Mar 25, 2016 06:35 UTC
  • Iran A Mako 27-12-1394

Masu saurare assalamu alaikum barkanmu da warhaka da kuma sake saduwa cikin wani sabon shirin Iran A Mako da ke leko muku wasu daga cikin muhimman abubuwan da suka faru a Iran cikin mako wanda ni MuhammadAwwal Bauchi na saba gabatar muku da shi da fatan masu saurare suna cikin koshin lafiya kuma za su kasance tare da mu tun daga farkon shirin har zuwa karshensa.

Kamar yadda muka saba ga kanun wasu daga cikin abubuwan da za mu yi dubi cikinsu a shirin na mu na yau. 

Daga cikin abubuwan da suka dau hankula a cikin makon har da ganawar da Jagoran juyin juya halin Musulunci yayi da ‘yan majalisar kwararru ta jagoranci ta Iran inda yayi magana kan wasu lamurra masu muhimmancin gaske, wani lamarin kuma da ya dau hankula shi ne bukukuwan girmama shahidai da aka gudanar inda shugaban kasa yayi bayani mai muhimmanci musamman dangane da batun kare wajaje masu tsarki na Ahlulbaiti da ‘yan ta’adda suke hari. Har ila yau kuma daga cikin lamurran da suka dau hankulan har da atisayen soji da dakarun kare juyin juya halin Musulunci na kasar Iran suka gudanar inda suka gwada wasu sabbin makamai masu linzami da suka kera. A bangaren diplomasiyya da kasa da kasa ma dai a cikin makon ne aka gudanar da wani taro na kungiyar hadin kan kasashen musulmi dangane da batun Palastinu inda tawagar Iran karkashin jagorancin ministan waje Muhammad Jawad Zarif ta bayyana mahangar Iran kan hanyoyin da za a magance matsalar Palastinu.

Wadannan watakila da ma wasunsu suna daga cikin batutuwan da za mu yi dubi cikinsu a shirin na mu na yau. Sai ku biyo mu sannu a hankali.

--------------------------------/

Masu Saurare barkanmu da sake saduwa.

Kamar yadda watakila kuka ji a farkon shirin a ranar Alhamis din da ta gabata ce Jagoran juyin juya halin Musulunci Ayatullah Sayyid Ali Khamenei ya gana da shugaba da kuma membobin majalisar kwararru ta jagoranci ta Iran, inda a jawabi mai muhimmancin gaske da yayi, yayi Karin haske dangane da abubuwa masu muhimmanci da ya kamata jami’ai da al’ummar Iran su lura da su a wannan yanayi da ake ciki yana mai cewa: Hanya guda ta cimma ci gaba na hakika ita ce karfafa tsarin cikin gida a fagaren tattalin arziki, al'adu da siyasa, kiyaye siffofi da koyarwa na juyin juya hali, yunkuri irin na jihadi, kiyaye mutumci da daukaka ta kasa da kuma nesantar narkewa cikin yanayi na kasa da kasa mai hatsarin gaske.

Har ila yau kuma yayin da yake ishara da irin kiyayya da kasashen yammaci suke nunawa Iran tun farkon nasarar juyin juya halin Musulunci har zuwa yau da kuma irin yadda a halin yanzu suke kokarin sakin fuska wa Iran amma da nufin cimma wata manufa ta su, Jagoran juyin juya halin Musulunci ya kirayi jami’ai da al’ummar Iran da su yi taka tsantsan inda yace: Ni dai ba wai ina goyon bayan yanke alaka da kasashen yammaci ba ne, to amma wajibi ne mu san da wa muke mu'amala? Saboda kuwa tun da fari kasashen yammaci suka shata daga da nuna kiyayya ga al'ummar Iran, a halin yanzu kuma suna kokarin neman yin tasiri ne a cikin kasar. Don haka Jagoran ya ce wajibi ne a yi taka tsantsan da wannan shiri na makiya din da suke bin hanyoyi daban-daban da suka hada da tasiri na ilimi, al'adu da tattalin arziki da kuma neman kulla alaka da jami'oi da masana, halartar tarurruka wadanda a zahiri na kara wa juna sani ne kan ilimi amma da manufar samun yin tasiri a cikin kasa da kuma aikewa da ‘yan leken asirinsu da sunan ayyuka na al'adu.

