a). Kamar yadda kuma al’umma sun qara nuna goyon bayansu bayan da xaliban suka nuna abubuwan da suka samu a ofishin da ke nuni da irin ayyukan leqen asirin da ake gudanarwa a wajen. Duk da cewa dai Amurkan ta ta barazana da kuma matsin lamba wa Iran kan ta sako waxannan ‘yan leqen asiri da suka sanya rigar diplomasiyya, to sai dai Imam da al’ummar Iran sun tsaya qyam wajen ci gaba da tsare su, suna masu kafa wa Amurkan wasu sharuxxa kafin a sako su. Hakan kuwa ya faru don sai da Amurkan ta amince da wannan sharaxi na cewa ba za ta tsoma baki cikin harkokin cikin gidan Iran ba kafin aka sako waxannan ‘yan leqen asiri.

Haka nan kuma, a daidai lokacin da ake cikin tsakiyar wannan rikici tsakanin Amurka da Iran a qarshe-qarshen shekarar 1979, sai ga wata matsalar kuma a hankali a hankali ta fara kunno kai, ita ce kuwa matsalar qungiyar ‘Mujahidin Khalq’ ko kuma qungiyar da aka fi sani da ‘Qungiyar Munafukai’.

Ita dai wannan qungiya, saboda irin karkacaccen tunani da ‘yan qungiyar suke da shi da kuma son rai da ya mamaye su, sun yi qoqarin dawo da komai gare su da kuma kame dukkan al’amurran gudanarwa a Iran, don haka ne ma suka goyi bayan shugaban Iran na wancan lokacin da daga baya aka tsige wato Bani Sadr don cimma burorinsu. Irin wannan tunani na ‘yan wannan qungiya dai bai samu goyon bayan Imam da al’ummar Iran ba, face ma dai al’umma xin suna ganinsu ne a matsayin munafukai waxanda suke qoqarin mai da hannun agogo baya. Kai a taqaice ma dai da wannan suna na munafukai suke kiransu, wannan ya sa sun gagara cimma nasara. Wannan rashin nasara da suka samu ya sanya ‘yan qungiyar gudanar da ayyukan ta’addanci da jami’ai da malamai a wancan lokacin, inda suka samu nasarar kashe da dama daga cikin jami’an gwamnati da kuma malamai masu riqo da hukumar. To sai dai kuma ba su jima suna yi ba, don kuwa irin qyamar da al’umma suke musu da kuma fuskantarsu da suke yi a duk lokacin da suka haxu da su ya tilasta musu gudu daga Iran da samun mafaka wajen wasu qasashe da suke adawa da gwamnatin musuluncin musamman ma daga tsohon shugaban qasar Iraqi Saddam Husaini.

-------------------------------------------/

To sai dai kuma babu shakka mafi girman matsalar da Juyin Juya Halin Musuluncin ya fuskanta kana kuma ya iya gamawa da shi, shi ne kallafaffen yaqin shekaru takwas da gwamnati kama karya ta Saddam Husaini ta kallafa wa Iran. Idan dai ana iya tunawa, a shekarar 1980 ne Saddam, bisa umarni da goyon bayan Amurka, tsohuwar Tarayyar Sobiyeti da kuma da dama daga cikin qasashen Turai da na larabawa, ya qaddamar da gagaruman hare-hare a kan Iran da nufin ganin bayan gwamnatin Musuluncin da aka kafa, a daidai lokacin da ba wani shiri na azo a gani da Iran xin take da shi sakamakon makirce-makircen maqiya da kuma irin riqon sakainar kashin da tsohuwar gwamnatin zalunci ta ‘ya’yan gidan Pahlawi suka yi da kuma miqa kai ga maqiya.

Da farko da Saddam da iyayengijinsa sun xauka cewa cikin ruwan sanyi za su gama da Iran, to sai dai kuma wasa-wasa sai wankin hula ya kai su dare, sakamakon irin qarfin jagoranci na Imam Khumaini (r.a) da kuma goyon bayan al’umma, sannan kuma ga kariya irin ta Ubangiji Maxaukakin Sarki. A wannan lokaci dai dubun-dubatan matasa sun fito fili kusan hannu rabbana wajen fuskantar maqiya waxanda suke da dukkan nau’oi na muggan makamai, inda daga qarshe dai jaruman al’ummar Iran suka samu nasara a kan abokan gaba da fatattakansu.

Ko shekara guda dai ba a yi ba da kawo qarshen wannan kallafaffen yaqi, kwatsam sai ga wata babbar matsala kuma ta fuskanto wannan juyi. Wannan matsala kuwa ita ce rasuwar Mu’assasi kuma Jagoran wannan juyi, Marigayi Imam Khumaini (r.a) a ranar 4 ga watan Yunin 1989, wannan rasuwa dai ba wai kawai ga al’ummar Iran ba face ma dai dukkan al’ummar musulmi da raunanan duniya ta girgiza su matuqar girgizawa. Maqiya wannan juyi dai da man shekara da shekaru suna jiran faruwar wannan lamari da kuma samun wannan dama, suna tunanin cewa rasuwar Imam dai za ta kawo qarshen wannan juyi da kuma faxuwar Jamhuriyar Musuluncin da ya kafa.

