Mar 25, 2016 06:39 UTC
  • Iran A Shekarar 1394 (1)

Masu saurare kamar yadda muka saba a duk lokacin da aka shigo sabuwar shekara ko dai ta miladiyya ko kuma ta hijira shamsiyya mu kan yi kokarin bitar wasu daga cikin batutuwan da suka fi daukar hankula dangane da Iran cikin shekarar da ta gabata din. Don haka bisa la’akari da shigowar sabuwar shekara ta hijira shamsiyya ta 1395 a nan Iran da ma wasu kasashen da suke amfani da wannan kalandar, don haka shirin na mu na yau zai yi dubi ne cikin daya daga cikin irin wadannan lamurran da suka fi dauk

Masu saurare assalamu alaikum barkanmu da warhaka da kuma sake saduwa cikin wani sabon shiri na Iran a Mako da ke leko muku wasu daga cikin muhimman abubuwan da suka faru a Iran cikin mako wanda ni Muhammad Awwal Bauchi na saba gabatar muku da shi da fatan masu saurare suna cikin koshin lafiya kuma za su kasance tare da mu tun daga farkon shirin har zuwa karshensa.

Masu saurare kamar yadda muka saba a duk lokacin da aka shigo sabuwar shekara ko dai ta miladiyya ko kuma ta hijira shamsiyya mu kan yi kokarin bitar wasu daga cikin batutuwan da suka fi daukar hankula dangane da Iran cikin shekarar da ta gabata din. Don haka bisa la’akari da shigowar sabuwar shekara ta hijira shamsiyya ta 1395 a nan Iran da ma wasu kasashen da suke amfani da wannan kalandar, don haka shirin na mu na yau zai yi dubi ne cikin daya daga cikin irin wadannan lamurran da suka fi daukar hankula a cikin shekarar wanda ko shakka babu shi ne batun yarjejeniyar nukiliya da aka cimma tsakanin Iran da manyan kasashen duniya.

Sai a biyo mu don jin yadda shirin zai kasance.

---------------------------/

Masu saurare barkanmu da sake saduwa.

Ko shakka babu diplomasiyyar Iran a shekarar da ta gabatan ta sake bayyanar da kanta wa duniya a matsayin wata diplomasiyya da take cike da hikima da kuma kwarewa wacce kuma za ta iya zama abin koyi ga sauran kasashe. Hakan kuwa ya biyo bayan nasarar da tawagar tattaunawar nukiliya ta Iran karkashin jagorancin ministan harkokin wajen kasar Dakta Muhammad Jawad Zarif ta samu, bayan tattaunawar mai wahala da sarkakakiya ta tsawon shekaru biyu da wani abu; inda suka sami nasarar kawo karshen shirin ‘yan mulkin mallaka masu son wuce gona da iri na ci gaba da matsin lamba na siyasa, tattalin arziki da kuma soji a kan Iran da nufin hana ta riko da tafarkin ci gaban da ta rika. Nasarar da Iran ta samu a fagen diplomasiyya da kuma mayar da barazanar makiya kan shirin nukiliyan Iran zuwa ga wata dama ta sake tabbatar da wannan hakki na nukiliya da take da shi, wata babbar nasara ce da siyasar Iran ta samu a gaban makircin makiya.

A shekarar da ta gabatan, an ware wani bangare mai muhimmanci na karfin diplomasiyyar Iran din wajen magance wannan matsala ta nukiliya da ma’abota girman kan duniya suka taso da ita. A fagen diplomasiyyar, Jamhuriyar Musulunci ta Iran ta samu nasarar yin tsayin daka wajen tinkarar takunkumin zalunci da makiya suka sanya mata da tilasta musu ja da baya da dage wani bangare na wadannan takunkumin. Wanda ko shakka babu hakan yana da alaka ne da irin tsayin daka da kuma gwagwarmayar al’ummar Iran din.

