Dec 30, 2018 07:00 UTC
  • New York Times: Sojojin Haya Dubu 14 Ne Daga Sudan Suke Yaki A Yemen

Jaridar New York Times ta kasar Amurka ta buga wani rahoton da ke cewa, sojojin gwamnatin Sudan su dubu 14 ne suke yaki a kasar Yemen a matsayin sojin hayar Saudiyya.

A cikin rahoton nata, jaridar New York Times ta bayyana cewa, a cikin sojoji dubu 14 da gwamnatin Sudan ta tura zuwa kasar Yemen a matsayin sojojin hayar Saudiyya da suke yi mata yaki kan al'ummar kasar Yemen, ya zuwa an kashe daruruwa daga daga cikinsu, an kuma kame wasu daruruwan a kasar ta Yemen.

Rahoton ya kara da cewa, akasarin sojojin da gwamnatin Sudan take bayar da su da su haya ga Saudiyya domin kai hare-hare a Yemen 'yan kabilar Janjawid ne da suke yankin Darfur, wadanda gwamnatin Sudan ta yi amfani da su wajen kisan kabilun bakaken fata ''yan Afrika wadanda ba larabawa da suke yankin Darfur a 'yan shekarun da suka gabata, wanda akan haka ne kotun duniya ta bayar da sammacin kame shugaban kasar ta Sudan Umar Hassan Albashir.

Haka nan kuma jaridar ta New York Times ta ce, bisa binciken da ta gudanar, da dama daga cikin iyalan wadanda ake tura 'ya'yansu zuwa yakin kasar ta Yemen daga Sudan basa goyon bayan hakan, amma ana tilasta su ko kuma ta hanyar ba su cin hanci da rashawa.

Tags