Nov 06, 2018 05:16 UTC
  • 'Yan Indonesia 103 Ne Aka Yanke Musu Hukuncin Kisa A Saudiyya A Kasa Da Shekaru Bakwai

Ma'aikatar harkokin wajen kasar Indonesia ta fitar da rahoton cewa: A tsakanin shekara ta 2011 zuwa 2018 da ake ciki, 'yan kasarta 103 ne aka yanke wa hukuncin kisa a kasar Saudiyya.

Rahoton ma'aikatar harkokin wajen kasar ta Indonesia ya fayyace cewa: 'Yan Indonesia da aka yanke wa hukuncin kisar mafi yawansu mata ne da suke gudanar da aikace-aikace a gidajen mutane a kasar ta Saudiyya, kuma tuni an zartar da hukuncin kisar kan mafi yawa daga cikinsu, yayin da sauran ake ci gaba da tsare su a gidajen kurkuku.

Fitar da wannan rahoto na ma'aikatar harkokin wajen kasar Indonesia ya zo ne sakamakon hukuncin kisa da mahukuntan Saudiyya suka zartar kan wata mace 'yar Indonesia ta hanyar fille mata kai a cikin 'yan kwanakin nan kan zargin laifin kisan kai, lamarin da ya janyo rikicin siyasa a tsakanin kasashen biyu musamman bayan da al'ummar Indonesia gami da kungiyoyi daban daban a kasar suka dauki matakin gudanar da zanga-zangar yin Allah wadai da mahukuntan Saudiyya gami da sanya matsin lamba kan gwamnatin Indonesia domin bin kadin 'yan kasarta a Saudiyya.

Babban dalilin da ya janyo bullar wannan dambaruwar siyasar shi ne matakin da mahukuntan Saudiyya suka dauka na aiwatar da hukuncin kisa kan 'yar kasar Indonesia mai suna Tuti Tursilawati kan zargin kisan kai ba tare da sanar da ofishin jakadancin Indonesia da ke kasar ta Saudiyya ba, ko sanar da iyalanta ko kuma makusanta ta musamman kamfanin da ke kula da harkokin 'yan kasar Indonesia da suke gudanar da ayyuka a kasar Saudiyya.

Bayan gudanar da bincike kan batun kisan Malama Tuti Tursilawati an samu tabbacin cewa: Dauki ba dadi ta yi da mutumin da ta kashe a kokarin da ya yi na yi mata fyade, kuma babu wani lauya da ya wakilce ta a shari'ar da aka gudanar kanta. A halin yanzu haka dai akwai 'yan kasashen yankin Asiya da gabas ta tsakiya da kuma Afrika da dama da suke gudanar da aikace-aikace musamman a gidajen Larabawa a kasar ta Saudiyya kuma suna fuskantar matakan wuce gona da iri da musgunawa ciki har da fyade amma babu wani mataki da mahukuntan kasar ke dauka domin kare musu hakkoki, bil-hasalima duk wani kokari da suka yi domin kare kansu zai kai su ga fuskantar mummunan hukunci ciki har da kisa da sunan haddi.

Rahotonni suna nuni da cewa: 'Yan kasashen waje da suke rayuwa a kasar Saudiyya musamman wadanda suke gudanar da aikace-aikace a gidajen mutane suna fuskantar matsalolin rayuwa musamman cin zarafi da musgunawa tare da gudanar da mu'amala da su tamkar bayi ko kuyangu da aka ribato a yaki, kamar yadda baki 'yan kasashen waje suke dandana kudarsu a duk lokacin da suka shiga hannun jami'an tsaron kasar, inda suke fuskantar mummunar mu'amala da dangogin azaba musamman rashin kula da kiwon lafiyarsu da sauransu. Sakamakon haka kungiyoyin kare hakkin bil-Adama da na fararen hula a kasar Indonesia suka bukaci mahukuntan kasarsu da su dauki matakin mai da martani kan bakar siyasar mahukuntan Saudiyya tare da kawo karshen yarjejeniyar taimakekkeniyar da aka kulla a tsakanin kasashen biyu. 

 

Tags