Mar 31, 2016 18:17 UTC
  • 12 Ga Farvardin Ranar Jamhuriyar Musulunci a Iran

Ranar 12 ga watan Farvardin, daya ne daga cikin ranaku masu tarihi da kuma muhimmanci cikin kalanda da tarihin Iran musamman cikin shekarun baya-bayan nan. Saboda kuwa a wannan ranar ce a shekarar 1357 hijira shamsiyya (1979), aka tabbatar da sakamakon shekara da shekaru na gwagwarmaya da fada da mulkin kama-karya ta gidan sarautar Pahlawi da kuma neman ‘yancin kan al’ummar Iran da kuma tabbatar da Jamhuriyar Musulunci a kasar ta Iran. A wannan ranar ce dai al’ummar Iran

Ranar 12 ga watan Farvardin, daya ne daga cikin ranaku masu tarihi da kuma muhimmanci cikin kalanda da tarihin Iran musamman cikin shekarun baya-bayan nan. Saboda kuwa a wannan ranar ce a shekarar 1357 hijira shamsiyya (1979), aka tabbatar da sakamakon shekara da shekaru na gwagwarmaya da fada da mulkin kama-karya ta gidan sarautar Pahlawi da kuma neman ‘yancin kan al’ummar Iran da kuma tabbatar da Jamhuriyar Musulunci a kasar ta Iran. A wannan ranar ce dai al’ummar Iran, ta hanyar ba da kashi 98.2 cikin dari na kuri’ar da suka kada a yayin kuri’ar jin ra’ayin al’umma da aka yi ga Jamhuriyar Musulunci, wanda hakan ya sauya tsari da tushen siyasa, zamantakewa da kuma al’adu a kasar sannan kuma ya kafa tsari na addini da kuma na mutane a kasar. A saboda haka ne tun daga wancan lokacin har zuwa yau a ke kiran wannan rana da sunan “Ranar Jamhuriyar Musulunci” a kasar ta Iran.

Bayan shekaru aru-aru na aiwatar da tsarin raba addini da siyasa da kuma tsare-tsaren gwamnatin da babu ruwanta da addini a duniya musamman a kasashen yammaci da kuma bayyanar da dokoki da shari’a ta Ubangiji a matsayin wasu lamurra da suka shafi rayuwar daidaiku na al’umma, to amma a shekarar 1979 a kasar Iran, an samar da wani tsari wanda ya tabbatar da rashin ingancin wadancan mahangar da kuma tabbatar da wata hukuma ta demokradiyya da ta ginu bisa koyarwa ta addini. Jamhuriyar Musulunci dai wani sabon tsari na gwamnati ne da ya ginu bisa koyarwar addinin Musulunci wanda yake kokari wajen gabatar da sabuwar rayuwa a fagen zamantakewa da siyasa ta bil’adama da kuma biya musu bukatunsu, ba wai kawai na duniya ba har ma da abin da zai samar musu da kyakkyawar rayuwa a gobe kiyama. A saboda haka ne ma Jagoran juyin juya halin Musulunci Ayatullah Sayyid Ali Khamenei yake cewa: “Jamhuriyar Musulunci tana da bangarori biyu: Na farko, Jamhuriya, wato ta jama’a ce, sannan kuma na biyu na Musulunci, wato wacce ta ginu bisa koyarwa ta Ubangiji da kuma shari’arsa”.

