Oct 04, 2017 11:24 UTC

Jama'a masu saurare Assalamu Alaikum barkan ku da warhaka barkanmu kuma d asake saduwa da kua cikin wannan shiri na Afirka amako, shirin da kan yi dubi a kan wasu daga cikin muhimamn lamurra da suka wakana a nahiyar Afirka a cikin mako, shirin na yau zai mayar da hankali kan cikar shekaru 57 da Najeriya ta samu 'yancin kai daga mulkin mallakar turawan Birtaniya, inda za mu mahangar masana a kan yanayin da Najeriya ta kasance a cikin wadannan shekaru, ta fuskacin ci gaba ko akasin hakan a banga

A ranar Lahadi da ta gabata ce 1 ga watan Oktoban shekara ta 2017, Najeriya ta cika shekaru 57 da samun 'yancin kai daga mulkin mallakar turawan Birtaniya.

Tun daga cikin shekarun 1800 har zuwa 1914, kasar da a halin yanzu ake kira Najeriya ta kasance a matsayin yankuna da turawan mulkin mallaka na Birtaniya suke shinfida ikonsu, daga shekarun 1914 har zuwa 1960 kasar ta ci gaba da kasancewa karkashin mulkin turawan Birtaniya, amma ana tafiyar da lamurranta ne tare da wasu fitattun mutane da turawan suka aminta da suka hada al'ummomi daban-daban daga bangarorin kasar a matsayin kasa guda.

A ranar 1 ga watan Oktoban 1960 ne Birtaniya ta bayar da 'yancin kai ga Najeriya, inda marigayi Sir Abubakar Tafawa Balewa ya zama firayi minister na farko a Najeriya. A shekarar 1963 kuma majalisar dokokin  Najeriya ta zabi Nnamdi Azikiwe a matsayin shugaban kasa, wanda ya maye gurbin sarauniya Elizabeth ta Biraniya, wadda take  a matsayin shugabar jeka na yi ka a Najeriya  a lokacin.

Bayan da Najeriya ta samu 'yancin kai daga mulkin mallakar turawan Birtaniya, an samu damar shimfida tsari da turba irin ta dimukradiyya a kasa, tare da bude kofofin samun ci gaba da habbakar tattalin arzikin kasa, to amma ba a je ko'ina ba, shekaru 6 kacal da samun 'yancin kan, sojoji sun yi juyin mulki, tare da kwace mulki daga hannun 'yan siyasa. Wannan lamari dai ya sanya kasar cikin wani yanayi na koma baya, tare da kawo cikasa  cikin lamurra da dama, da kuma haifar da rikici mai matukar muni, wanda ya kawo karshe a cikin shekara ta 1970.

Sojoji sun ci gaba da rike ragamar mulkin Najeriya har zuwa shekara ta 1979, inda Alh. Shehu Shagari ya karbi ragamar shugabancin kasar a karkashin shugabancin dimukradiya, wanda kuma shi ma ya kawo karshe a cikin shekara ta 1983 bayan an sake zabensa a wani sabon wa'adin mulki na biyu a karkashin inuwar jam'iyyarsa ta NPN, inda a nan ma sojoji suka sake yin juyin mulki.

Haka lamarin ya ci gaba sojoji suna ta yi wa junansu juyin mulki suna karbar ragamar iko da kasar har zuwa shekara ta  1999, inda aka sake girka tsarin dimukradiyya a kasar, wanda kuma har yanzu haka kasar tana ci gaba da tafiya  a kan tsarin dimukradiyya.

Da dama daga cikin masana suna ganin cewa katsalandan da sojoji suka yi ta yi a cikin ahrkokin mulki a Najeriya, ya kawo cikas da tsaiko wajen ci gaban da ya kamata kasar ta samu, a matsayinta na kasa mai arzikin ma'adanai da noma da makamashi da kuam arzikin yawan jama'a, idan aka kwatanta da wasu sa'ointa da suke a matsayi guda ko kuma ta dara su kafin samun 'yancin kai.

