Shugabar Majalisar Dokokin Afirka Ta Kudu Ta Kai Ziyara Kasar Iran
https://parstoday.ir/ha/news/iran-i23705-shugabar_majalisar_dokokin_afirka_ta_kudu_ta_kai_ziyara_kasar_iran
Madam Baleka Mbete ta iso birnin Tehran a yau Juma'a inda ta sami tarbar shugaban kwamitin Majalisa na alakar Iran da Afirka ta kudun malama Barvaneh Salahshur.
(last modified 2019-08-10T14:54:46+00:00 )
Sep 01, 2017 19:21 UTC
  • Shugabar Majalisar Dokokin Afirka Ta Kudu Ta Kai Ziyara Kasar Iran

Madam Baleka Mbete ta iso birnin Tehran a yau Juma'a inda ta sami tarbar shugaban kwamitin Majalisa na alakar Iran da Afirka ta kudun malama Barvaneh Salahshur.

A gobe Asabar madam Baleka Mbete za ta gana da  shugaban Majalisar shawarar musulunci ta Iran Dr. Ali  Larijani domin tattauna alakar da ke tsakanin kasashen biyu.

 Bugu da kari za a yi taro na kwamitin kasashen Iran da Afirka ta kudun wanda zai maida hankali wajen tattauna yadda za a sake fadada alakar kasashen biyu.

Iran da Afirka ta kudu suna da kyakkyawar alaka ta fuskokin tattalin arziki da cinikayya.