Jan 24, 2018 06:26 UTC
  • Sojojin Kasar Iran Sun Sami Nasarar Gwajin Makami Mai Linzami Mai Suna Qadir

A rana ta biyu a ci gaba da gudanar da atisayen soji wanda sojojin Jamhuriyar Musulunci ta Iran suka fara , sojojin ruwa na kasar sun gwada makami mai linzami mai cin dogon zango a cikin nasara.

Kamfanin dillancin labaran Tasnim ya bayyana cewa a cikin wani atisayi mai suna Muhammad rasulallah 5 (s), sojojin ruwa na kasar sun gwada wani makami mai linzami, mai kuma cin dogon zango a karon farko, wanda aka bawa suna  Qadir a cikin tekun Oman,  inda makamin ya sami nasarar kaiwa ga bararsa ba tare da kuskure ko kadan ba.

Wannan makamain mai linzami yana daga cikin makaman linzami wanda ake amfani da su a yakin da ake amfani da na'urori na zamani, kuma yana da karfi wajen lalata duk abin da ya samu. 

Labarin ya kara da cewa wannan atisayin sako ne ga dukkanin makobtan Iran sannan gargadi ne ga wadanda suke barazana ga tsarin Iran da kuma yankin gaba daya.

Tags