A halin yanzu Shugaba Muhammad Buhari shi ne shugaban kasa da ke mulki a matsayin  zazzaben shugaban najeriya a karkashin tsarin dimukradiyya, wanda ya karbi ragamar shugabancin kasar a cikin yanayi mai matukar muni ta tabarbarewar lamurra, wanda kuma yana daga cikin alkawullan da ya dauka tun a lokacin yakin neman zabe, kan shiga kafar wando daya da duk wasu ayyuka na ba daidai ba da suke kawo cikas ga ci gaba kasar a dukkanin bangarori, musamman ta fuskar cin hanci da rashawa da kuma gurgunta tattalin arzikin kasa, da kuma matsalolin tsaro da suka addabi kasar musamman a yankin arewa maso gabashin kasar, bayan bullar 'yan ta'adda masu na kungiyar Boko Haram a shekarun baya-bayan nan.

A cikin jawabi da ya gabatar ga al'ummar kasar na cika shekaru 57 da samun 'yancin kasar, shugaba Buhari ya jaddada aniyarsa ta aiwatar da alkawullan da ya yi wa 'yan Najeriya, da hakan ya hada da samar da ayyukan yi ga matasa, inda ya ce zai samar da ayyuka ga matasa dubu 10,000, kamar yadda kuma ya yi alkawalin fuskantar matsalar karancin wutar lantarki a kasar, inda ya ce za a kara yawan kara yawan wutar lantarki daga mega watta 7001 da kasar ke samarwa  ahalin yanzu zuwa mega watt 10,000 daga nan zuwa shekara ta 2020.

A dangane da matsalolin da ake fuskanta  ayankunan kudu maso gabashin kasar kuwa, shugaba Buhari ya bayyana cewa zai tattauna da shugabannin al'ummomi na yankin Neja Delta, domin ganin an warware dukkanin matsalolin da ake fuskanta a yankin baki daya, tare da jaddada cewa ba zai taba bari a  raba Najeriya ba.

A lokacin da ya juya kan batun yaki da cin hanci da rashawa kuwa, shugaban ya kara jaddada cewa babu gudu babu ja da baya kan abin da ake yi  kan hakan.

Tazara  ……………………………………..

A kan wannan batu na cika shekaru 57 da samun 'yancin kan Najeriya, mun ji ta bakin Farfesa Mustafa Gwadabe masani kan tarihin siyasa daga jami'ar Ahmadu Bello da ke Zaria, kan yadda yake ganin yanayin Najeriya daga lokacin samun 'yancin kai ya zuwa yazu ta fuskancin ci gaba ko akasin haka……

Hira {gwadabe}  () ………………………..

To dangane da batun tsaro wanda yake da gagarumin muhimmanci wanda sai ya tabbata ne ma ake samun ci gaba ta fuskar siyasa da bunkasar tattalin arziki a kowace kasa. Major Yahya Shinko mai ritaya masani kan harkokin tsaro daga Najeriya, ya bayyana mana yadda yake kallon batun tsaro a Najeriya tun daga bayan samun 'yanci daga mulkin mallaka na turawan Birtaniya.

Hira major ()………………………….

 

To a nasa bangaren Dr Sadiq Umar Abubakar Gombe Babban darakta na hadin kan jam'iyyun siyasa na Najeriya, ya bayyana mana mahangarsa kan yadda lamurra suka kasance a cikin wadannansheakru ta fuskar siyasa da zamantakewar al'umma.

Mosahebeh Gombe () ……………………………..

 

Jama'a masu sauraren lokacin da muke da shi dai ya kawo jiki dole  anan za mu ja linzamin shiri, sai Allah ya kai mu mako nag aba za a ji mu dauke da wani jigon kafin lokacin a madadin wadanda suka hada manasa sautin shirin na ke yi muku fatan alkhairi.

 

 

 

 

   

 

Tags