Rouhani: Bakin Al'ummar Iran Ya Zo Daya Kan Trump Da HK.Isra'ila
(last modified Sun, 06 May 2018 11:18:46 GMT )
May 06, 2018 11:18 UTC
  • Rouhani: Bakin Al'ummar Iran Ya Zo Daya Kan Trump Da HK.Isra'ila

Shugaban kasar Iran Dakta Hasan Rouhani ya bayyana cewa bakin al'ummar Iran ya zo daya dangane da shugaban Amurka da H.K.Isra'ila, yana mai jan kunnen Amurka dangane da batun ficewa daga yarjejeniyar nukiliya yana mai cewa Iran tana da hanyoyin kare kanta daga duk wata barazana.

Shugaban Rouhani ya bayyana hakan ne a jawabin da ya gabatar a ziyarar da ya ke ci gaba da yi a lardin Khorasan Razavi da ke arewacin kasar Iran inda yayin da yake magana kan barazanar da shugaban Amurkan Donald Trump na ficewa daga yarjejeniyar nukiliyan ya bayyana cewar: Babu wani amfani da Amurka za ta samu a fadarta da al'ummar Iran, don haka matukar dai ta fice daga yarjejeniyar nukiliyan, to kuwa ba da jimawa ba za ta yi tsananin nadama.

Yayin da kuma yake magana kan karfin kare kai da Iran take da shi da Amurka da wasu kasashen Turai da na larabawa suke ta magana kai, shugaban na Iran ya ce: Iran dai ba za ta taba tattaunawa da wani dangane da karfin da take da shi na kare kanta ba, ko shakka babu za ta ci gaba da kera makamai da kuma ajiye su gwargwadon bukatar da take da ita.

Yayin da yake magana kan kungiyoyin ta'addanci da manyan kasashen duniya suke goyon bayansu, shugaba Rouhani ya ja kunnensu da cewa: Iran dai ba za ta taba bari makiya suke sake kirkiro wata kungiyar ta'addanci irin su Daesh a yankin nan, don kuwa tana fatan ganin yankin nan ya zauna cikin lafiya da kwanciyar hankali.