A yayin wannan tattaunawar dai, Jamhuriyar Musulunci ta Iran ta samu nasarar nuna wa duniya cewa ko da wasa ba ta da shirin mallakar makaman nukiliya, kamar yadda ma’abota girman kan suke yadawa, kamar yadda ta nuna musu cewa hanyar tattaunawa, itace kawai hanya guda da ta fi dacewa wajen magance matsalolin da suke kunno kai. Don haka ne ake ganin nasarar da Iran ta samu a yayin wannan tattaunawar a matsayin daya daga cikin batutuwa mafiya muhimmanci a bangaren siyasa a iran a shekarar da ta gabatan. Ita dai wannan tattaunawar ta ginu ne bisa yarjejeniyar da aka cimma tsakanin Iran da manyan kasashen duniya, wato Amurka, Rasha, China, Faransa, Ingila da kuma kasar Jamus a ranar 24 ga watan Nuwamban 2013, sannan kuma bayan tattaunawa ta kusan shekaru biyu, daga karshe dai a ranar 14 ga watan Janairun 2015 aka cimma yarjejeniya ta gaba daya a birnin Vienna, wacce ta tanadi takaita wasu bangarori na shirin nukiliyan na Iran a bangare guda kuma da cire mata dukkanin takunkumin da aka sanya mata wadanda suke da alaka da shirin nukiliyan nata na zaman lafiya.

Har ila yau diplomasiyyar Iran din ta tabbatar wa duniya Iran da al’ummarta ba za su taba mika kai ga tursasawa, mulkin mallaka da kuma neman wuce gona da irin ma’abota girman kai, sannan kuma za su tsaya kyam wajen kare hakkokinsu. Tun da fari dai ma’abota girman kan duniyan suna so ne su dakatar da shirin nukiliyan zaman lafiyan na Iran, sun yi iyakacin kokarinsu wajen ganin sun hana tace sinadarin uranium a cikin gidan Iran, su rufe cibiyoyin nukiliyan Iran da ke Arak da kuma na Fordo da kuma hana duk wani shiri na bincike da samun ci gaba a wannan fagen. To amma ko shakka babu sun sha kashi a wannan bangaren.

Ko shakka babu cimma yarjejeniyar nukiliyan, ya sanya tsare-tsare da makircin makiyan Jamhuriyar Musulunci ta Iran sun zamanto aikin baban giwa, saboda sun gaza cimma manufofin da suke da su a kan Iran din cikin kuwa har da batun barazana ta soji suna masu fakewa da dokokin MDD da suka sanya shirin nukiliyan na Iran a cikin fasali na bakwai na dokokin majalisar da ya ba da damar amfani da karfi a kan wata kasa. Don kuwa cimma yarjejeniyar ya fitar da Iran daga wannan fasalin. A takaice hakan ta tilasta musu amincewa da hakkin da al’ummar Iran suke da shi na mallakar fasahar nukiliya ta zaman lafiya cikin kuwa har da batun tace sinadarin uranium.

Masana al’amurran yau da kullum suna ganin cimma yarjejeniyar nukiliyan da kuma abubuwan da hakan ya haifar kuma zai haifar a nan gaba a matsayin wata nasara ta siyasa, da ke tabbatar da cewa shirin nukiliyan na Iran na zaman lafiya ne sabanin abin da makiya suka jima suna nunawa. A halin yanzu dai duniya ta amince da Iran a matsayin daya daga cikin kasashen da suka mallaki fasahar nukiliya, wacce kuma take da hakkin ci gaba da wannan shiri nata, wanda da man shi ne babban abin da Iran din ta jima tana son cimmawa da kuma tabbatar wa duniya shi. Hakan kuwa baya ga amfani da tattalin arziki da hakan ya haifar, kamar yadda za mu gani a nan gaba.

