Oct 16, 2017 11:21 UTC
  •  Majalisar Dinkin Duniya Ta Bai Wa Kasar Chadi Tallafi Kudi Domin Fada Da Cutuka

Asusun da ke fada da cutukan Kanjamau da tarin fuka da zazzabin cizon sauro da ke karkashin Majalisar Dinkin Duniya ya ce ya bai wa Cahdin kudin da suka kai Euro miliyan 74

Bayanin asusun ya ce a cikin shekarun bayan nan kasar ta Chadi ta sami ci gaba sosai a fada da wadannan cutukan guda uku, tare da yin kira a gare ta da ci gaba da kokarin da take yi.

Kididdigar ma'aikatar kiwon lafiya ta kasar Chadi ta nuna cewa; A  shekarar 2015 kaso uku da digo uku na al'ummar kasar sun kamu da cutar da Aids.

Bugu da kari kididdigar ta kuma ambaci cewa; Zazzabin cutar cizon sauro ne yake sanadin mutuwar mutane fiye da kaso 35% na al'ummar kasar.

Har ila yau, a tsakanin 2007 zuwa 2014 fiye da mutane dubu  shida da dari biyu ne suka kamu da cutar tarin fuka, wanda ya karu zuwa dubu goma sha biyu da dari uku da ashirin da biyar. Sai dai yadda  an sami nasarar yin maganar cutar daga kaso 22 % zuwa kaso 72 %.

Tags