Har ila yau kuma yayin da ya koma kan zaben ‘yan majalisar dokoki da na kwararru ta jagoranci da aka gudanar a watan da ya gabata a Iran din kuwa, Jagoran ya bayyana cewar: Ta hanyar wannan gagarumar fitowar da mutane suka yi yayin wannan zaben, a hakikanin gaskiya mutane sun bayyanar da goyon baya da kuma yardar da suke da ita ne ga tsarin Musulunci a aikace. Jagoran ya ce irin fitowar da al’ummar Iran suka yi da yakai kashi 62 cikin dari na wadanda suka cancanci kada kuri’arsu, ko shakka babu wani kaso ne mai girma idan aka kwatanta shi da na mafi yawa daga cikin kasashen duniya, hatta ma a kasashen da suke ikirarin kare demokradiyya.

Daga nan kuma sai jagoran yayi kiran da ‘yan majalisar (wato ta dokoki da ta kwararrun) zuwa ga kokarin sauke nauyin da ke wuyansu na yin hidima wa al’umma da kuma kare koyarwar juyin juya halin Musulunci wanda al’ummar suka fito da kuma ba da rayuwarsu don kare shi.

-------------------------------------/

Masu saurare barkanmu da sake saduwa.

Kamar yadda kuka ji a farkon shirin a ranar Asabar din da ta gabata ce shugaban kasar Iran Dakta Hasan Ruhani ya bude taron kasa na girmama ranar shahidai karo na uku da aka gudanar a nan Tehran inda yayin da yake jinjinawa irin sadaukarwar da shahidan juyin juya halin Musulunci da kuma na lokacin kallafaffen yaki bugu da kari kan hakuri da kuma tsayin dakan iyalan shahidan ya bayyana cewar: wajibi ne mu koyi darasi sadaukarwa daga wajen iyalan shahidai, dakarun da suka sami raunuka da sauran sojoji masu sadaukarwa.

Shugaba Ruhani ya bayyana shahidan a matsayin wani babban jari na zamantakewar al’ummar Iran yana mai cewa: juyin juya halin Musulunci na Iran ya zo ne don ya bayyanar da hasken musulunci da kuma tabbatar da kyawawan dabi’u da ‘yan’uwantaka a cikin al’umma.

Yayin da ya koma kan kokarin da ‘yan ta’addan kungiyoyi masu kafirta musulmi suke yi na kai hare-hare da keta hurumin hubbarori da wajaje masu tsarki na Imaman Ahlulbaiti (a.s) a kasashen Iraki da Siriya kuwa, shugaba Ruhani ya ce wadannan wajajen sun zamanto wasu jan layi da Iran ba za ta taba bari a keta huruminsu ba.

Shugaba Ruhani ya ce: Lamarin bas hi ne cewa wadannan wajajen suna Iraki ne ko Siriya ko wasu kasashen na daban ba, ba za mu taba bari ‘yan ta’adda su keta hurumin Hubbarorin Iyalan gidan Annabi (s.a.w.a) ba. Lalle za mu yake su.

Tun farko-farkon kokarin ‘yan ta’adda na kai hare-hare da kuma mamaye wajaje masu tsarki na Imaman Ahlulbaiti (a.s) a kasashen Iraki da Siriya, Jamhuriyar Musulunci ta Iran ta aike da kwararrunta a fagen ayyukan soji don taimakawa dakarun wadannan kasashe kare wadannan wajajen, kuma ya juya yanzu ya taimaka nesa ba kusa ba wajen hana ‘yan ta’addan cimma wannan bakar aniya ta su.

-----------------------------------/

Masu saurare barkanmu da sake saduwa.