Shekara da shekaru kenan jami’an gwammnatin Amurka suke ta kai gwauro su kai mari wajen ganin sun matsa wa Iran lamba da kuma dunkufar da kasar ta hanyar zarge-zarge marasa tushe da suka hada cewa Iran tana kokarin mallaka makamin nukiliya, goyon bayan ayyukan ta’addanci da kuma take hakkokin bil’adama, wanda suna daga cikin abubuwan da suka fake da su wajen sanya wa Iran takunkumi kala kala tsawon shekaru talatin da wani abin da suka gabata. Duk da cewa ya zuwa yanzu dai an samu nasarar kwace daya daga cikin irin wadannan makamai da Amurkan take amfani da su don cimma bakar manufarta kan Iran, to amma duk da hakan dai jami’an Iran ba su sake jiki ba, don kuwa har ya zuwa yanzu dai suna ci gaba da tsaka tsantsan da kuma sanya ido kan ayyuka da dabi’un Amurkan.

Haka nan ne ma ya sanya Jagoran juyin juya halin Musulunci Ayatullah Sayyid Ali Khamenei, cikin amsar wasikun da shugaban kasar Iran din Dakta Hasan Ruhani ya aike masa tun sanar da shi cimma yarjejeniyar da kuma lokacin fara aiwatar da ita, yayi ishara da batun rashin amincewa da kuma yarda da sakin fuska irin ta AMurka, yana mai jan kunnen jami’an na Iran da su yi taka tsantsan don kuwa Amurka ba abar yarda ba ce; kamar yadda kuma ya kiraye su da su sanya ido wajen ganin Amurkawan sun cika dukkanin alkawurran da suka yi; yana mai cewa wajibi ne daga lokacin da aka ga Amurka da kawayen nata sun karya yarjejeniyar da aka cimma din to wajibi ne a gaggauta dakatar da aiki da yarjejeniyar don kuwa a cewarsa ba cikin ruwan sanyi aka cimma yarjejeniyar ba, ita ma Iran akwai abubuwan da ta rasa da kuma dakatar da su.

-----------------------------/

To daya daga cikin bangaren wannan yarjejeniyar shi ne cewa bayan Iran ta cika alkawurran da ta dauka na takaita wasu bangarori na shirin nukiliyan nata na zaman lafiya, a bangare guda kuma za a cire mata dukkanin takunkumin da aka sanya mata da suke da alaka da shirin nukiliyan nata na zaman lafiya, wato wadanda MDD ta sanya mata, da kuma na Amurka da Tarayyar Turai.

Ko shakka babu dage wadannan takunkumin ya bude wani sabon shafi na mu’amala ta tattalin arziki tsakanin Iran da sauran kasashen duniya wanda kuma ko shakka babu zai taimaka wajen rage wasu matsaloli na tattalin arziki da aka sanya kasar ciki. Wannan sabon tsarin kyautata tattalin arzikin yana cikin siyasar tattalin arzikin dogaro da kai da karfi na cikin gida da ake da shi ne wanda jagoran juyin juya halin Musulunci Ayatullah Khamenei ya sha jaddada wajibcin riko da shi don magance kara shiga matsalar tattalin arziki da kuma dogaro da wasu daga waje.

Cikin shekarar da ta gabatan dai, sakamakon cimma yarjejeniyar nukiliya da kuma dage wa Iran takunkumi, hakan ya bude kofar sake kulla alakoki na tattalin arziki da kasuwanci tsakanin Iran da wasu kasashen duniya da suka fito daga nahiyoyi daban-daban da suka hada da Turai, Asiya, Afirka da sauransu.

Daga cikin abubuwan da aka yi don kara karfafa alaka ta tattalin arziki tsakanin Iran da kasashen duniyar bayan dage takunkumin sun hada har da taron shugabannin kasashen duniya masu arzikin iskar gas da aka gudanar a birnin Tehran wanda ya sami halartar shugabanni da manyan jami’an kasashe daban-daban; wanda hakan ta zamanto wata dama ta tattaunawa tsakanin wadannan kasashe da Iran don karfafa alakar da ke tsakaninsu.

