'Yan Tawayen Kasar Uganda Sun Kai Hari Gabashin D/Congo
Akalla Mutum 6 ne suka rasa rayukansu sanadiyar wani hari da 'yan tawayen Uganda suka kai jihar Kivo ta Arewa dake gabashin Jamhoriyar Demokaradiyar Congo.
Gidan Radion Oukafai na kasar Congo ya nakalto mazauna yankin Beni na jahar Kivo na cewa kimanin fararen hula 6 ne suka rasa rayukansu sakaniyar wani gumurzu tsakanin 'yan tawayen kungiyar Allied Democratic Force (ADF) ta kasar Uganda da jami'an tsaron jamhoriyar Demokaradiyar Congo a kauyen MayiMoya dake yankin na Beni.
Sanarwa ta ce 'yan tawayen na Uganda sun kwashi dukiya mai yawa ta al'ummar garin na MayiMoya.
Har ila yau mazauna yankin na Beni sun bayyana takaicinsu kan yadda gamayar rundunar tsaron kasar da na dakarun wanzar da zaman lafiya na MDD ke gudanar da ayyukansu a yankin, tare da neman a gudanar da gyara da rundunar hadin gwuwar.
Tun daga shekarar 1994 ne 'yan tawayen na Uganda suke kai hare-hare a gabashin Demokaradiyar Congo, lamarin da ya salwanta rayukan fararen hula da dama na yankin Beni na gabashin kasar ta Congo