Kamaru: An Kashe Mutane Biyu A Harin Ta'addanci
Dec 25, 2016 19:05 UTC
Mutane Biyu Sun Mutu A wani harin ta'addanci da aka kai a yau lahadi a kasar Kamaru.
Majiyar gwamnatin kasar ta kamaru ta ce ayau lahadi ne aka kai hari a wata kasuwar Kirsimeti da ke garin Mora a rewacin kasar da ya yi sanadin mutuwar wata mace guda da kuma wani dalibi.
Wannan dai ba shi ne karon farko ba da aka kai hari a garin na Mora. A baya kungiyar boko haram ta kai harin ta'addanci a cikinsa wanda ya haddasa asara mai yawa.
Majalisar Dinkin Duniya ta bayyana Kasar Kamaru a matsayin ta biyu bayan Najeriya da su ke fuskantar munanan hare-haren kungiyar Boko Haram.
Tags