Aug 24, 2018 06:24 UTC
  • Wasu 'Yan Bindiga Sun Kashe Sojojin Gwamnatin Libiya A Yankin Arewacin Kasar

Wasu gungun 'yan bindiga sun kai farmaki kan wajen binciken ababan hawa a garin Zliten da ke gabashin birnin Tripoli fadar mulkin kasar Libiya, inda suka kashe sojojin gwamnatin kasar hudu.

Magajin garin Zliten Moftah Ahmadi ya sanar da manema labarai cewa: Wasu gungun 'yan bindiga da ake kyautata zaton 'yan kungiyar ta'addanci ta Da'ish ne sun kaddamar da harin wuce gona da iri kan tawagar sojojin gwamnatin hadin kan kasa a Libiya da take gudanar da binciken ababan hawa a kan hanyar da ke tsakanin birnin Tripoli da garin Zliten a jiya Alhamis, inda suka kashe sojoji hudu tare da jikkata wasu biyar na daban.

Kafin gungun 'yan bindigan mai kunshe da mutane uku su tsere daga wajen da suka kai harin, sojojin gwamnatin Libiya sun samu nasarar halaka daya daga cikin maharan. 

Tags