Ruhani Ya Ki Amincewa Da Bukatar Ganawa Da Trump A MDD
Ma'aikatar harkokin wajen kasar Iran ta tabbatar da labarin da ke cewa shugaban kasar Hasan Ruhani ya ki amincewa da bukatar da shugaban kasar Amurka Donald Trump ya gabatar masa na yana son su gana da kuma tattaunawa da shi a bayan fagen taron babban zauren MDD karo na 72 da aka gudanar a kwanakin baya.
Kakakin Ma'aikatar Harkokin Wajen na Iran Bahram Qassemi ne ya bayyana hakan a yayin wata ganawa da yayi da manema labarai a jiya Lahadi a yayin da yake amsa tambayar da aka masa na cewa shin da gaske ne shugaba Trump ya so ganawa da shugaba Ruhanin a birnin na New York.
Mr. Qassemi ya ce eh lalle gaskiya ne, yana mai cewa Amurkawa din ne suka bukaci hakan, sannan shi kuma shugaban kasar Iran Dakta Hasan Ruhani ya ki amincewa.
Shuwagabannin biyu dai sun halarci taron MDD karo na 72 da aka gudanar a helkawatar majalisar inda duk suka gabatar da jawabai don bayyanar da matsayar kasashen su kan batutuwa daban-daban musamman kan yarjejeniyar nukiliyan kasar Iran.
Babu wata ganawa da ta taba hada wani shugaban Iran da na Amurka tun bayan nasarar juyin juya halin Musulunci a kasar Iran a 1979, in banda a shekara ta 2013 da shugaba Ruhanin ya amincewa da bukatar shugaban Amurka na wancan lokacin Barack Obama na su yi magana ta wayar tarho shi ma a yayin taron MDD ne.