To amma ta Allah ba ta su ba, don kuwa sai ga shi miliyoyin al’ummar Iran sun fito wajen jana’izar Imam da kuma jaddada mubaya’arsu ga wannan kira na Imam da kuma yin alqawarin kare manufofin Imam har qarshen rayuwarsu. Wani abin da kuma ya qara sa maqiyan suka yanke qauna daga cimma wannan manufa ta su, shi ne zaven Ayatullah al-Uzma Sayyid Aliyu Khamene'i da Majalisar Qwararru Mai Zaben Jagora ta yi a matsayin wanda zai gaji Imam (r.a). Wannan zave dai ya tabbatar wa al’umma da kuma maqiyan cewa tafarkin Imam dai na nan daram kuma za a ci gaba da shi, hakan kuwa saboda masaniyar da suke da shi cewa Ayatullah Khamene'i dai na daga cikin xaliban Imam na kurkusa ko kuma ma mu ce wanda ya fi dacewa da wannan matsayi saboda tsoron Allah, hangen nesa, ilmi, sanin madafan gudanarwa da dai sauran siffofin da ya ke da su.

--------------------------------------------------/

Har ila yau kuma, xaya daga cikin matsaloli da barazanar da Juyin Juya Halin Musulunci ya dinga fuskanta kuma ya ke ci gaba da fuskanta ita ce barazanar gwamnatin Amurka a vangarori daban-daban na siyasa, tattalin arziqi, tsaro, farfaganda da dai sauransu. Amurka dai tun bayan samun nasarar Juyin Juya Halin Musulunci da kawar da gwamnatin kama karyar Shah, ta rasa haramtattun manufofinta a Iran, don haka ne ta xau wannan mataki na barazana don ganin ko za ta iya kawar da gwamnatin Musulunci. Daga cikin matakan soji da Amurkan ta xauka a kan Iran har da qoqarin shirya juyin mulki wa gwamnatin Musulunci, waxanda kuwa suka fito fili daga cikin irin waxannan makirce-makirce, su ne, qoqarin juyin mulkin shekarun 1980 da 1983, to sai dai kuma da taimakon Allah da kuma tsayin dakan al’umma, an samu nasarar kawo murqushe wannan makirci.

Takunkumin tattalin arziqi ma dai na daga cikin hanyoyin da Amurkan ta bi wajen matsa wa Iran lamba, wanda ya faro ne tun daga farko-farkon nasarar Juyin Juya Halin har zuwa wannan lokaci kullum zai daxa qaruwa yake yi, to sai dai shi ma wannan makirci, kamar sauran makirce-makircen bai sa Iran xin ta miqa wa Amukawan kai ba. Takunkumi na baya-bayan nan shi ne kan batun shirin nukiliyan zaman lafiya na Iran wanda Amurkan da kawayenta suka mai da shi wata dama ta ci gaba da takurawa Iran da yi mata matsin lamba duk dai da nufin cimma waxannan baqaqen manufofinsu. Har zuwa lokacin da suka ga dai babu sarki sai Allah, wato sun gagara cimma waxannan manufofin. Don haka sai suka koma ga hanyar tattaunawa da Iran da nufin kawo qarshen wannan lamarin. Daga qarshe dai vangarorin biyu sun cimma yarjejeniyar da ta fara aiki a kwanakin baya inda Iran ta taqaita wasu vangarori na shirin nukiliyan nata a vangare guda kuma aka xage mata dukkanin takunkumin da aka sanya mata da suke da alaqa da shirin nukiliyan.

Wata hanyar kuma da Amurkan ta ke bi wajen baqanta wannan juyi da kuma qasar Iran xin ita ce hanyar farfaganda da yaxa qarairayi. Daga cikin irin waxannan qarairayi har da ikirarin take haqqoqin ‘yan’Adam, goyon bayan ayyukan ta’addanci da kuma qoqarin mallakan makaman qare dangi. Batun take haqqoqin ‘yan’Adam da goyon bayan ayyukan ta’addanci dai batutuwa ne da suka jima suna yawo da su, to amma su ma dai ba su sami karvuwa a wajen da dama daga cikin al’ummomin duniya ba, musamman ganin yadda Amurkan ta ke take haqqoqin bil Adama a cikin da wajen Amurkan da kuma yadda ta ke goyon bayan qungiyoyin ‘yan ta’adda irinsu Haramtacciyar Kasar Isra'ila da dai sauransu.

---------------------------------------/

Waxannan dai kaxan kenan daga cikin matsalolin da Juyin Juya Halin Musulunci na Iran ya fuskanta cikin sama da shekaru 36 na wannan juyi.

Ko ba a faxi ba dai yadda Juyin Juya Halin ya samu damar magance matsaloli masu wahalan gaske da ya fuskanta yana nuni ne da qarfin da tsarin Musulunci ya ke da shi wajen magance matsaloli. Xaya daga cikin dalilan da suka sanya samun nasara da ficewa daga cikin matsalolin da aka ta fuskanta cikin waxannan shekaru 36, babu shakka, shi ne jagoranci. Don kuwa duk cikin waxannan shekaru muna iya ganin rawar da jagoranci ya taka wajen magance kusan dukkan matsalolin da aka fuskanta. A bisa tsarin mulki na Iran, Jagora dai, baya ga masaniya, sanin al’amurran gudanarwa, sanin ya kamata, dole ne kuma ya kasance mutum ne ma’abucin tsoron Allah da sanin haddodin Ubangiji. Don haka ne a duk lokacin da wata matsala ta kunno kai, jami’ai da sauran al’umma sukan miqa al’amurransu ga jagoranci don magance ta.

Wani rukuni kuma na gwamnatin Iran xin wanda shi ma ya taka rawa nesa ba kusa ba wajen magance matsalolin da aka shiga, shi ne qarfi na al’umma. Don kuwa ta hanyar goyon bayan al’umma ne wannan juyi ya samu nasara, sannan kuma ta hanyar goyon bayan al’umma xin ne aka samu nasarar magance matsaloli daban-daban irinsu kallafaffen yaqi, rasuwar Imam da kuma barazanar yau da kullum na Amurka, a irin waxannan lokuta dai al’umma xin sun kasance tare da jagoransu da kuma sauran jami’an gwamnati wajen fuskantar waxannan matsaloli.


Tags