Ranaku goma na alfijirin nasarar juyin juya halin Musulunci a kasar Iran, wasu ranaku ne na tunawa da abubuwan farin ciki da sosa rai ga al'ummar Iran wanda sakamakon hadin kan al'umma da kuma jagorancin marigayi Imam Khumaini (r.a) suka sami nasarar tabbatar da mafi girman juyin juya hali na al'umma a karni na ashirin.
Gwamnatocin kasashen Faransa da Masar sun jaddada bukatar kara karfafa dangantakar soje da kuma tsaro a tsakanin kasashen biyu.
Miliyoyin ambiya mazhabar shi'ar Ahlul bait (AS) daga sassa daban-daban na duniya na ci gaba da isa birnin Karbala na kasar Iraki, yayin da kuma wasu suke a kan hanyarsu ta isa birnin, domin halartar tarukan arba'in an shahadar Imam Hussain (AS).
Yau Asabar ce 13 ga watan Aban na wannan shekara ranar da aka ware a nan Iran, aka kuma bata sunan ranar " yaki da kasashe masu girman kai na duniya".
Ministan harkokin waje na jamhuriya musulinci ta Iran, Muhammad Jawad Zarif, ya dawo gida Tehran, bayan kammala wani ran gadinsa na kwanaki biyar a wasu kasashen Afrika.
A ci gaba da ran gadin da ya ke a wasu kasashen Afrika, ministan harkokin waje na Jamhuriya musulinci ta Iran, Muhammad Jawad Zarif, ya isa birnin Yamai na Jamhuriya Nijar.
Kwararrun sun fito ne daga kasashen mambobi na kungiyar tarayyar Afirka domin tattauna matsalolin da suka shafi batun 'yan gudun hijira.
Shugaban kasar Iran ya jaddada aniyar kasarsa ta bunkasa alaka da taimakekkeniya tsakaninta da kasar Nigeriya.
A yau 14 ga watan Oktoban 2017, jakadan tarayyar Najeriya a Iran Alh. Hamza Ibrahim Tsiga ya mika takardunsa na kama aiki a hukumance ga shugaba Rauhani.
Kakakin ma'aikatar harkokin wajen kasar Iran ya bayyana cewa: Jawabin shugaban kasar Iran a zaman taron babban zauren Majalisar Dinkin Duniya karo na 72 a birnin New York na kasar Amurka ya fito da hakikanin fuskar siyasar Jamhuriyar Musulunci ta Iran a yankin gabas ta tsakiya dama duniya baki daya.