Nijar : Isufu Ya Karbi Shugabancin karba-karba na G5 Sahel
(last modified Wed, 07 Feb 2018 05:20:10 GMT )
Feb 07, 2018 05:20 UTC
  • Nijar : Isufu Ya Karbi Shugabancin karba-karba na G5 Sahel

Shugaba Isufu Mahamadu, na Jamhuriyar Nijar ya karbi shugabancin karba-karba na kungiyar G5 ta kasashen yankin Sahel, a taron shuwagannin kungiyar karo na hudu da ya gudana jiya Talata a birnin Yamai fadar gwamnatin Nijar.

Shugaba Ibrahim Bubakar Keita na Mali ne ya jagoranci kungiyar kafin ya mika ragamar shugabancinta ga takwaransa na Nijar.

A taron da suka gudanar Jiya, shuwagabannin sun bayyana cewa har yanzu da sauran gibi a kudaden da suke bukata wajen kaddamar da rundunar hadin gwiwa kasashen.

Shugaba Ibrahim Bubakar Keita na Mali ya fada a jawabinsa a wurin taron cewa, kawo yanzu Dala Milyan 294 kawai aka samu cikin 450 da ake bukata.

Nan gaba ne dai a ranar 23 ga watan Fabrairun nan ake sa ran kasashen biyar da suka hada da (Mali, Nijar, Chadi, Burkina Faso da Mauritania) zasu gudanar da wani taron neman tallafi a birnin Brussels.