Oct 23, 2018 11:46 UTC
  • MDD Ta Nuna Damuwarta Kan Yadda Yanayi Ke Kara Kamari A Yemen

Jami'in dake kula da jin kai na MDD ya nuna damuwarsa kan yadda matsalar rashin isar da agaji kai kara kamari a kasar Yemen sakamakon yakin fice goma da iri da kawancen saudiya ya kadamar kan al'ummar kasar ta Yemen.

Cikin wani rahoto da ya gabatar a Zauren MDD Mark Lawcok jami'in dake kula da harakokin jin kai na Majalisar, ya ce yaki ya sanya yamaniyawa miliyan takwas da dubu 400 wato kashi 75% cikin al'ummar kasar cikin wani yanayi na bukatar taimakon gaggawa.

Lawcok ya ce cikin wata mai kamawa kimanin yamaniyawa miliyan uku ne za su shiga cikin matsananci hali na karamcin abinci, kuma mafi yawa daga cikinsu za su kasance mata da yara kanana.

Lawcok ya kara da cewa a halin da ake cikin akwai yara kanana dubu 400 dake matsananciyar wahala  saboda rashi abinci mai gina jiki.

Tags