Aug 14, 2018 07:02 UTC
  • Rahoton MDD Ya Ce Akwai Dubban 'Yan Ta'addan Kungiyar Da'ish A Yankin Gabas Ta Tsakiya

Rahoton Majalisar Dinkin Duniya ya sanar da cewa: Duk da nasarar da aka samu na murkushe kungiyar Da'ish a kasashen Iraki da Siriya amma har yanzu akwai dubban 'yan ta'addan kungiyar a yankin gabas ta tsakiya.

A rahoton da kwamitin kwararru masu sanya ido kan takunkumin da Majalisar Dinkin Duniya ke kakaba wa a duniya ya gabatar a jiya Litinin ya fayyace cewa: Yawan 'yan kungiyar ta'addanci ta Da'ish a kasashen Iraki da Siriya a halin yanzu ya kai kimanin dubu talatin.

Rahoton kwararrun na Majalisar Dinkin Duniya ya kara da cewa: A halin yanzu haka akwai 'yan kungiyar ta'addanci ta Da'ish kimanin  4,000 a cikin kasar Libiya, kamar yadda wani adadi mai yawa na 'yan kungiyar aka dauki matakin jibge su a cikin kasar Afganistan.

Kwamitin kwararru masu sanya ido kan takunkumin da Majalisar Dinkin Duniya ke kakabawa a duniya yana fitar da rahotonsa ne a duk bayan watanni shida ciki har da irin halin da kungiyoyin 'yan ta'adda irin su Da'ish da Al-Qa'ida suke ciki a duniya.

Tags