Yawan Shahidan Palasdinawa A Yankin Gaza Ya Karu
A ci gaba da hare-haren da jiragen yakin HKI suke kaiwa kan yankin Gaza a kasar Palasdinu ya karu zuwa hudu
Kamfanin dillancin labaran Mehr ya bayyana cewa a ci gaba da hare-haren da jiragen yakin HKI suke kaiwa kan yankin Gaza, a safiyar yau Asabar, mayakan rundunar Izzuddeen Qassam reshen soja na kungiyar Hamsa 4 ne suka yi shahada.
A daren jiya jumma dai dakarun izzuddeen Qassam biyu ne suka yi shahada. Har'ila yau ma'aikatar lafiya ta Palasdinawa ta bada sanarwan cewa daga ranar Alhamis zuwa jiya jumma'a Palasdinawa 1,114 ne suka ji raunuka daban daban.
A ranar Laraban da ta gabata ce shugaban kasar Amurka Donal trump ya bada sanarwan amincewa da birnin Quds ya zama cibiyar mulkin HKI, wanda ya fusata al-ummar Palasdinu da kuma kasashen duniya da dama.