Mar 09, 2018 04:59 UTC
  • Sojojin Libya Sun Baiwa 'Yan Ci Ranin Afrika Wa'adin Kwanaki 9 Da Su Bar Kasar

Rundunar sojin kasar Libya ta bayar da wa'adin kwanaki 9 ga 'yan Afrika da suke cikin kasar ba bisa ka'ida ba, da su gaggauta barin kasar.

A cikin bayanin rundunar sojin kasar ta Libya wanda aka fitar a jiya Alhamis, an kirayi daukacin 'yan Afirka da suke cikin kasar ta Libya ba bisa kaida ba da su fice daga nan zuwa ranar 17 ga wannan wata na Maris.

Bayanin sojin kasar ta Libya karkashin jagorancin janar Halifa Haftar, ya bayyana shigar dubban 'yan Afirka a cikin kasar Libya da cewa ya taimaka matuka wajen kara jawo matsalar tsaro a kasar.

Tun bayan da 'yan tawaye masu alaka da kungiyar alqaeda tare da taimakon NATO da wasu kasashen larabawa suka kifar da gwamnatin Mu'ammar Ghaddafi a shekarar 2011, har inda yau take kasar Libya ba ta sake sheda zaman lafiya ba.

Tags