A makon da ya wuce ne dakarun kare juyin juya halin Musulunci na Iran, a ci gaba da atisayen sojin da suke yi, suka gwada wasu sabbin makamai masu linzami masu cin dogon zango don tabbatar da irin karfin da suke da shi na mayar da martani bugu da kari kan irin shirin da suke da na kare kasar Iran daga duk wata barazana da za ta iya fuskanta.

Yayin da yake magana kan gwajin makaman da kuma ihu bayan harin da jami’an Amurka suka dinga yi kansa, kwamandan dakarun kare sararin samaniyya na kasar ta Iran Birgediya Janar Amir Ali Hajizadeh ya bayyana cewar karfafa irin karfin da Iran take da shi a fagen makamai masu linzami dai wani jan layi ne da Iran ba za ta taba amincewa ta dakatar da shi ba, yana mai cewa gwajin wadannan makamai koda wasa bai yi hannun riga da yarjejeniyar nukiliya da aka cimma tsakanin Iran da manyan kasashen duniya ba.

Janar Hajizadeh ya ci gaba da cewa: Amurka dai ta yi dukkanin kokarinta, ta hanyoyin barazana da leken asiri wajen hana wannan shiri na karfafa makamai masu linzami na Iran amma ta gaza.

Jami’an Amurka kama daga na fadar White House, ma’aikatar tsaro Pentagon da ma’aikatar cikin gida da sauransu sun ci gaba da surutu kan wannan gwajin makamai da Iran ta yi suna masu barazanar cewa za su kai maganar kwamitin tsaron MDD da nufin sake kakabawa Iran takunkumi, lamarin da jami’an Iran musamman na soji suka yi watsi da shi da cewa babu wani abin da zai hana Iran ci gaba da wannan shiri na ta na kare kanta daga wuce gona da irin makiya koda kuwa hakan zai kai a sake sanya mata takunkumi ne.

-----------------------------/

Masu saurare barkanmu da sake saduwa.

Kamar yadda kuka ji a farkon shirin, a makon da ya wuce ne aka gudanar da wani taron shugabannin kasashen kungiyar hadin kan kasashen musulmi a birnin Jakarta, babban birnin kasar Indonusiya bisa maudhu’in Palastinu da Masallacin Qudus mai tsarki.

A yayin wannan taron dai, ministan harkokin wajen kasar Iran, Dakta Muhammad Jawad Zarif ne ya wakilci shugaban kasar Iran a wajen taron inda a jawabin da ya gabatar ya bayyana cewar, wajibi ne matsalar Palastinu da masallacin Qudus a matsayinsu na babbar matsalar duniyar musulmi, a yi dukkanin abin da za a iya wajen aiwatar da alkawurran da aka dauka a aikace da nufin tabbatarwa kuma kare hakkokin al’ummar Palastinu.

A jawabin nasa, ministan harkokin wajen na Iran yayi kakkausar suka dangane da siyasa da kuma ayyukan kwamitin tsaron MDD, bisa wasu dalilai masu yawa, kwamitin tsaron ya gaza wajen sauke nauyin da ke wuyansa kamar yadda dokokin MDD suka tanadar, kamar yadda kuma ya bar haramtacciyar kasar Isra’ila tana ci gaba da gudanar da bakar siyasarta ta mamaya wanda take ci gaba da zama barazana ga sulhu da zaman lafiyan duniya.

Dakta Zarif ya ci gaba da cewa wajibi ne a ba da himma a aikace wajen kawo karshen mamayar da sahyoniyawa suke yi wa Palastinu a matsayin wani aiki da kuma hobbasa na gaba daya da nufin ‘yanto Palasatinawa daga mawuyacin halin da suke ciki da kuma kawo karshen kokarin da sahyoniyawa suke yi na sauya yanayi da kuma tsarin kasar Palastinu musamman birnin Qudus mai tsarki.

Bayan wannan taron dai, ministan harkokin wajen na Iran ya wuce zuwa kasashen Singapore, Brunei da kuma Thailand don ganawa da manyan jami’an kasar da nufin karfafa alakar da ke tsakanin bangarori biyu.

-------------------------------------/

END