Har ila yau kuma a cikin shekarar da ta gabatan ne dai aka gudanar da taro na 26 na majalisar tsare-tsare na kungiyar ECO ta hadin gwiwan tattalin arziki da aka gudanar a Tehran, taron da ya sami halartar wakilai daga kasashe daban-daban na duniya; musamman kasashen Asiya bisa la’akari da cewa kasashe 10 daga cikin membobin kungiyar sun fito ne daga wannan nahiyar wadanda kuma suke da mutanen da suka kai miliyan 440, hakan lamari ne da zai tasirin gaske a bangaren karfafa tattalin arziki bisa la’akari da irin kusaci na al’adu da kuma tarayyar da aka yi cikin manufofi tsakanin iran da wadannan kasashen.

Har ila yau a bangare guda kuma a shekarar da ta gabata duniya ta shaidi faruwar farashin man fetur a kasuwar duniya, faduwar farashin da aka jima ba a ga irinsa ba. Saboda man fetur din da ake sayar da kowace gangan sama da dala 100 sai ga shi ya dawo kasa da dala talatin wanda ko shakka babu hakan yayi mummunan tasiri cikin tattalin arzikin kasashe masu arzikin man fetur wadanda kuma suka dogara da man fetur din a bangaren karfafa tattalin arzikinsu cikin su kuwa da Iran din wacce ta kasha 60 da wani abu na tattalin arzikinta ya dogara da man fetur din. A saboda haka ko shakka babu dage wannan takunkumin ya taimaka kuma zai taimaka wajen rage irin wannan matsala ta faruwar farashin man da kuma tasirinsa cikin tattalin arzikin kasar da ma sauran kasashen da suka dogara da mai din.

=------------------------------/

To ko ma dai mene ne abin da babu shakku cikinsa shi ne cewa cimma wannan yarjejeniya ta nukiliya da aka yi a shekarar da ta gabatan, ya sanya wani bangare mai yawa na kokarin makiya Iran wadanda suke kokari wajen bakanta juyin juya halin Musulunci na kasar da kuma dunkufar da Jamhuriyar Musulunci ta Iran din ya sha kashi da kuma zama aikin baban giwa. Don kuwa a dukkanin bangarori na ilimi da fasahar nukiliya, iran ta sami nasarar isa ga wani mataki mai girman gaske da kuma samar da abubuwan da take bukata na gudanar da binciken nukiliya da kuma samar da abubuwan da take bukata a bangaren samar da maganin cututtuka masu tsananin wahalar magani ta hanyar samar da makamashin da cibiyoyinta na nukiliya suke bukata.

A hakikanin gaskiya ana iya cewa duk da irin kafar ungulun da Amurka da kawayenta na larabawa da haramtacciyar kasar Isra’ilasukayi a baya wajen mayar da iran saniyar ware da kuma hana ta ci gaba a fagen ilimi da fasahar nukiliya, to amma a halin yanzu bayan cimma wannan yarjejeniyar iran ta sami nasarar bude wa kanta wasu sabbin kofofi na ciyar da kanta gaba musamman a bangaren tattalin arziki, lamarin da makiyan ba sa fatan gani. Ko shakka babu Iran za ta shiga sabuwar shekarar ta 1395 ne a daidai lokacin da kasashen duniya ciki kuwa har da manyan cikinsu suke ci gaba da tururuwa zuwa gare da neman kulla alaka ta kasuwanci da tattalin arziki da ita.

Masu saurare saboda karancin lokaci a nan za mu yi ban kwana da ku, amma da yardar Allah a shirinmu nag aba za mu yi muku dubi ne cikin alakar Iran da kasashen nahiyarmu ta Afirka cikin shekarar da ta gabata ta 1394 din.

------------------------------------/

END


Tags