Sojojin Nijar Sun Hallaka Wasu 'Yan Boko Haram A Kasar
Rundunar sojin Jamhuriyar Nijar ta sanar da cewa sojojin kasar sun sami nasarar hallaka wani adadi na 'yan kungiyar Boko Haram a wani ba ta kashi da ya gudana tsakanin bangarorin biyu.
Kamfanin dillancin labaran Associated Press ya nakalto Kanar Moustapha Michel Ledru, daya daga cikin kwamandojin sojojin na Nijar yana cewa sojojin sun sami nasarar hallaka alal akalla 'yan Boko Haram 10 a lokacin da suka yi kokarin kai hari wani sansani na sojojin da ke yankin Diffa da ke Kudu maso gabashin kasar daidai da kan iyakar kasar da Nijeriya.
Kanar Ledru ya kara da cewa a yayin gumurzun, wasu sojoji guda uku sun sami raunuka, yana mai cewa 'yan Boko Haram din sun ranta cikin na kare ne bayan da sojojin suka bude musu wuta. Har ila yau ya ce sun sami nasarar kwace makamai da albarusai daga wajen 'yan Boko Haram din.
Yankin na Diffa dai yana ci gaba da fuskantar hare-haren 'yan kungiyar ta Boko Haram wadanda suka samo asali daga Nijeriya. Rikicin na Boko Haram dai yayi sanadiyyar mutuwar dubban mutane da kuma tarwatsa wasu miliyoyi a kasashen Nijeriya, Nijar, Kamaru Da Chadi.