A Iran, bayan kifar da gwamnatin kama karya ta Shah a kasar, an gabatar da wasu shawarwari na irin tsarin gwamnatin da ake son kafawa. Daga cikinsu har da “Jamhuriyar Demokradiyya” da “Jamhuriya” da sauransu, to amma marigayi Imam Khumaini (r.a), wanda ya assasa Jamhuriyar Musulunci ta Iran, tun ranar farko ya sha jaddada muhimmancin kafa tsarin gwamnati irin na Jamhuriyar Musulunci, ta yadda ya sha nanata cewa bai kamata a kara ko a rage koda kalma guda daga cikin wannan jumla ta “Jamhuriyar Musulunci” ba. Marigayi Imam Khumaini dai yayi amanna da cewa addinin Musulunci yana da dukkanin abin da ake bukata wajen gudanar da rayuwar bil’adama da suka hada da tabbatar musu da ‘yanci da daidaito da dai sauransu. A saboda haka ne ya ki amincewa da shawarar da wasu suka kawo na kafa “Jamhuriyar Demokradiyya ta Musulunci”, wanda a mahangarsa amincewa da hakan yana nuni da cewa Musulunci ya rasa tushen demokradiyya kenan, alhali kuwa tsarin demokradiyya da girmama ra’ayin mutane yana cikin wannan addinin ne. Marigayi Imam Khumaini (r.a) yayi bayanin wannan batu cikin wata hira da yayi da manema labarai inda ya ce: wannan batu na “Jamhuriyar Demokradiyya ta Musulunci” cin mutumci ne ga Musulunci; tamkar ne a ce: Jamhuriyar Musulunci ta adalci, wannan cin mutumcin Musulunci ne don kuwa adalci wani bangare da tushe ne na Musulunci, ba wai ya aro shi daga wani waje ba ne. A saboda haka ne ma al’ummar Iran suka rungumi wannan tunani na marigayi Imam Khumaini (r.a) da kuma tabbatar da shi a dukkanin tarururruka da zanga-zangogi da suke yi inda suke rera shahararren taken nan na su na “ ‘yanci kai, ‘yanci (na zamantakewa), Jamhuriyar Musulunci (muke so)”. A saboda haka a fili ana iya cewa jamhuriya da kuma Musulunci, wasu tushe ne guda biyu wadanda a tsarin Musulunci ba za a taba raba su ba. A saboda haka ne aka kafa gwamnati ta demokradiyya ta addini a Iran a ranar 1 ga watan Aprilun 1979, wanda ake ganinta a matsayin gwamnati irin ta ta farko tun farko-farkon Musulunci shekaru dubu da wani abu da suka gabata.

Yayin bayanin ma’anar ‘tsarin demokradiyya na addini’ ana iya cewa: “Demokradiyya ta addini’ tana nufin wata hukuma ce wacce ta ginu bisa shari’a ta Ubangiji sannan kuma ta samu karbuwa daga wajen mutane, sannan shugaban wannan hukumar yana gudanar da ayyukansa ne karkashin inuwar “riko da dokokin Ubangiji, tabbatar da hakki, yin hidima wa mutane da kuma samar da fagen ci gaba da daukaka ta duniya da lahira ga al'umma.” Don haka ne tushen demokradiyya na addini ya dara tushen demokradiyya na kasashen yammaci. Bambancin kuwa yana cikin tushen ‘yancin dan’adam ne cikin rayuwarsa da ke da alaka da duniyarsa da kuma lahirarsa da kuma alakar hakan da rayuwarsa ta daidaiku da kuma ta zamantakewa ta al’umma. Marigayi Allamah Tabataba'i, sanannen mai tafsirin Alkur’ani mai girma din nan sannan kuma masanin falsafa na duniyar Shi’a yana fadin cewa: Wasu suna tunanin kasashen yammaci ne suka kawo wa bil’adama ‘yanci, demokradiyya da hakkokin bil’adama, alhali kuwa Musulunci tun sama da shekaru 1400 da suka gabata yayi bayanin wadannan abubuwa a mafi kyawun yanayi da kuma gabatar da su ga bil’adama. To amma kasashen yammaci ta hanyoyin kafafen watsa labaransu suna kokarin nunawa duniya cewa su ne suka kawo wa bil’adama wadannan abubuwan”.

Marigayi Imam Khumaini (r.a) yayi amanna da cewa makiyan Musulunci su ne ummul aba’isin din hana al’ummomin duniya fahimtar hakikanin hukunce-hukuncen Musulunci. Imam ya bayyana cewar: A lokacin da aka aiwatar da Musulunci yadda yake ne, mutane za su fahimci cewa demokradiyyar boge ta kasashen yammaci ba komai ba ce idan aka kwatanta ta da ta Musulunci.

Marigayi Imam Khumaini ya ci gaba da cewa: Mai yiyuwa ne a samu wasu bangarori na kama da juna na zahiri tsakanin demokradiyyar da muke son kafawa da kuma demokradiyyar kasashen yammaci, to amma mu dai demokradiyyar da muke son kafawa, babu irinta a yammaci. Demokradiyyar Musulunci ta fi zama kammalalliya a kan demokradiyyar yammaci.

A saboda haka ne da dama suke ganin akwai bukatar fahimtar demokradiyya ta addini idan aka kwatanta da demokradiyya ta kasashen yammaci. A wannan bangaren ana iya dubi cikin wasu bangarori da tushe masu muhimmanci na tsarin demokradiyya na addini karkashin batutuwa irin su adalci, shari’a ta Ubangiji, amincewa da yarda ta mutane, hidima ga al’umma da kuma ‘yanci.

