Jun 19, 2018 05:50 UTC
  • Rasha 2018: Kasashen Afirka Na Ci Gaba Da Shan Kashi A Gasar Cin Kofin Duniya

A ci gaba da wasan kwallon kafa na duniya da ake gudanarwa a kasar Rasha, kasar Tunusiya ta shigo sahun sauran takwarorinta na nahiyar Afirka da suka sha kashi a gasar bayan da kungiyar kwallon kafa ta Ingila ta doke ta da ci 2-1.

A wasan da aka buga a daren jiya Litinin kungiyar kwallon kafa ta Ingila ta samu nasarar doke abokiyar karawarta ta kasar Tunusiya da ci 2-1, wanda hakan ya sanya kasar Tunusiya ta shigo sahun sauran takwarorinta na Masar, Moroko da Nijeriya da suka  sha kashi a wasannin da suka yi a baya.

Kungiyar kwallon kafa ta Ingila din dai ita ce ta fara sanya kwallon farko a ragar kasar Tunusiyan ta hannun dan wasanta mai suna Harry Kane, to sai dai kasar Tunusiya ta farke ne ta hannun dan wasanta Ferjani Sassi  a bugu daga kai sai mai tsaron gida da Tunusiyan ta samu. Ingila ta sanya kwallonta na biyu ne a daf da tashi inda Harry Kane din ya sanya kwallo na biyu a ragar kasar Tunusiyan.

Har ila yau a sauran wasannin da aka buga a jiyan dai kungiyar kwallon kafa ta kasar Sweden ta sami nasara a kan kasar Koriya da ci 1-0, sai kuma a wasa na biyu kuma kungiyar kwallon kafa ta kasar Belgium ta sami nasara a kan kasar Panama da ci 3-0. 

Tags