Oct 16, 2017 08:40 UTC
  • Majalisar Dinkin Duniya Zata Gabatar Da Tallafi Ga Kasar Chadi Domin Yaki Da Cututtuka

Asusun da ke tallafawa a fagen yaki da bullar cututtuka a duniya na Majalisar Dinkin Duniya zai gabatar da tallafin kudade ga gwamnatin Chadi domin samun damar yaki da cututtukan kanjamau ko kuma sida, tarin fuka da zazzabin cizon soro a kasar.

Asusun da ke tallafawa a fagen yaki da bullar cututtuka a duniya na Majalisar Dinkin Duniya ya bayyana cewa: Gwamnatin Chadi da samu gagarumin ci gaba a fagen yaki da cututtukan kanjamau ko kuma sida, tarin fuka da kuma zazzabin cizon soro a cikin 'yan shekarun baya-bayan nan, sakamakon haka Asusun na Majalisar Dinkin Duniya zai tallafawa gwamnatin kasar ta Chadi da kudi euro miliyan saba'in da hudu domin ganin an kawo karshen cututtukan uku a kasar ta Chadi.

Ma'aikatar lafiya ta kasar Chadi a shekara ta 2015 ta sanar da cewa: Yawan mutanen da suka kamu da kwayar cutar kanjamau ko kuma sina a kasar sun kai kashi 3.3 cikin dari na al'ummar kasar amma yanzu an samu damar dakile ci gaba da yaduwar cutar cikin hanzari, kamar yadda yawan masu dauke da cutar tarin fuka daga shekara ta 2007 zuwa 2014 suka karu daga 6,200 zuwa 11,325. Haka nan yawan masu dauke da cutar cizon soro sun haura zuwa kashi 35 cikin dari, kuma cutar tana ta fi lashe rayukan kananan yara.  

Tags