-
An Sace Wani Dan Kasar Jamus A Nijar
Apr 12, 2018 06:45Gwamnatin Jamhuriyar Nijar ta ce an sace wani Bajamushe da ke gudanar da ayukan jin-kai a kusa da iyakar Mali.
-
Ministan Harkokin Wajen Nijar Ya Yi Murabus
Apr 12, 2018 04:00Ministan harkokin wajen Jamhuriyar Nijar, Ibrahim Yakuba ya yi murabus daga mukaminsa, tare da janye jam'iyyarsa ta (MPN Kishin-kasa) daga kawancen jam'iyyu masu mulki na MRN.
-
Aljeriya: An Sanar Da Makoki Na Kwanaki Uku Sakamakon Mutuwar Mutane 257 A Hatsarin Jirgi
Apr 12, 2018 03:54Shugaban kasar Aljeriya Abdulaziz Butaflika ya sanar da makoki na tsawon kwanaki a fadin kasar, sakamakon mutuwar mutane 257 a wani hatsarin jirgin da ya auku jiya a kasar.
-
Buhari Yayi Karin Bayani Kan Dalilan Tsayawarsa Takarar 2019
Apr 11, 2018 13:02Shugaba Muhammadu Buhari yayi karin bayani dangane da dalilan sanar da tsayawarsa takarar shugabancin kasar a shekara ta 2019 bugu da kari kan batun rikicin makiyaya da manoma bugu da kari kan rikicin Boko Haram da 'yar makarantar Dapchi da 'yan Boko Haram din suke ci gaba da rike ta.
-
Somaliya Ta Dakatar Da Shirin UAE Na Horar Da Sojojin Kasar
Apr 11, 2018 13:02Kasar Somaliya ta dakatar da kasar Hadaddiyar Daular Larabawa (UAE) daga shirin da take aiwatarwa a kasar na ba da horo ga daruruwan sojojin kasar a wata alama da ke nuni da irin tsamin da alakar da ke tsakanin kasashen biyu ta ke ci gaba da yi.
-
Dakarun Kasar Tunusiya Sun Yi Arangama Da 'Yan Wata Kungiyar Ta'addanci A Kasar
Apr 11, 2018 13:01Ma'aikatar tsaron kasar Tunusiya ta sanar da cewa dakarun sojin kasar sun yi arangama da 'yan wata kungiyar ta'addanci da ke gudanar da ayyukanta a yankuna masu duwatsu da ke yammacin kasar.
-
Kimanin Mutane 257 Suka Rasu Sanadiyar Hadarin Jirgin Soja A Aljeriya
Apr 11, 2018 06:46Hukumomin Aljeriya sun sanar da mutuwar mutane 257 sanadiyar hadarin jirgin soja a kasar
-
An Kashe Mutane 4 A Gabancin Kasar Demokradiyyar Congo
Apr 11, 2018 03:37Sojojin gwamnatin kasar ta Demokradiyyar Congo ne su ka sanar da kai farmaki akan wata kungiya ta masu dauke da makamai tare da kashe shugabanta da kuma masu gadinsa
-
Amurka Ta Cire Chadi Daga Cikin Kasashen Da Ta Hanawa Yin Hijira
Apr 11, 2018 03:22Kamfanin dillancin labarun Reuters ya ambato majiyar gwamnatin Amurkan tana sanar da cire 'yan kasar Chadi daga cikin jerin kasashen da ta hanawa yin hijira zuwa Amurka.
-
Uganda: 'Yan Adawa Sun Kalubalanci Matakin Cire Dokar Kayyade Shekarun Dan Takarar Shugabancin Kasa
Apr 10, 2018 14:28'Yan adawa akasar Uganda sun garzaya kotu domin kalubalantar matakin cire dokar da ta kayyade shekararun dan takarar shugabancin kasa da ke cikin kundin tsarin mulkin kasar.