Sep 20, 2017 17:17 UTC
  • Dr Ruhani: Amurka Tana Kaskanta Kanta Saboda Sabawa Ka'idojin Kasa Da Kasa

Shugaban Hassan Ruhani na kasar Iran ya bayyana jawabin da shugaban kasar Amurka Donald Trump yayi a babban zauren majalisar dinkin duniya a jiya Talata da cewa, jawabin na trump ya kaskantar da kasar Amurka ne a gaban kasashen duniya.

Shugaban ya bayyana haka ne a jawabin da ya gabatar a babban zauren MDD a dazu-dazun nan, ya kuma kara da cewa yerjejeniyar shirin nukliyar kasar Iran da ta cimmawa tare da manya manyan kasashen duniya 5+1 a shekara ta 2015, yerjejeniya ce ta kasa da kasa, wadda  har ma kwamitin tsaro na MDD ya maida ita kuduri mai lamba 2231, don haka karya wannan yarjejeniya daga bangaren Amurka zai cutar da Amurka ne ita kadai, domin dukkanin kasashen duniya suna mutunta yarejejeniyar.

A wani bangare na jawabinsa shugaba Ruhani ya bayyana cewa, mutanen kasar Iran basu bukaci wani abu fiye da adalci da kuma 'yanci da samun ci gaba ba. Don haka ba zata fara karya alkawarin da ta dauka da wadannan kasashe ba, amma kuma idan sauran bangarorin suka karya nasu alkawarin Iran zata maida martanin da ya dace.

Dangane da matsalolin kasashen Yemen Bahrain, Myanmar da Afganistan kuma, shugaban ya ce kada kasashen da suke da hannu wajen jefa su cikin yaki da tashe- tashen hankula, su yi zaton cewa  su ma zasu zauna cikin zaman lafiya da ci gaba na lokaci mai tsawo lokaci.

Tags