-
Saudiyyah Ta Hana 'Yan Qatar Shiga Harami Domin Yin Umrah
Jun 11, 2017 17:09Sakamakon yanke alakar da Saudiyya tare da wasu kasashen da gwamnatin Qatar, mahukuntan saudiyya sun hana wasu 'yan kasar Qatar gudanar da aikin Umrah.
-
Sojojin HKI Sun Yi Awan Gaba Da Palastinawa 7
Jun 11, 2017 07:42Dakarun tsaron Haramcecciyar kasar Isra'ila sun kai farmaki kan Palastinawa a wannan lahadi tare da yin awan gaba da Mutane 7
-
Qatar Ta Gode Wa Iran Saboda Kokarinta Na Magance Rikicin Da Ya Kunno Kai Tsakaninta Da Saudiyya
Jun 10, 2017 12:41Ministan harkokin wajen kasar Qatar Muhammad bn Abdurrahman Al Thani ya jinjinawa Jamhuriyar Musulunci ta Iran da kuma gode mata saboda irin kokarin da take yi wajen magance rikicin da ya kunno kai tsakaninta da wasu kasashen larabawa karkashin jagorancin kasar Saudiyya.
-
JMI Ta Yi Allah Wadai Da Hare Haren Ta'addanci A Garuruwan Babil Da Karbala Na Kasar Iraqi
Jun 09, 2017 12:42Gwamnatin Kasar Iran ta yi Allah wadai da hare haren ta'addancin da aka kai a garuruwan Karbala da kuma Babil na kasar Iraqi a safiyar yau Jumma'a wanda ya tafi da rayukan mutane akal 30 wadanda basu san hawa ko sauka ba.
-
Rarrabuwar Kawukan Kasashen Larabawa Kan Rikicin Qatar Da Saudiyya.
Jun 09, 2017 02:40Kasashen larabawa sun sami sabadi a tsakaninsu kan rikicin da ke faruwa tsakanin gwamnatocin kasashen Saudia da kuma kasar Qatar, wanda ya kai ga katse dangantakar jakadanci da kuma rufe kan iyakokin kasashen biyu ta sama da kasa.
-
Saudiyya, UAE, Bahrain, Masar, Suna Ci Gaba Da Kara Matsa Lamba A Kan Qatar
Jun 09, 2017 01:55Kasashen Saudiyya, UAE, Bahrain da Masar, sun fitar da wani bayani a jiya na hadin gwiwa, da ke saka wasu mutane 59 da kuma wasu cibiyoyi da kungiyoyi 12 da suka ce suna da alaka da Qatar a cikin jerin wadanda suke kira 'yan ta'adda.
-
Qatar Ta Ce Za Ta Iya Jurewa Duk Wani Irin Mataki
Jun 08, 2017 13:30Kasar Qatar ta ce za ta iya jurewa kan duk wani irin mataki da kasashe makoftanta zasu dauka akanta, aman ba zata taba mika kai ba.
-
Cutar Kwakera Ta Kashe Mutane 789 A Yemen
Jun 08, 2017 11:42Hukumar lafiya ta duniya ta ce mutane sama da dubu dari ne suka kamu da cutar amai da gudawa ko kuma kwalera a kasar Yemen.
-
Rashin Damuwar Gwamnatin Kasar Masar Da dubban Daruruwan Misrawa A Qatar
Jun 07, 2017 09:47Matakin da gwamnatin kasar Masar ta dauka na katse dangantaka da kasar Qatar domin neman yardar Kasashen Saudiya da Emarate ya fusata misrawa kimani dubu 250 da ke zaune a kasar Qatar
-
Takun-Saka Tsakanin Qatar Da Saudiyya Na Kara Tsananta
Jun 07, 2017 03:35Tun bayan da rikicin da ke tsakanin Saudiyyah da Qatar ya fito fili sakamakon sanar da yanke dukkanin alaka da kasar Saudiyya ta yi da Qatar kwanaki uku da suka gabata, lamurran suna ci gaba da kara dagulewa a tsakanin kasashen larabawan yankin tekun Fasha.