Aug 21, 2018 19:00 UTC
  • IEA:Korea Ta Arewa Ba Ta Dakatar Da Ayyukanta Na Nukuliya Ba.

Hukumar kula da makamashin nukiliya ta tabbatar da cewa babu wata alama dake tabbatar da cewa kasar Korea ta Arewa ta dakarar da ayyukanta na nukiliya.

Cikin wani sabon rahoto da ta fitar a daren jiya Litinin, hukumar dake kula da makamashin nukiliya ta kasa da kasa ta ce ci gaba da kuma fadada shirin nukiliyar kasar Korea ta Arewa da kuma bayanan dake fitowa daga birnin Pyongyang kan wannan lamari, abu ne mai tayar da hankali.

Rahoton ya ce daga karshen watan Avrilu zuwa karshen watan Mayu, akwai alamomi dake nuna yadda mahukuntan birnin Pyongyang suka kara fadada ayyukansu na makamashin nukiliya.

Rahoton ya ce zuwa lokacin da hukumar dake kula da makamashin nukiliya ba za ta iya kafa na'urorinta a cibiyoyin makamashin nukiliyar na  Korea ta kudun  ba, to batun sa ido kan ayyukan na ta kayadadde ne.

Hukumar ta yi tuni da cewa tun a shekarar 2009 ne hukumomin birnin Pyongyang suka fitar da hukumar makamashin nukiliya ta kasa da kasa daga shafukan sadarwa na cibiyoyin nukiliyar kasar kuma daga wannan lokaci zuwa yanzu sun ki bayar da damar gudanar da bincike kan cibiyoyin nukiliyar kasar.
  

Tags