Apr 25, 2016 13:09 UTC

Jama'a masu saurare Assalamu Alaikum barkanku da warhaka barkanmu kuma da sake saduwa da ku a cikin wannan shiri an Afirka a mako, inda mukan duba wasu daga cikin muhimman lamurra da suka waka a wasu daga cikin kasashen nahiyar Afirka a mako, a yau ma shirin da yardar zai leka tarayyar Najeriya, J. Nijar, masar, da sauransu, gwargadon yadda lokaci y aba mu hali, da fatan za a kasance tare da mu.

To bari mu fara da batun Najeriya, ainda a cikin wannan makon ne aka cika shekaru 2 da sace yan matan sakandaren Chibok da yan Boko Haram suka sace, inda kuma har yanzu ake ci gaba da nuna damuwa dangane da makomarsu da ma sauran wadanda yan ta'addan na Boko haram suka sace a wasu wuraren. A kan wannan lamari an gudanar da jerin gwano a birnin Abuja fadar mulkin Najeriya, dan rahotonmu a Abuja Muhammad Sani Abubakar ya halarci wurin, ga abin da ya shirya.
…………………
To a nasu bangaren majalisun dattijai da na wakilai a Najeriya sun gudanar da zama kan wannan batu, Sanata Gobir dan majalisar dattijai ne, ya yi wa sashen Hausa Karin bayani kan zaman nasu:
…………………..
To shi ma a nasa bangaren Honorable Garba Chede, ya yi was ashen Hausa Karin bayani kan nasu zaman a majalisar wakilai kan abubuwan da suka yi dubi a kansu da kuma matakan da za a dauka.
…………………………..
To za mu sake komawa Najeriya daga bisani, yanzu bari mu nufi jamhuriyar Nijar, inda yanzu haka dai yan majalisa daga bangaren jam'iyyun adawa sun yanke shawarar komawa zaman majalisar, domin ci gaba da aikinsu, bayan da suka kaurace ma majalisar tun kwanakin baya, saboda abin da suka kira rashin halascin zaben da aka yi.
Alh. Tijjani Abdulkadir dan majalisar dokokin jamhuriyar Nijar ne daga bangaren adawa, ya yi was ashen Hausa Karin bayani kan dalilansu na daukar wannan mataki.
 ………………………….
A cana kasar Masar kuwa ziyarar da sarkin masarautar Saudiyya ya kai kasar ce ta bar baya da kura, inda al'ummar kasar suke gudanar da zanga-zangar nuna kin amincewa da matakin da gwamnatin kasar ta dauka na mika wasu tsibirran kasar da ke cikin kogin Maliya ga Saudiyya, sakamakon wata yarjejeniya da aka cimmawa tsakanin mahukuntan kasashen biyu kan hakan, wadda al'ummar kasa ba su da masaniya  a kanta.
Dr. El-harun Muhammad masani ne kan harkokin siyaar kasa da kasa daga Najeriya, ya yi was ashen Hausa Karin bayani kan mahangarsa dangane da abubuwan da syka biyo bayan ziyarar sarkin na Saudiyya a Masar.
…………………………..
To bari mu sake komawa Najeriya kamar yadda muka yi alkawali. Yanzu haka batun matsalar karancin wutar lantarki a kasar ya zama daya daga cikin abubuwan da suka fi cima al'ummar kasar tuwo a kwarya, inda wasu bayanai na baya-bayan nan da mahukuntan kasar suka bayar sun ce za a ci gaba da fuskantar wannan matsala daga nan har zuwa karshen watan Mayu mai kamawa, tare da danganta hakan da matsalolin fasa bututun iskar gasar da danyen mai a yankunan kudancin kasar.
Injiniya Murtala Muqaddas masani kan harkokin makamashi da wutar lantarki, ya yi wa shashen Hausa Karin bayani kan yadda yake kallon lamarin.
……………………….

A can kasar Chadi kuwa har yanzu ana jiran a sanar da sakamakon zaben shugaban kasar da aka yi a kasar, wanda ake zaton cewa shugaban kasar Idris Deby ne ya lashes hi.
Sai dai wasu daga cikin al'ummomin kasar na kokawa kan yadda zaben ya gudana, inda ak ayi amfani da karfi kan masu adawa da shugaba Deby, inda yanzu haka ma aka nemi wasu aka rasa, bayan da iyalansu suka tabbatar da cewa sun je fa ma dan takarar adawa kuri'a ne ba Idris Deby ba, haka nan kuma wasu bayanan na cewa jami'an tsaro fiye da 40 sun yi batan dabo, wanda shi ma wasu ke danganta hakan da batutuwa na siyasa.

…………………………………
A kasar Kenya kuwa, shugtaban kasar Uhuru Kenyatta tare da mataimakinsa William Roto ne suka yi kira zuwa ga sulhu da yafiya a tsakanin al'ummar kasa baki daya.
A lokacin da yake halartar wani gangami na dubban magoya bayansa a wani makeken filin wasa da ke garin Nagoru a kasar ta Kenya, shugaba Kenyatta tare da mataimakinsa sun yi kira da babbar murya kan a manta da duk wani abu da zai iya kawo rarraba da rashin fahimtar juna a tsakanin a'ummar kasar.
Haka nan kuma a lokacin da yake magana kan batun rikicin da ya faru a kasar a cikin shekarun 2007 da 2008, Kenyatta ya bayyana takaicinsa matuka kan abubuwan da suka faru, inda ya ce abin bakin ciki ne, kuma yana fata wani abu mai kama da haka ba zai sake faruwa a kasar ta Kenya ba, tare da yin kira da a hada kai tare da yin sulhu a tsakanin dukkanin bangarori na al'ummar kasar domin ci gabanta da zaman lafiyarta.
………………………
To jama'a masu saurare gain cewa lokacin da muke da shi ya fara kawo jiki, dole a nan za mu dakata, sai Allah ya hada mu a mako na gaba, za a ji mu dauke da wani jigon, kafin lokacin a madadin wadanda suka hada sautin shirin a faifai har ya kammala, na ke yi muku fatan alhairi, wassalamu Alaikum.


Tags