Jan 10, 2019 12:17 UTC
  • Mayakan Haya Na Kasar Sudiya Da Dama Sun Halaka A Kasar Yemen

Wani jirgin yaki wanda ake sarrafa shi daga nesa ya kai hari kan taron wasu mayakan haya na kasar Saudia a kudancin kasar Yemen inda ya halaka da dama daga cikinsu.

Tashar talabijin ta Al-Masiriyya ta kungiyar Ansarullah ta bada labarin cewa an kai harin ne a Laradin Lahej daga kudancin kasar ta Yemen, amma bata bayyana yawan sojojin hayan da suka halaka ba.

Amma tashar talabijin ta Al-Arabiyya mallakin kasar Saudia ya bada labarin mutuwar sojojin haya 5 a harin da kuma raunata wasu da dama. 

Labarin ya kara da cewa sojojin hayan mabiya tsohon shugaban kasar ta Yeman Abdu Rabbu Hadi Mansur suna fareti ne a lardin Lahej a lokacin aka kai masu harin. 

Tun cikin watan Maris na shekara ta 2015 sojojin kasar Saudia da kawayenta suka farwa kasar Yemen da yaki da nufin maida tsohon shugaban kasar Abdu Rabbu Hadi mansur kan kujerar shugabancin kasar ta Yemen.

 

Tags