-
Yahudawa Sahyuniya Sun Rusa Gidan Palastinawa 132 A Qudus
Jan 10, 2018 02:53Wata cibiyar kare hakin bil-adama a Palastinu ta sanar a wannan Talata cewa 'Yan Sahayuniya sun rusa gidajen Palastinawa 132 a birnin Qudus cikin shekarar 2017 da ta gabata.
-
An Zargi Amurka Da Hannu A Tashe-tashen Hankula A Iran
Jan 09, 2018 15:43Wani tsohon jami'in Baitulmalin Amurka, -Paul Craig Roberts ne ya tabbatar da cewa kasarsa tana da hannu a cikin tashe-tashen hankulan da suka faru a Iran a makwannin da suka gabata.
-
Syria: 'Yan Ta'adda Sun Kai Wa Birnin Damascuss Hari Da Makaman Roka
Jan 09, 2018 15:41Harin na yau talata ya ci rayuka da kuma jikkata mutane 41
-
Sa'ib Uraikat Ya Ce Matakin Da Shugaban Amurka Ya Dauka Kan Qudus Zai Kara Rikici A Yankin Gabas Ta Tsakiya
Jan 09, 2018 03:00Babban jami'i mai shiga tsakani a kungiyar fafatukar 'yanto Palasdinu ta PLO ya bayyana cewa: Matakin da shugaban kasar Amurka ya dauka kan birnin Qudus lamari ne da zai kara bullar watan rikici da tashe-tashen hankula a yankin gabas ta tsakiya.
-
An Fice Da Yarimomin Saudiya Zuwa Gidan Yari Na Al-Ha'ir
Jan 08, 2018 15:43Kimanin yarimomi da tsfin hukumomin saudiya 60 ne aka dauke da wurin da ake tsare da su zuwa gidan yari na Alha'ir.
-
Gwamnatin Yemen Ta Bukaci Tattaunawa Kai Tsaye Da Gwamnatin Kasar Saudiya
Jan 08, 2018 04:22Priministan kasar Yemen ya bukaci tattaunawa kai tsaye da gwamnatin kasar Saudiya wacce take yakar mutanen kasar ta Yemen ba tare da tattaunawar ta hada da tsohon shugaban kasar Abdu rabbu hadi Mansur ba.
-
Taron Wasu Kasasken Larabawa Kan Birnin Qudus
Jan 08, 2018 03:36A ranar Asabar din da ta gabata ce wasu kasashen larabawa 6 da suka hada da Saudiya, Hadaddiyar daular larabawa, Jodan, Maroco, Palastinu da Masar tare da halartar babban sakataren kungiyar kasashen Larabawa Ahmad Abu Gaid suka gudanar da taro kan birnin Qudus ba tare da cimma wata matsaya ba.
-
Gwamnatin Masar Ta Karyata Zargin Goyon Bayan Shirin Donald Trump Na Kwace Birnin Qudus
Jan 07, 2018 16:04Gwamnatin Masar ta karyata rahoton da wata jaridar Amurka ta yada cewa: Masar ta nuna yardarta a fakaice da shirin shugaban kasar Amurka na shelanta birnin Qudus na Palasdinu a matsayin fadar mulkin gwamnatin Haramtacciyar kasar Isra'ila.
-
Sojojin Yamen Sun Kakkabo Jirgin Saman Yakin Rundunar Kawancen Saudiyya
Jan 07, 2018 16:02Sojojin Yamen da dakarun kungiyar Ansarullah na kasar sun kakkabo wani jirgin saman yakin rundunar kawancen masarautar Saudiyya da ke kaddamar da hare-haren wuce gona da iri kan kasar ta Yamen.
-
Saudiyya: Ma'aikatar Shari'a Ta Tabbatar Da Kame Yarimomi 11
Jan 07, 2018 03:02Babban mai shigar da kara na kasar ta Saudiyya ya ce an kame yarimomin 11 ne bayan da suka yi gangami a bakin fadar mulkin kasar