Mogherini: Dole Ne Kowane Bangare Ya Yi Aiki Da Yarjejeniyar Nukiliya Iran
(last modified Sat, 18 Feb 2017 07:55:01 GMT )
Feb 18, 2017 07:55 UTC
  • Mogherini: Dole Ne Kowane Bangare Ya Yi Aiki Da Yarjejeniyar Nukiliya Iran

Babbar jami'a mai kula da siyasar wajen kungiyar tarayyar turai Federica Mogherini ta bayyana cewa, kungiyar tarayyar turai za ta ci gaba da yin aiki da yarjejeniyar nukiliya da aka cimmawa tare da Iran, kuma dole ne sauran bangarorin yarjejeniyar su aiki da ita kamar yadda aka cimma matsaya.

Federica Mogherini ta bayyana hakan ne a lokacin da take ganawa da ministan harkokin wajen kasar Iran Muhammad jawad zarif a gefen taron da ake gudanarwa kan harkokin tsaro a birnin Munich na kasar Jamus.

Shi ma a nasa bangaren shugaban hukumar kula da makamashin nukiliya ta duniya IAEA Yukiya Amano a lokacin da yake ganawa da ministan harkokin wajen kasar ta Iran ya jaddada cewa, hukumar za ta ci gaba da goyon bayan wannan yarjejeniya, tare da bayyana gamsuwarsa kan yadda ya ce Iran tana aiki da yarjejeniyar kamar yadda aka cimmawa tare da ita.

Matsayar da kungiyar tarayyar turai gami da hukumar IAEA suka dauka dangane da yarjejeniyar nukiliya kan shirin Iran, na a matsayin mayar da martani ne ga shugaban Amurka Donald trump, wanda ya sha alwashin yin watsi da wannan yarjejeniya.