Ansarullah: Amurka Da Kawayenta Suna Goyon Bayan Ta'addanci.
Babban sakataren Kungiyar Ansarullah ta Yemen, Abdulmalik al-Huthy ya ce wajibi ne a sauya sunan kawancen kasa da kasa da Amurka take jagoranta zuwa na goyon bayan ta'addanci maimakon na fada da ta'addanci.
Abdulmalik al-huty ya fadawa jaridar 26 September ta Yemen da ta yi hira da cewa; Ita kanta Saudiyya da take cikin kawance ba za ta tsira daga a karkasata ba zuwa kananan kasashe.
Badruddin al-Huty ya kara da cewa; Sabani da rarrabuwar kawunan da ake da shi a cikin kasar Saudiyya, zai sake fitowa, domin kuwa gwamnatin kasar ta kama-karya ce wacce take kokarin yi wa sabanin da ake da shi a cikin kasar kwalliya.
Dangane da nasararorin da aka samu akan kungiyar Da'esh a cikin kasashen Syria da Iraki da lebanon, Huthy ya ce; Nasarsa ce ga dukkanin al'ummar musulmi.