Dangane da wannan batu marigayi Imam Khumaini (r.a) yana fadin cewa: “Harshen damo da karo da juna cikin magana da aiki’ wani bangare kana kuma wata siffa ce mai muhimmanci ta tsarin demokradiyyar kasashen yammaci. Don kuwa kasashen yammacin a bangare guda suna daga taken kare hakkokin bil’adama, adalci da ‘yanci’, to amma a aikace su ne a kan gaba wajen yin karen tsaye wa wadannan abubuwa da kuma take su. Imam ya ci gaba da cewa: Wadannan mutane, da a matsayin misali suke rera taken kare hakkokin bil’adama, to amma su ne wadanda suka fi take hakkokin bil’adaman”. Irin wadannan misalan dai suna da yawan gaske cikin ayyuka gwamnatocin kasashen yammaci, ta yadda wannan harshen damo ya zamanto wata siffa da take bin gwamnatocin kasashen yammacin. Daya daga cikin misalan hakan shi ne irin mulkin mallakar da suka yi wa kasashen Afirka, Asiya da Latin Amurka lamarin da ya sanya al’ummomin wadannan kasashen cikin mawuyacin hali da kuma koma bayan da har ya zuwa yanzu suke fuskanta ba tare da komai kashi nuna damuwa da kuma neman afuwar wadannan al’ummomi ba.

Ga misali gwamnatin Faransa, wacce a yayin yunkurin neman ‘yancin kan al’umma kasar Aljeriya daga mulkin mallakar shekaru 130 na Faransawa, gwamnatin Faransan ta kashe sama da mutanen Aljeriya miliyan guda, to amma har ya zuwa yanzu gwamnatin Faransan ta ki neman afuwar al’ummar Aljeriyan, face ma dai ta yi kokarin sanya hakan cikin dokokin kasar inda aka bayyana wannan danyen aikin a matsayin wani lokaci abin alfahari ga al’ummar Faransa da kuma tarihin kasar.

Irin wadannan misalan dai suna daga yawa cikin tarihin kasashen Turai da Amurka dake nuni da karo da juna da ke cikin magana da kuma aikinsu.

Har ila yau kuma daya daga cikin nauyin da ke wuyan shugaba a tsarin demokradiyya na addini shi ne riko da kuma aiwatar da koyarwa da kuma hukunce-hukuncen addinin Musulunci. A saboda haka ne ma yayin da yake magana dangane da irin nau’in alakar da ke tsakanin mutane da kuma jami’an gwamnati a Jamhuriyar Musulunci, Ayatullah Sayyid Ali Khamenei, jagoran juyin juya halin Musulunci ya ke cewa: “Daya daga cikin siffofin da tsarin demokradiyya na addini ya kebanta da su, shi ne cewa alakar da ke tsakanin jami’an gwamnati da mutane ba kawai ta takaita alaka ta bin doka ba ne, face dai baya ga hakan akwai kuma alaka ta girmamawa da kuma ‘yan’uwataka da imani, wanda hakan ya samo asali ne daga imani da akidar mutane, mahanga da kuma koyarwa ta addini da kuma riko da koyarwa da kuma tushe na juyin juya hali”.

A saboda haka, a irin wannan tsarin dukkanin komai za su kasance ne karkashin koyarwar addinin Musulunci, wanda hakan yana magance irin matsala ta kyawawan halaye da bayyanar muggan dabi’u wadanda suka yi katutu da daurin has ga kasashen yammacin. Wannan kuwa yana daga cikin mafiya muhimmancin bambance bambancen da ke tsakanin tsarin demokradiyya na Musulunci da irin na kasashen yamnmaci wanda yake ganin komai bisa tushe na jin dadin dan’adam da sha’awace sha’awace na son zuciyarsa alhali kuwa shi Musulunci yana ba da muhimmanci ne ga abubuwan da za su kyautata rayuwar dan’adam a nan duniyar da kuma gobe kiyama.

A takaice dai ana iya takaita dukkanin wannan bahasi na mu na tsarin demokradiyya na Musulunci da aka kafa shi a Iran a irin wannan rana (1 ga watan Aprilu 1979), cikin wannan magana ta Jagoran juyin juya halin Musulunci Ayatullah Khamenei inda yake cewa: “Tsarin Jamhuriyar Musulunci, shi ne dai wannan demokradiyya wacce take watsi da demokradiyyar da ta ginu bisa tushe na kuskure na kasashen yammaci. Demokradiyya ta addini ita ce demokradiyyar da take tabbatar da karama ta hakika ta dan’adam da kuma sanya rayuwar mutane karkashin koyarwa ta addinin Allah, ba karkashin tafarki na jahiliyya wacce ta ginu bisa bukatu na kamfanoni tattalin arziki da na makamai da kuma abubuwan da suke bukata ba. A tsarin Jamhuriyar Musulunci dai, rayuwar mutane tana tafiya ne karkashin koyarwar addinin Allah da kuma bukatu na mutane”.


Tags