Mar 15, 2018 11:20 UTC
  • Rasha Ta Ce Ita Ma Za Ta Kori Wasu Jami'an Diplomasiyyar Birtaniyya Daga Kasar

Kasar Rasha ta ce nan ba da jimawa ba ita ma za ta kori wasu jami'an diplomasiyyar Birtaniyya da suke kasar a matsayin mayar da martani ga korar jami'an diplomasiyyarta su 23 da Birtaniyya ta yi biyo bayan rikicin da ya kunno kai tsakanin kasashen biyu dangane da batun amfani da gubar da aka yi a kan wani tsohon dan leken asirin Rashan a birnin London.

Kamfanin dillancin labaran Reuters ya jiyo kamfanin dillancin labaran kasar Rashan, RIA, yana fadin cewa ministan harkokin wajen kasar Rashan Sergei Lavrov ya bayyana hakan a yau din Alhamis a yayin da yake yin watsi da zargin da Birtaniyyan take yi wa Rashan kan hannu cikin wannan harin, inda ya ce lalle Rasha za ta mayar wa kura da aniyarta.

Birtaniyya din dai ta bakin firayi ministan kasar, Theresa May, da kuma sakataren harkokin waje Boris Johnson sun ce Rasha ce ta kai wannan harin wa  wa tsohon dan leken asirin Sergei Skripal dan shekaru 66 da 'yarsa Yulia 'yar shekaru 33 a kwanakin baya a birnin London da wani sinadari mai guba da nufin kashe shi da kuma rufe bakin duk wani mai adawa da shugaban kasar Vladimir Putin a cewarsu.

Birtaniyya din dai ta sanar da cewa za ta dau mataki kan kasar Rasha ciki kuwa har da takunkumi da kuma korar wasu jami'an diplomasiyyar Rashan da suke London.

 

Tags